Latest Updates

Yadda ake Tuwon Madara/ Alawar Madara cikin minti Biyar

Sponsored links

Yadda ake Tuwon Madara/ Alawar Madara cikin minti Biyar.

Wasu da dama suna mamakin yadda ake hada tuwon madara, wanda wasu kuma suke kira da suna alawar madara. Wadda a turance kuma ake kira da Milkcandy. 
Ba wani abu bane mai wahala ba, sai dai rashin sani wanda kuma an ce yafi dare duhu. Wannan rubutu zai taimaka maku sosai wurin  samarda alawar madara cikin ƴan mintuna kadan. 
Ku karanta jawabin dake ƙasa daki-daki domin samun sanin yadda zaku samar da tuwon madara cikin sauki, ba tare da an dauki tsawon lokaci ba

 TUWON MADARA

INGREDIENTS/ abubuwan da ake hadawa da su.
1.Madaran gari rabin loka
2.Sugar gwangwani biyu
3. Leda
PROCEDURE/ yadda ake yi:
A samu ruwa kamar rabin kofi a zuba a tukunya sai a juye sugar, a barshi yayi ta dahuwa har sai yayi kauri. In kika dangwala zaki ga yana yin ďanko kamar na aya mai sugar. Sai ki ďauko madarar kina juya wa kina zubawa, idan ya shige duka shikenan in kuma bai shige ba sai ki bar sauran.
Amma kada yayi qarfi sosai kada ki ce dole sai duka madarar ki ta shige. Sai a juya bayan tray a shimfida leda a kwashe kafin ya fara yin brown, kada kice zaki barshi bayan kin juya, yana hade wa ki sauke. A samu mara ko muciya (kneading stick) a sa shi yayi plat dai-dai kauri ko faďin da kike so.
Shikenan sai a yayyanka shape ďin da ake so. 
Akwai tuwon madara mai kwakwa plz idan akwai wacce ta iya ta koya mun ta comment. Saboda ina ta tunanin a cikin madarar ake zubawa kafin a zuba ko kuwa a sugar ne.
Ni fa bana son baki na ya zauna shiru ba ya aiki. 
Kuci gaba da kasancewa da wannan shafin mungode da ziyartarku.
Kuma kada kumanta ku’aje mana ra’ayinku a comments box dake kasa mungode.

Sponsored Links

One Comment

Leave a Reply

Back to top button