Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 45

Sponsored links

What happend?”.

Ya faɗa a cikin kunenta da wata irin shaƙaƙƙiyar murya da bata taɓa ji da ga garesa ba, gata acan ƙasan maƙoshi matuƙa. Yanda sautin ya ratsa kunenta har cikin ɓargonta da ƙwaƙwalwar ta ya sata rumtse idanunta da masifar ƙarfi tana wani ƙanƙamesa. Ihu kawai ya rage ya sakar mata ko zata gane a wane riski ta jefashi, amma sai ya danne cike da jarumta ya furzar da boyayyan huci. Cikin sigar tambaya ya sake faɗin, “Uhhuyim?”.

Nan ma kamar bazata amsa ba sai kuma ta nisa tana sauke ajiyar zuciya. Kanta ta ɗan girgiza a hankali ta ce, “Mafarki”.

“Mafarki?”.

Ya maimaita akan lips ɗinsa yana ƙoƙarin saka idanunsa cikin nata kasancewar ta ɗago da ga jikin nasa. Kanta ta gyaɗa masa tana ɗan kauda idonta, dan tun abinda ya faru ɗazu a tsakaninsu sai ta tsinci kanta da jin matsananciyar kunyarsa. Yanzun ma dan kawai tana a firgice ne. Kamar zai ƙara magana sai kuma ya share, murya a shaƙe mai tabbatar da ya gaji da magana ya motsa lips ɗinsa a nutse kamar a fisge, “Kinyi salla?”.

Kanta ta ke girgiza masa batare da ta yarda ta kallesan ba yanzu ma. Komai bai sake cewa ba ya miƙe kawai, kamar wanda ke’a yanayin sanyi jiki ya nufi hanyar bathroom. Da kallo ta bisa ƙasa-ƙasa, mummunan mafarkin da tayi a kansa na dawo mata. (Mafarki ba gaskiya ba ne) zuciyarta ta ayyana mata, hakan ya sata sauke ajiyar zuciya ta zame ta kwanta jin sanyi na ratsa mata gaɓoɓi. Bai wani jima sosai ba ya fito, bargon data rufa ya kama ya yaye, tai saurin riