Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai Book 2 28-29

Sponsored links

Mami tun daga ranar ta Fara gyaran jiki dama tana yin abinta sabo da Balarabe ya Mata Illa,Nawwar ne ya samu Baffa yace Baffa Wai baza kuyi test na aure ba? Baffa yace test din uban wa lafiyar mu kalau ko Sanda muke saurayi da budurwa bamu Yi ba sai yanzu ko kanjamau ce da ita ko ni ai sai dai mu shafawa juna mu wuce lahira, karka kawo min Iskanci a nan Kai dama komai sai kayi Wasa a ciki sa’anka ne ni, yanzu da Auta ne zance zamuyi na hankali da shi,Nawwar dariya yayi dama tsokanarsa yayi yasan haka zai ce Auta shine na kirki,yace to Ni Zan kawo Amaryar taka? A’a zanje in dauko kayata ni na saka nace ka kawo min Mata gida dan Sa Ido, Auta yana zaune Yana ji yace Baffa Alkawarina fa? Gashi aure ya kusa tabbata,Karka damu Auta ko Yar gidan uban waye ka kawota sai dai duniya ta zageni akan aurenka ace anyiwa yaro aure da wuri amma ko wace Zan aura maka,Auta yace to Baffa dama akwai wata yar ajinmu yanzu ita nake so sunan larabawa ne da ita sunanta Sahar,Baffa yace Kai dai kayi shuru tunda Candy ya matso ai kana shiga University sai aure,yace to Allah ya kaimu,Nawwar yace Wai da gaske wannan mahaukacin yaron zaku biyewa kuyiwa aure,aure fa ba Wasa bane fisabilillahi kamar Auta fa 23yrs shi ba wani me jikin girma sosai ba sai yazo ya kasa rike aure,aure fa akwai wahala Auta kayiwa kanka fada wannan iskancin da kake ji gwara ma ka hakura,Baffa yace Kai Ina ruwanka,Nawwar yace shike nan ni dai Kar a sani a ciki wlh ba ruwana ba sa hannuna a ciki Kamar Auta nawa yake me ya sani ma a duniya Ina wannan yaron ina mace, Auta ya bata rai yace ni dama bance kasa baki b….rashin kunya zaka min Nawwar ya nufe shi zai make shi Baffa yace karka ta min dana ba ruwanka da shi ka kyale mu muyi zancen mu,Kai Auta bana son rashin kunya Yana magana kana yi,ai gani yake kanmu daya tunda Kuna daure masa gindi,Auta Murmushi yayi yace waye zai daure min abuna abuna kalau yake ba Wanda ya daure shi,ko Nawwar yaso yayi dariya dan shi har ga Allah hausarsa yayi ya manta ma sunan Antena ne,Auta Kuma yace shi ba a daure Masa kayansa ba,Auta tashi yayi sum sum ya fice abinsa,Nawwar ya fice ya koma gida wajen Mami yace yanzu da gaske auren za ayiwa Auta? Mami tace Wai me Auta ya tare maka ne da yarona ya lalace ai gwara a Masa auren, tunda Auta ya damu mutane Kawai idan da Hali ayi Masa Kar yazo ya fada harkar banza yaje yaci Karo da lalatattu, Kai da kake salihin ji nake da su Miracle ka hadu da tuni ma baka lalace ba badan Allah ya Kare ba shine zaka dame ni,Nawwar yace Mami Rabin tawa Zaki zaga,Ni ai ba zaginta nayi ba ai ta kirki ce gaskiya na fada,yace shike Nan ayiwa Auta aure lafiya ni dai ba ruwana ko daurin aure bazan je ba,karka je Mana dama wa ya gayyaceka cewar Mami.

Kaka Kuwa kwana Suka Yi suna tafiya a mota daga nan aka shiga jirgi da shi ta Jedda,Kaka tsoro ya kamashi Addua Kawai yake ya zaci wata state din zasu je a jirgi a ransa yace wata jahar zamu je Ina Jin lallai me kamafanin nan Yana da kudi ta wani bangaren Kuma zuciyar kaka a tsorace take sai da Suka Yi tafiya a jirgi ta Kai awa shida sannan Suka sauka a kasar Qatar Ashe kasar Qatar aka kawo Kaka za a siyar dashi azzalumai matsafan wasu larabawan suke Neman wani abu na sassan jikina mutum shine bakar fata shine marar gata shi za a kai a kashe shi Kamar ba Allah ne ya halicce shi ba,Mutumin bayan sun fito daga airport Kaka dai binsa yake dunkum dunkum Babu me jin yaren daya,a jikin wani shago mutumin ya tsaya tare da siyowa Kaka lemo da Madara da nama,Kaka ya samu waje ya zauna ya cika cikinsa dam,mutumin yayiwa Kaka Alama da ya jira shi.

