Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 141

Sponsored links

Sosai kirjin Daneen Waheeda ya buga, yayinda Daneen Ammarah ke murmushi kawai tana bin Iffah’r da kalion kasan ido, Bayan ta gaishe da su duk cikin girmamawa Daneen Ammarah ta nuna mata Daneen Waheeda. “Ga wata maman taki nan tazo kuna Saudiyya, nasan kin san dai sunanta da labarinta tun kafin yau”. Fuskar Iffah cike da murmushi ta jinjina mata kai. Kafin ta kara gaishe da Daneen Waheeda din da zancen cikin nan va sata sumar zaune, cikin murmushin yake ta kai hanunta kan Iffah’r ta shafa. Daneen Ammarah ta sake waiwayawa ta nuna mata Iftihal da tai kamar ma bata san mi ake ba “Wannan yar uwarki ce ita kuma, sunanta Iftihal, itace first born a wajen mamanki. Tanada kanne maza har uku”.

 

Murmushi kawai Iffah tai sai dai batace komai ba kamar anda itama Iftihal din ko dagowa batai ba. Yanda tai din kuma sai ya zafi Daneen Ammarah. Ita kanta malikat Haseenat dai tayi shiru ne amma fuskarta ta nuna jin zafin abinda Iftihal din tayi. Ita kam Iffah ko’a kwalar rigarta, hankalinta kwance suka cigaba da hirarsu da Daneen Ammarah da Jaddah..

Sai da tai sallar la’asar a sashen Malikat Haseenat sannan ta baro, fuskarta dauke da murmushin abinda take kullama Iftihal. Dan ta dau alwashin sai tayi dana sanin zamanta a masarautar nan duk da gidan kakanninta ne. Da ga nan sashen Malikat Bushirat ta nufa, sai dai ta samu wai bata nan tana a

sashen Shahan-shan. Hakan bai bata mamaki ba, ba kuma ta nuna ya dameta ba ta koma sashenta ita da tawagarta. Sai kusan karfe biyar ta nufi sashen Tajwar Eshaan..

A lokacin da Iffah ke nufar sashensa a lokacin shi kuma yake fita ta kofar sirrinsa zuwa sashen Malikat Haseenat. Cikin sa’a kuwa ya sameta ita daya a dakin. Kyawawan idanunta na tsufa ta zuba masa har ya kammala sakama kofar key ya cigaba da takowa gareta a nutse. A hankali ya kai zaune gabanta ya tankwashe kafafunsa.

Ya tada a kan lips a dan fisge kamar baya so.Murmushin ta sakar masa cikin yar tsokana ta amsa da “Barkan ka dai Abbien unborn”. Idanunsa ya dan waro mata na alamar mamaki, sai dai kuma bai iya cewa komai ba dan yama rasa bin fadar. Dariya Malikat Haseenat tayi mai kayatarwa, tace, “Ni dai bana fata ko mace ko namiji da za’a haifa su gado min wanna miskilancin naka Hafidi. Ace magana a bakin mutum amma furta ta ta zama aiki”, Kasa ya dan yi da kansa kawai yana murmushi. Kafin cikin son kauda maganar ya ce, “Amm Jaddah! Kamar yanda kika bada shawara nayi amfani da ita. Ani musu gwaji ta wasu abubuwan hallitar jikinsu kamar gashi da yawu jini batare ma da sun san duk muni hakan ba. Ita na bada nata, Sayeed Tasadduq-Husain kuma ya samomin na iyayen nata dan kamar yanda na fada miki dama tunda na saka a kaudasu a kasar shine yay aikin kuma shi kadai suka sani ya kuma san inda suke a yanzu haka ma”.

Cike da zumudi Mammah tace, “Ya ake ciki? Mi result din ya nuna kuma?”

Sai da ya dan ja iska kusan minti daya kafin ya nisa. “Al’amarin gaskiya yazo da rudani zance ne koba haka ba oho. Result din sun nuna shi Mahaifinta ne,amma macen ba itace ta haifeta ba”.

.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button