Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 143

Sponsored links

A hankali ya cigaba da takawa cikin dakin yaje gabanta ya tsaya. Jitai kawai an tura mata yatsu cikin gashi. A firgice ta dago dan ko kadan bayaji motsin shigowar tasa ba. Cikin juna idanunsu suka shige, kowanne cike da kewar dan uwansa kamar sun hada watanni basu hadu ba. Itace ta fara janye nata a slowlv. kamar mai in kunvarsa ta maida kanta kasa ta dukar. Numfashi ya dan furzar kadan, tare da dukowa

ya zare ribbon din hanunta ya saka cikin tsintsiyar nasa hannun kamar maisa bangles, sai kuma ya maida duk hannayen biyu saman kanta ya tattaro gashin a tsakkiya ya dare mata.

“Thanks you”.

Ta fada cikin siririyar muryarta da ke ratsa masa jiki, yasan tsaiwarsa a wajen bazata hafar masa da da mai ido ba. Dan haka ya rabata ya wuce cikin tafiyar tasan nan daddaya dan azuminsa ya isa lafiya. Da kallo ta bisa har ya shige bayi, sai kuma ta saki sassanyar ajiyar zuciya ta mike. Closet dinsa ta nufa kasancewar akwai finger print dinta yanzu akai itama. Lallausar jallabiya kalar maroon ta zaba masa, tare da alkyabba irin ta sarakan saudiyya. Fitowarta dal-dai da tashi. Kallo daya ta masa ta dauke kai dan har yanzu ta kasa sakewa da kalion wanna jikin nasa. Kanta a kasa ta karaso gabansa, karamin towel da ke hannunsa ta amsa, babu musu ya sakar mata, sai da ta lumshe idanunta sannan ta fara tsane masa jikin. Dan garetan murmushi ya saki idanunsa kan kyakykyawar fuskarta harta kammala. Man da yake amfani da shi ta ajiye zata gudu ya rikota a slowly yaNmaidota baya. Sai da ya gama kare mata kallo da gaNsama har kasa sannan ya dire kan fuskarta da idanun ke lumshe. A can kasan makoshi ya furta, “Shi man wazai shafa?”. Batare data bude idon ba ta ce, “Ka tayani”.

 

“Naki wayon”.

 

 

 

Ya bata amsa yana maidota gabansa da kyau. Dan murmushi tai zatai magana ya ce mata, “Shilli!!!” Shiru tai ta hadiye abunta. Shi kuma ya daura mata man a kan hannu. “Oya zan makara sallar magrib”. Babu yanda ta iya dole ta shafa masa. Kirjinta sai bugawa yake da sauri-sauri dan da gaske jikin nan nasa toro yake bata. Ta rasa mike birge maza suke maida kansu haka ita kam. Rashin mafita ya sa dole har shiryawa sai da ta taimaka masa wajen yi. Tana kammala saka masa turare ya kamo fuskarta cikin tafukan hannunsa ya sumbaci goshinta da idanunta da karan hancinta, sai kan habarta. Sassanyar ajiyar zuciya ta dan saki. Bata ankara ba kawai ta gansa duke gabanta ya dan daga rigarta ya sumbaci cikinta. Da ga haka ya wuce abinsa cikin dakewa kamar bai aikata komai ba. Da kyar ta iya bude ido ta bisa da kallo, dai-dai zai fice ya dan tsaya a jikin kofar tare da juyowa suka hada ido. Kauda nata tai da sauri, shi kuma ya dan sakin murmushi a iya lips da fadin, “Idan kika bar sashen nan kafin na dawo sai na hukuntaki”. Da ga haka ya fice ya barta da murmushi a fuska..

Bai shigo gida ba sai da aka idar da har sallar isha’in da asham, dan bayan idar da sallar magrib ya sha ruwa da dabino a can. Da ga haka yay zaman karatun Alkur’ani. Kowa yasan hakan yake yi a duk shekara, dan baya shigewa sai bayan an kammala salla baki daya kamar yanda yake yi idan ba’a azumi sai ani har sallar isha’i. Bisa rakkiyar su Sayeed Fayzul-haq ya dawo sashensa. Hadiminsa kam tun da yaji a bakin masu girki Zawjata-almilk tazo itamace taima Shahan-shan girki da kanta baiyi gigin biyosa har nan ba sai ya lake a 3 floor din. Babu kowa a faion sai sanyin ac da kamshi mai dad ba irin wanda ya bari ba. Bedroom ya nufa domin rage kaya, zuciyarsa na raya masa tama gudu kenan bataji gargadinsa ba. Sai dai yana murda handle din kofa itama tana budewa, kusan cin karo sukal da juna ALLAH dai ya kiyaye taja baya da sauri, sai kuma ta kusan faduwa sai da ya rikota jikinsa. A jiyar zuciya ta sauke cike da shagwaba ta ce, “Thanks you”

Maimakon amsa. mata godiyar cak ya dagata bisa kasa suka koma dakin. Tana watsal-watsal da kafafu da rokon ya sauketa ita yunwa takejl bai ma saurareta ba sai da ya direta inda yake bukata ya rufe bakin tsiwar dan iya yaren da zuciyarsa da kwakwalwar ke bukata kenan kawai……

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button