Hausa Novels and Stories

Nihad Chapter 19 Hausa Novel

Sponsored links

Hadeta Khalil yayi da bango fuskarsa a daure yana kallonta cikin kakkausar murya yace “Zan maki gargadi na karshe, kar ki sake ta6a min wayata a gidan nan, kar kuma ki sake shigo min nan, ina me baki wannan shawarar”

 

Nihad dai gabanta sai faduwa yake ganin how huge he is a gabanta, ita bata ta6a sanin ma haka yake da tsayi ba, gashi ya murtuke fuska uwa ba drivern gidansu ba, amma duk hakan bai sa ta fasa daure masa nata fuskar ba ita ma, sai dai bata ce komai ba, komawa baya yayi yana kallonta, irin kallon kyama sannan ya nuna mata kofa calmly yace “Fita” Ba musu ta nufi kofa, tana isa dai dai kofar ta juyo ta kallesa tana wani yatsine fuska har da harararsa tace “Sai ka gaya min nawa ka siya shegen wayar taka in baka kudin wanda ya fi shi yanxun nan, ban ta6a ganin wanda ke takama da rakani kashi ba sai kai” Still yayi yana kallonta babu ko kiftawa, tana gama fadin abinda xata fada ta bar wajen da sauri tayi hanyar dakinta ta shige ciki ta kulle kofar tana sauke ajiyar xuciya, jingina tayi da kofar wani bakin ciki da takaici ya turnuketa wai yau ita da drivern gidansu ne kadai a gida daya har yana gaya mata maganar banza, ta ji xuciyarta na tafarfasa, she is still yet to believe this, ta kasa yarda wai da gaske wannan mutumin Abba ya sa su gida daya su dinga xama, how will that even be, fadawa tayi saman gado ta fashe da kuka tace “Wayyo Abba me yasa xaka min haka” Ita da dai drivern nan ai gwara ko almajiri ne Abba ya nemo mata su xauna gida daya, ta ci kukanta me isarta bacci ya dauketa a haka. Washegari har kusan karfe goma bata fito ba ga wani mugun yunwa da take ji, tashi tayi da kyar daga karshe ta shiga bandaki tayi wanka ta fito, daya daga akwatunanta dake dakin ta bude ta fiddo wata doguwar rigarta ta saka, xaunawa gefen gado tayi feeling so sad and dejected, daga karshe ta mike ta nufi kofa tana tafiya a hankali ta bude kofar ta fito parlor, babu kowa parlon sai take away din abinci da ta gani a tsakar parlon, ta saci kallon ko ina na parlon sannan ta karasa inda abincin yake tana ta6e baki ta bude take away din tana kallon abincin ciki, jollof rice ne sai sheki yake da katon kaza, ko rabi kuma bai ci ba, kazar ma bai wani ci ba ya bari, ta bude ledan dake wajen taga drinks ne sai chocolates me yawa, vibration din waya taji saman kujera ta kalla da sauri amma bata ga wayar ba, wanda hakan yasa ta gane wayar na karkashen throw pillow dake saman kujeran, har xata kai hannu ta daga pillow din ta ji an kulle kofar kitchen, sosai gabanta ya fadi ta juyo da sauri suka yi ido hudu da shi ya fito daga kitchen din rike da cup din shayi, sai a sannan ya ji vibration din wayarsa ya karaso da sauri, wanda tun kan ma ya karaso Nihad tayi hanyar dakinta tana harararsa, ya ajiye cup din hannunsa ya bi ta da kallo har ta shige dakin

