Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai Book 23-24

Sponsored links

da shagwaba tace kirana tayi fa matsala ce shi yasa yace to shike nan kije da motata karki kai dare tace to,da Yamma ta shirya taje,bayan sun dan taba hira Wise ta bawa Sera labarin komai,Seraline tace ki kyale su tunda uwarsa tana ciki kin San uwa tana da power zata iya yanke hukunci ko shi Mijin naki sai ya Mata biyayya ke me ya dameki suyi ta Yi miji shi Zaki rike duk abinda zasuyi a banza yaran dai idan Suka Miki kici ubansu wannan Sabreen din naga Alama bata daku bane,Wise tace zanyi bariki a gidan nan,Seraline tace a’a karki Yi please dariya Suka Yi tace kinga Iyamami da ace ba uwarsa bace da yanzu na canja Mata kamanni Mata da budurwar zuciya kullum zo kiga kwalliya ta wani saka jambaki harfa kitso ake Mata da Attach wallahi Rannan cewa tayi sai an sa Mata Attach,Seraline ta dinga dariya tace na gani ai,tace ni ai da dangin Sabeer sun Fara min wulakanci ya taka musu birki da Kansa ya kwatar min yanci shike nan ai Yana Jin harka a local government yaci ubansu kaf.

Wise da Sera suna Hira Suka ji hayaniya lekowa Suka yi Suka ga Auta da Iklima bakuwa matar da za a aurawa Papa suna kokawa, Namiji da mace karfi ba daya ba sai gashi Auta ya fasa Mata Hanci da baki jini Yana fita,Fitowa sukayi da Sera suna tafawa Auta wise tace Auta another punch Auta Kamar dan China haka yayiwa Iklima budu budu tana ta ihun agaji,Iyamami ce ta fito da gudu tana zagin Auta tace ubanka ta maka yanzu zaka Yi kisan Kai Dan iskan yaro marar tarbiyya dama uwarku bata muku tarbiyya ba,Auta yace ai ke shi yasa naga tarbiyar ce dake ke naki Iyayen tarbiyyar Suka Miki ai da sun Miki tarbiyya da baki abinda kike ba Kuma wallahi ta sake cewa zata aikeni sai na karyata baras,au au yanzu dama akan Kawai tace zata aikeka shine ka Mata wannan dukan,yace ae ni sa’anta ne ko kece bazan je ba bare wata kucaka kazama,ta kirani wai Kai yaron nan nine yaronta ko kanin ubanta ne ni,ko Papa kanin Ubana baya min wannan Kiran sai ita sabo da kin kawota Zaki cusawa Papa ya aureta baya so ta tafi gidan ubanta wallahi baza a sata a gidan nan ba ai ba gidanki bane kema Iyamami,Dan ubanka ko ubanka bai Isa dani ba bare kai,ai Ubana Yana tsoronki aljanarsa tana kafarki ni tawa a kafarki take? a kafar uwata take bazan biki ba idan Kinga dam ki tsine min ma,ai Kuwa idan na tsine maka sai ta kamaka yanda na Sha wahalar rainonka da goyaka a bayana ga shegen kukan tsiya haka nake goyaka kayi min fitsari da kashi duk na wanke maka,Auta yace Iklima take ko wa bata da waje a gidan nan baza a aureta ba, Iyamami tace to na gani idan ka Isa sai mu gani mace daya tayiwa Dana kadan wannan Karuwar ce zata bar gidan nan bana kaunarta.

 

 

Auta ya nuna Wise yace wannan da kike gani hadin Allah kenan mace Daya tamkar da dubu ai akan ki aurawa Papa Mata goma to gwara ki bashi Wise guda daya,baki ji sunan bane Wise ta ko Ina Wise ce duk ta cike gurbinsu su goman ,kainuwa dashen Allah ita da Papa sai Allah, yau naga dan iskan yaro haka ka koma cewar Iyamami, Auta yace Kuma sai ta haifo mana yara Papa ya samu yaran kirki masu Jin Kansa ba irin Sabreen ba ciwon Kai hawan jini da Kansa to Sabreen kenan, Auta ya kalli Wise yace kina haihuwa na zama Dan raino, ki share su Iyamami ba Arabic ba boko baza su gane ba ko Papa ya sakeki Ina nan zanyi ciki dake ni a haka ma Ina so,Iyamami salati ta saki tace au kwarto ka koma Kuma to wannan sai an sa Ido a kanka tunda ka Fadi haka zaka iya zagawa dama kaga Karuwa ce shike nan kwartonki a gida, Auta yace ke ma da kinyi wa ya san irin zalamar da Kika Yi a zamaninki, ki dai gyara tsufanki ko Kya samu ki cika da Imani yanzu mutuwa ma Yara dauke su take ba sallama bare ke da kin tafi gangara idan baki tuba ba sai yaushe, kin girma kisan kin girma,ki sani gadararki ke Kika haifi yara to suna da hakki a kanki wallahi sai Allah ya tambayeki tunda Amana ya baki,

Dan Adam guda aka zabeki aka baki su gasu nan har Mata da maza aka hada Miki matan sun gujeki sai sunga dama suke zuwa daga su sai yaransu sabo da duk kinbi kin watsa Kan yaranki da kanki Aunty Rukayya da Aunty Binta ko gaisheki basa zuwa sai suyi shekaru sai da dalili suke zuwa Babu zumunci Sam yaransu basu sanmu sosai ba muma Haka to a haka kike so idan kin mutu muyi zumunci zuriarki su hada Kai a haka,yanzu Maman Sabreen duk kin jawo yanzu anyi baran baran,komai kin lalata Baffa ma da Papa badan Allah yasa ba da yanzu sun farrake to a haka ke son yaranki kike Yi? Ai ke ce ma makiyiyarsu,kina ta shiga hakkinsu kin hanasu zaman lafiya da matansu,takala na bala’i me kudi nayi mene amfaninsa sabo da koshi ya Miki yawa Zaki ci abinda kike so Allah ya bawa yaranki kudi, wani abin ma samun waje ne koshi ya Miki yawa da ace Zaki tashi ki wayi gari ace ta Yaya ma Zaki ci ki rayu kike da baki tsaya wannan abin baki da lokacin wannan abin,ta cikinki kike Yi,for God sake ki kyale mutane su sakata su wala Ki ja mutuncinki ki ja girmanki ke yanzu dadine Kamar mu ace mu zauna Muna fada Miki magana yanda muka ga dama,kin Sa surukai duk sun rainaki kowa ya tsaneki idan Kika mutu waye zai miki Addua me kyau ko yabon halinki baza muyi ba sai dai muce Allah raka taki gona wallahi sai na raka makara ina tsaye Ina latsa wayata Ina chat,kin San dai yanzu haka akeyi ana makarbata tsabar bushewar zuciya Zaki ga mutane ba ruwansu waya ma suke dannawa suna chatting abinsu,ko mutum ya hau tiktok akan kabari Yana kallon shirme da fitsara to yanzu haka akeyi,Ki kyale mu Dan Allah mu sarara,ki fadawa bakuwarki ba a aikena idan bata sani ba ta sani me aikena sai ya shirya ba kowa ba wlh sai Ina ganin mutuncin mutum bare tazo tana ce min Kai yaron nan sabo da ita bazawara ce wa ya san me tayi aka saketa maybe ma uwar mijinta tayiwa dukan tsiya ke kin kawota sabo da son zuciya danki ya aura kina nan za a aureta ta karyaki ta Miki buju buju ba ruwanmu Kuma Kuna Yi Muna Shan Ginger juice mu ba ruwanmu,har wani Galavanting take a gidan mutane.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button