Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai Book 2 30

Sponsored links

Dagaci ana ta cin duniya da tsinke har sunyi kyan gani,Rabi ta sake Aiko musu da kayan sawarta data cire zata bayar tace a bawa Gaji,Gwaggo sauki ya samu sosai tana iya Dan tafiya kadan kadan itama sai data zabi manyan riguna a ciki Wanda zasu shigeta,Gaji sai daukan wanka ake yi ana neman bazawari,Asirin Zayya matar Danbinni ya karye tuni Danbinni ya saketa ya auro wata bazawara me hankali suna zamansu haka Yana lallaba rayuwarsa ya daina iya shegen da yake yaran Zayya biyu suna hannun matarsa suna zamansu,Babu kukan da Zayya bata Yi ba da roko yace wallahi baza ta dawo gidansa ba ya tsaneta yanzu baya sonta,Dole ta hakura ta tashi a tutar Babu ba tsuntsu ba tarko.

Sabreen ce taje wajen Mama ta samu Mama duk ta rame ta canja,tana ganin Sabreen sai data Yi kwalla tace na jawa kaina,Sabreen tace yo haka Kika zaba dai Mama gashi nan kin rasa Mami ta rasa amma ki sani Mami Aurenta za a maida da Baffa,kema baki kyauta ba dama idan kana tunanin kayiwa wani to kanka kayiwa gashi ni bani da auren ke Babu gashi kowa baya ta tamu shima Papa ya auri matarsa baya son laifinta ta Gama da shi bazai iya Mata kishiya ba Mata Muna sani mu dinga cutar kanmu da kanmu gashi yanzu inda Muka Kare Wanda Muka zalunta Kuma sune a sama,Ni gaskiya na gane gaskiya Shaye shayen ma so nake na daina na kusa hakura da shi duk da ban daina ba Nan gaba Zan daina,Mama ta kasa magana ma bata da abin fade Dan ma Allah yasa gidansu suna da rufin asirinsu dai dai gwargwado ba rashin ci Babu rashin Sha.

Omaira ke Omaira Abba Yana kwala Mata kira Shuru Omaira bata sani ba bacci ma take ita ,Uwa Babar Abba tace ai wannan yaran idan kana Jin jarabar duniya to su kenan,ai Kai Kam Ismail baka yi Dace ba ka haifi jaraba,Abba yace kyale su Watarana sai na bar gidan nan naga uban Wanda zasu raina,sun gaba talautani bani da farcen susa,Omaira ce ta fito tana mika tace Umma tace kana kirana? Mari ya kawo Mata ta kauce,Uwa tace yawwa nadawa Yar iska duka,Umma ce ta fito tace wallahi duk Wanda ya taba min ‘ya sai ya Gane kurensa,to fitsararriya kina bakin ciki Dana zai Sha shayi da Madara shi yasa Kika hana yarsa tazo ta je aikensa,Umma tace madarar me yan madarar burar….ta narko ashar,ai ke kin Zama mayya badan haka ba an sakeki zaman me kike Yi a gida shekara da shekaru har da Kai Kara kotu kice ba inda zaki je kotu ta baki damar zama a gidan tsohon miji kinji kunya dai ana korarki kina mannewa marar zuciya,zaman yarana nake Yi Kuma Dole ya ciyar damu karya kuke wlh baku Isa kuga bayana ba marasa godiyar Allah jahilai Allah ya baku baku so Inshaallah a yarana sai an samu wasu sun muku ranar da duk duniya babu Wanda zai iya muku ita,Dariya Uwa tayi tace a hakan? Ana kawo talakawan duk ba na kirki a yaran naki,Bilkisu ce ta shigo gidan tayi Sallama itace Babba a dukkan Yaran da aka Haifa sai ka dauka kanwar Umma ce,tana shigowa Abba ya fice daga gidan ma gaba Daya yasan bala’i tazo da kanta yanzu za ayi batacciya,ita kanta Uwa Shuru tayi ta wayance tare da furta Allah Yana Nan, Hayaniyar me nake ji? Bilkisu ta tambaya tana zazzare Ido ita dama kana ganinta kasan Kalar bala’i ce,badai Umman mu ake zagi ba? Umma tace gasu nan abinda Suka Saba kullum tunda aka aureni suke min haka gashi har na girma Kuma an sakeni ma baza a kyale ni ba ta karasa da hawaye,Bilkisu tace Abba ne Kawai zamu kyale sabo da mu cika da Imani billahillazi tsohuwar wani ba tamu bace ko Kaka uwa ce,Omaira tace never Bilkisu tace to tunda hakane a raba gida Bari kotu tazo ta tsagawa uwarmu sashenta kowa ya ji da Kansa zamu katange mata bangarenta kofa kowa da tasa mun gaji, Omaira tace Ina cikin masu buga bulo da ni za a buga bulo Aunty Bilkisu tace Allah yaji Kan Cele badan ta mutu ba da yanzu an wuce wajen nan na so Cele a gidan nan take da tayi min maganin wannan tsohuwar, Omaira tace kice da yanzu ta farfasa Mana jiki.