xaunawa yayi saman kujera yana kallon throw pillow din kamar me son gano ko ta ta6a ko bata ta6a ba, da sauri ya dau wayar kafin ya katse ya daga ganin Abba ne, gaishesa yayi da ladabi Abba ya amsa yace “Anjima da yamma ka daukota ku zo gida ina son magana da ku” Khalil yace “Toh in sha Allah” Abba yace “Ai motar na can gidan ko?” Khalil yace “Ehh yana nan” Abba yace “Ina sauraronku xuwa nan da bayan la’asar” Khalil yace “In sha Allah” Daga haka Abba ya katse wayar, ajiye wayarsa yayi ya jinginar da kansa da kujera, this spoilt his mood the more, Allah ya sani he can’t endure staying under the same roof with this Brat, he wish this never happened, he detest the sight of her, da yasan this is how things will end babu abinda xai kawosa gidansu, da baxai fara ba, yanxu ta yanda ma xai ce ta shirya su je gida shine babban aiki a wajensa, ko magana baya son yana hadasa da ita, mikewa yayi ya dau wayarsa ya zura a aljihu ya fice daga parlon xuwa compound don ya fi zama comfortable xama a nan, abinda Nihad bata sani ba shine shi ya ma fita shiga damuwa kawai dakewa yake yi, kuma bata ki jininsa ba yanda shi ya ki jininta. Ganin yunwa na neman mata illa ta kara fitowa parlor, this time around hanyar kitchen ta nufa tana bin ko ina da kallo, ga kayan abinci amma babu kayan miya, gashi ita ba gwanar cin indomie ba ce, babu yanda ta iya haka ta dafa indomien ta fito ta wuce dakinta, tana ajiye indomien ta fashe da kuka sosai cike da tausayin rayuwarta, why did this happen to her, waye yayi mata haka yayi ruining happiness dinta all of a sudden, tasan duk rashin jin ta ko da singlet bata xama comfortable zama a inda ba gidansu bane, ko su Husnah da take bi she is very cautious of her self and her body, kuka take yi sosai wishing duk wannan abun bai faru da ita ba, indomien da bata ci ba kenan daga karshe, kawai ta tashi tayi alwala tayi sallahn azahar ta kwanta gefen gado hawaye na sauka idonta. Ana la’asar Khalil ya shigo parlor ya zauna yayi dialing number Abba, Abba na dagawa ya gaishesa sannan yayi kasa da murya yace “Abba tace ita baxata ba” Abba yace “Ohk, ba ta waya” Khalil yace “Toh” M

 

yayi ya nufi hanyar dakin da take ciki, yanda kasan yana kallonta jikin kofar haka ya hade rai yana kallon kofar, sai kuma yayi Knocking kofar, Nihad da ke kwance har sannan ta mike zaune tana kallon kofar, sai da ya sake Kwankwasawa ta mike xaune ta wani hade rai, sai kuma ta tashi ta tafi gun kofar ta bude cike da tsiwa tana harararsa tace “Lafiya kake kwankwasa min kofa Malam? Ko da bashi ne?” Mika mata wayar hannunsa yayi ba tare da ya kalli fuskarta ba, ta kalli wayar da kamar baxata amsa ba sai kuma tayi tunanin kila Umma ce, fixge wayar tayi daga hannunsa tana kallon Number sai taga number Abbanta ne, sosai gabanta ya fadi, tayi karfin halin kai wayar kunne, cikin sanyin murya tayi sallama, Zaro ido tayi tana sauraron abinda Abba ke ce mata with strictness, can ta kalli Khalil da ya koma can gefe ya jingina da bango ya rungume hannunsa, Abba bai bar ma Nihad space din cewa komai ba ya katse wayarsa daga karshe, ta fashe da wani matsanancin kuka tana kallo Khalil tace “Allah ya isa, ban yafe maka ba wllh, yaushe kace min mu je can gida nace Aa?? Wallahi ni baxan ta6a yafe maka ba” Sai kuma ta durkushe wajen tana kuka sosai ta kalli wayarsa dake hannunta tayi wurgi da shi ta mike ta shige cikin daki ta fada kan gado tana rera kuka, ya dau wayar tasa ya bar wajen. Bayan Nihad ta ci kukanta ta koshi ta mike ta dau hijab din da tayi sallah ta saka sannan ta fito daga dakin, compound ta fito ta gansa xaune driver seat ya bar motar a bude alamar dai ita yake jira, fuskarta a murtuke ta bude back seat ta shiga ta xauna, ya sauka daga motar ya tafi ya bude gate…..

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button