Hausa Novels Complete Documents

Daudar Gora Book 1 Page 68

Sponsored links

Tajwar Eshaan da ke kishingiɗe bisa ƙayataccen kujera mai kama da wani madaidaicin gado gabansa butar shayi ce da ƙaramin kofin da alamu suka nuna yasha ko zai sha, idanunsa ya janye daga kan television da yake kallo ya ɗan waigo garesu. Akan Iffah dake tafiya tamkar hawainiya ya fara saukewa, fuskarta a sakaye take, hanunta dake riƙe da rigar jikinta ne ta ƙasa kawai a bayyane. Janye wa yay ya maida ga Malikat Haseenat. Ta ɗan hararesa da salon kulawa da nuna damuwa. Idanun ya janye a sannu daga kanta itama yana sakin kasaitaccen murmushi….

Harya gama gaisawa da kakar tasa a yanda yake kishingiɗe batare da ya motsa ba Iffah na tsaye ƙyam tamkar an dasata. Malikat Haseenat ta maida kallonta gareta tare da ambatar sunanta. A dake Iffah ta amsa dan tayi alƙawari ma kanta bazata taɓa barin rauninta sake bayyana ga kowa ba a yanzun. Kafinma Malikat ta sake cewa wani abu tai ƙasa a hankali, cikin rashin ƙwarin jiki ta zube ƙasan lallausan carpet ɗin da ko jikin zomo bazai nuna masa laushi ba. Ƙamshi ko ba’a magana dan ko’anan ake shukashi iyaka kenan.

“Amincin ALLAH ya tabbata a gareka”.

Ta faɗa badan har zuciyarta abinda take son faɗar kenan ba. Sai dai kwarjininsa daya mamaye falon da duk girmansa take jinta a matse yaƙi bata damar fitar jin zafinsa dake a ƙasan zuciyarta a zahiri. Kamar a waccan ranar yau ma bai amsa ba, babu ma alamar yajita tattare da shi. Daga cikin hular alkyabbar jikinta ta cije lips ɗinta da masifar ƙarfi tamkar zata hudasu da haƙori…..

“Ai ma Zawjata-almilk rakkiya ɗakin da Tajwar zaiyi barci a yau”.

Furucin Malikat Haseenat ga hadiman dake rakuɓe gefe zube a ƙasa kawunansu rissine tun shugowarsu ya nema sarƙe numfashin Iffah da Tajwar Eshaan a lokaci guda. Babu wanda Malikat Haseenat ta kalla a cikinsu sai ɗaya daga cikin Hadiman ce da suke girki ta miƙe da rawar jiki zuwa inda Iffah take. Dole ta mike dan a furucin Malikat Haseenat babu wasa ko ɗaukar turjiya ga kowannensu….

Shiru falon babu wanda ya sake ƙwaƙwƙwaran motsi har hadimar data raka Iffah iyakar ƙofar ɗakin ta dawo Malikat Haseenat ta sallamesu. Da ga shi sai ita suka rage, dan haka ya kafeta da idanunsa. Kai Malikat Haseenat ta ɗauke gefe tamkar bata gansa ba ko fahimtar kallon.

“Anan zata zauna, sai ka zaɓi inda kake buƙatar ta kasance har tsahon sati ɗaya, dan zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu masu mata hidima zasu kasance tare da ita. Na damƙa amanarta a hannunka, ina kuma fatan ta kasance ƙarƙashin kariyar UBANGIJI. Fatan alkairi da shiga sabuwar rayuwa, tare da tayaka murnar sabon aure. Na barku cikin amincin ALLAH”.

Da alama gushewar numfashi da rikicin wannan tsohuwa ya gama daskarar da jinin Shahan-shan. Dan harta fice a falon ko gashin idonsa bai ƙyafta ba, kai kace wani butun butumine aka dasa a wajen domin tarihi…….

Duk da dare ne gaba ɗaya masarautar ta ɗauki ɗumi bisa wannan bahagon hukunci na Malikat Haseenat. Basu da al’amarin yazoma a bazata ba, hatta Malikat Bushirat da Daneen Ammarah da Jasrah da akai zaman da su komai ya musu cak. Abinda suka sani kawai komawar Iffah sashenta, bawai kaita turakar Shahan-shan ba. Miyasa Malikat Haseenat ta canja lissafin a kan kansu suma?. Wannan itace tambayar daketa musu kaikawo su duka.

“Ni kam dai a wannan gaɓar na kasa gane komai wlhy Akia. Shin minene dalilin Mamma nayin haka? Miyasa lissafin ya canja daga yanda muka tsara gaba ɗaya?”.

Kamar malikat Bushirat bazata tanka har ta kai ta kawo kusan sau uku kafin ta dubi Jasrah mai maganar. “Kaina ya kulle Jasrah”. Ta faɗa a takaice da kaiwa zaune bakin gadon ta dafe kanta.

“Ya ALLAH! Wlhy zuciyata ta fara kai ni ga hasashen wani abu daban?”. Jasrah ta sake faɗa tana dafe nata kan itama.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button