A ranar Aunty Bilkisu ta Kira sauran Yan uwan Suka hada kudi ciki kwana uku aka kawo yashi da siminti Kamar gidansu Abba bashi da ikon magana sunfi karfinsa, Suka taru dukkansu su takwas cif aka Kira ma’aikata masu buga bulo baza su siyo ba yayi tsada gwara a buga musu bulo, Masu buga bulo dukkan matan suna wajen sai kac fore maza ana farawa Bilkisu aka fara zubawa kwaben bulon ta buga guda daya Suka Yi tafi da ihu,sai Sai Nazifa da Nazira Suma Yan biyu ne,sai Safiyya da Sufia Yan biyu ne su ma Suka buga har Kan Omaira sai twins Suma Rahma da Raheema,sauran Suka barwa ma’aikata suna ta fama a ranar Suka buga bulo,Cikin dare Uwa ta fito da tabarya kowa Yana bacci gaba daya tasa tabarya ta doke bulo din kaf bata bar ko guda Daya da lafiya ba ta koma ciki tayi kwanciyarta sai da safe su Omaira Suka ga bulo a farfashe gaba daya an tarwatsa su,ransu ya baci ga asarar kudi sunyi dama su ba wani kudi ba,gida ta dawo ta fadawa Umma,Umma tace kyale su dan Allah nasan Babu me Yi sai kakar ku Allah Kuma zai saka Mana Allah Yana kallon su,baya bamu ci da sha ga wulakancinsu sabo da sun sa ya sakeni,abin haushi ma Wai abin nasu duka danginsu na rasa me na tare musu a duniya haihuwa laifi ce,Omaira tace kiyi hakuri Umma komai zai wuce Allah ya Mana arziki zasu ga tsiya.

Umma tace badan ku ba da naga wulakanci a duniya a gidan nan to Allah ya min arzikin Yara Ni ko yanzu sai dai nace Alhmdllh.

Nazifa ce ta shigo tace me nake ji haka Wai an rushe mana bulo? Uwa tana ji tayi mukus,Nazifa tace ko waye Allah ya tsine Masa Albarka ba shi ba rahamar Allah ai mu bama kisan mummuke a fito fili Mana a fasa a bainar jama’a a gani,wallah ko waye Allah ya tsinewa uwarsa,Uwa tana ji tasan da ita suke sun San ma itace da ubansu baza su zage shi ba ko me yayi musu kyale shi suke Yi amma ita da sauran dangi basa kyalewa,Kannen Uwa ne Suka shigo su biyu Sa’ade da goshi, Nazifa tace kannen wata ma matane duk gidansu Mata sunfi yawa namijj daya ne tal Kuma tambadadde ne ma namijjin gashi nan duniya duk tayi Masa Ruku’un Dila,Sa’ade tayi dariya ba shiri tace shegun Yara Baku da aiki sai bakar magana yanzu Baballlen kanin Uwa shine tambadadde duniya ta Masa Ruku’un Dila, Nazifa tace to mene shi dan kwaya bama gwara Mata masu tausayi ba mazan wasu duk gasu nan daga sunyi aure sai matansu da Dangin matansu mace ma me tausayi da Jin kai baza ayi Addua Allah ya bada dana gari masu Albarka ba sai maza maza mace ba mutum bace sabo da jahilci ku Kuma da kuke son maza wace ta haife ku idan ba mace ba,ku sai ku canja kanku ku koma mazan ai Jahilcin banza idan ance muku jahilai kuce ku ba haka ba,Omaira tana fari da rangwada tace mu da muke da baiwa ma iri iri mune fa farin cikin mazan su taba mu ma Dadi ne,Umma ta kwade Omaira tace ke a gaban namu ne,nace dan basu San Miracle bane da fitsara bane,haka ranar Suka yini suna Shige da fice a gidan suna tijara iri iri idan wannan tazo ta tafi gidan mijinta sai wannan tazo Uwa sai barin gidan tayi ranar sai dare ta dawo shima Abba guduwa yayi sabo da jarabar yaran nan,Umma Kuwa da tana Hana yaran ta gaji yanzu Ubansu Kawai zasu yiwa ta taka musu birki sabo da mahaifi mahaifi ne ko ne yayi musu basa ce Masa kala in Banda Cele itace kadai take fada Masa abinda taga dama shima da dalili abinda ya mata dole tayi.

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button