Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 88

Sponsored links

Driving take hankali kwance dariyar mugunta kwance akan fuskarta, “kifi daga sama gashasshe”, ta fada tana cigaba da dariyarta, ashe haka motar keda dadi bata sani ba? Dake jiya bata cikin hayyacinta shiyasa bataji ba?, dama ance abinda ba naka bane yafi dadi, itako ta samu motar yawo a bagas…….

Horn tayi a gaban gate din me gadi ya taso ya bude mata da sauri yana gaisheta, bata amsa ba tace;

“Kar a rufe motarnan da ita zan koma”…..

“Angama hajiya”…

Ya fada yana rufe gate bayan ta shiga….

Direct part din daddy tayi bayan tayi parking motar, sosai take san magana dashi akan auren da suke shirin yi, tinda bukatarta ta riga ta biya bataga dalilin auren tsoho ba, idan auren ne gwara ta auri khaleel ya fiye mata ubansa……

Knocking daya tayi daddy dake zaune a parlour ya taso ya bude kofar….

Saida mood dinsa ya chanja daga ganinta, kallo daya zaka masa kasan ba karamin jindadin ganinta yayi ba, irin ka dade kana neman mutum sai yau Allah yasa ya ganshi……..

“Namu ni dakai, a fasa! Zan dawo maka da duk abinda na karba, ko ka barshi kawai a madadin danka khaleel, dama shiya kamata in aura!”….

“You must be kidding! Kinsan plan din danayi akan aurennan kuwa, harfa hafsah na saka!”….

“Wannan kuma matsalarka! Nina saka ka saki matarka? In banda abinka me zanyi da tsoho kamarka? Sannan ni bazan iya cin amanar khaleel ba…Banyi expecting zamuna dragging akan wannan maganar ba! Kamata yayi kayi farin ciki da nace na fasa tinda nina maka dole tin farko!”….

Saita kansa yayi ganin idan ya biyo mata ta haka bazasu daidaita ba yace;

“Hakane daughter I don’t even know what came to my mind, you deserve khaleel not me gaskiya, forgot to even tell you khaleel na kwance a asibiti bashi da lafiya sosai because he couldn’t reach you”…..

“Subhanallah, wani hospital yake?”….

Ta tambaya tanajin tausayin khaleel karo na farko a rayuwarta….

“National Hospital, Abuja”

“Zanje in dubashi Insha Allah”….

Ba daddy ba har ita da kanta tayi mamaki dataji tana son zuwa dubashi, daga jiya zuwa yau jinta take kamar different person……

“Ok, ya bani sako in baki, let me get it”

Yana fadin haka ya haura sama……

Daddy na sakkowa daga steps bayan ya dauko sakon wayarsa ta shiga ringing, ganin me kiran yasasa dauka da sauri yana sawa a speaker, gabadaya ya manta da mutum a parkour……

Tinda ya fara wayar hankalinta ke kai, hakanan ta samu kanta da bawa wayar dukkan nitsuwarta…..

“Hmmm kaidai bari mutumina, aikin gurina ya kammalu, na gama da tsegaran yaronnan dan gidan Alhaji Abdallah”…..

“Ahh kace anyi nasara kenan”….

“Sosai ma, take taken uwarsa justice fatima ne keban tsoro, naga alamun tana neman gano bakin zaren shiyasa jiya na aika yarana suka kaiwa gurin hari, maganar da nake maka yanzu an kona prison din kurmus”…..

Dariya daddy yayi ya shiga komawa sama yana fadin;

“Kai kai abu yayi kyau gaskiya amma na tayaka murna, hankali kwance zakayi harkannan yanzu kabar alhaji abdallah da jimami kasan ba karamin ji da munafukin dansa yake ba”…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button