Kaka ya nuna ba matsala mutumin Yana tafiya kaka ya fece ya dinga gudu gudu sauri sauri bai San Ina ya nufa ba bai San Ina aka kawo shi ba tunanin Kaka ma duk a Kasar Saudiyya yake wata state din har dare Kaka bai daina tafiya ba Kawai bi yake ta ko wanne lungu da sako,Mutumin Yana dawowa ya nemi kaka ya rasa Takaici da bakin cikin irin kudin da zai samu Kaka ya cuce shi ya gudu,haka ya ja kwafa ya sake dubawa bai ga Kaka ba babu alamarsa yasan tabbas ya gudu masauki ya tafi cike da bacin rai,Kaka Kawai tafiya yake sai da ya kwana Yana zaga gari Bai San Ina yake ba kafafunsa duk sun kumbura,waje ya samu ya zauna domin ya huta,tagumi ya zuba yace Ni da kasar waje har abada me za ayi da wata kasar waje,yanzu Kaka ya zaiyi ma ya koma garin Makkah shi yake tunani ba gida Nigeria ba,yace banga riba a wannan tafiyar ba,Cele tawa ta bata,na Sha wahala gashi da alama an kawo Ni nan a cuce ni,Yana ta maganganu shi kadai sai ga wani babban mutum bahaushe yace Sannu Malam,Kaka yace Kai masifa Kai bala’i ko Ina kaje sai kaga bakar fata sabo da shishigi da jaraba ko wacce kasa bakar fata sun taru sun cike gari jama’a muyiwa kanmu fada mu zauna a kasar mi Ina riba cikin wannan masifa,sai da Kaka ya Gama sannan ya dago ya kalli mutumin yace yanzu nan ma Kuna nan Wai bawan Allah nan Ina ce? Yace Kai baka San inda kake ba? Kaka yace ni nasan sadai a Saudiya nake Makkah wani balarabe ya min hanyar aiki yace zamu je a koya min aiki Jan dinga Jan motar Yogourt ya hadani da wani mutum balarabe sai naga mun dauki hanyar jidda a mota Muka shiga jirgi sai Muka zo nan bawan Allah wannan wacce Jaha ce a Saudiya? Mutumin yayi dariya yace ai Nan kasar Qatar kake cikin birnin Alqahira,Kaka yace Jar uba dan nan kayiwa Allah ka taimaka min na koma Makkah Dan Allah,Mutumin yayi dariya yace karka damu zuwa gobe kana Makkah Inshaallah,Kaka Yana ta murna Yana godiya mutumin waya ya dakko ya Kira wasu larabawa suna ta larabci Kamar ba bahaushe namu ba ashe shima sake cinikin Kaka yayi shi Kuma can dai Riyad za a Kai Kaka a siyar da shi,shi Kuma ba masu Luwadi za a bawa su siya in Suka Gama da mutum su sake shi ko su hallaka shi,shima bahaushen da shi ake hada Kai ana cutar bakar fata Dan uwansu bahaushe Kuma musulmi sabo da shi ya Zama hamshakin me kudi yafi shekara ashirin a zaune a Qatar sana’arsa kenan Luwadi har suke siyar da mutane ana Basu kudi a lalata su ba tsoho ba yaro ba matashi kowa Suka samu dama a kansa damawa suke,shima tafiya yayi da Kaka a gidansa Kaka ya kwana yaci ya sha da safe Kaka yayi wanka mutumin ya bawa Kaka Jallabiya sabuwa ya canja sannan ya hadashi da wani matashin balarabe me suffar Dan daudu ya tafi da Kaka aka sake shiga Jirgi da Kaka tare da juyawa da shi Saudiyya,suna zuwa Jedda Kaka murna ta kamashi Yana cewa naka sai naka ji bahaushe Dake dan uwa ne ya tallafa min gani a Jeddah Hauwa kulu Majadan Alhmdllh,Balaraben ya shiga mota da Kaka a zuwan zai kaishi Makkah sai ya wuce da shi Riyad,Kaka Kawai yaga bai yarda da tafiyar ba tun kafin su bar gari su Shiga daji yace a tsaya zaiyi fitsari ya nuna musu gabansa,ganewa sukayi Suka tsaya dai dai inda akayi toilet na mutane ka tsaya ka shiga Kaka ya fita Yana waige waige ya Shiga toilet ya fito ya lallaba yabi ta baya ya arce da gudu ya Sha kwana basu sani ba,Taxi ya tare ya shiga ya Fadi address din gidansu na Makka Basu ma karasa Makkah dinba ashe Driver ya Kai Kaka har kofar gida Kaka ya biya driver kudi ya fada gidansu cikin daki ya haye saman gadonsa ya ja bargo ya lulluba yana Nishi da hakkin wahala Wai ya buya kenan.

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button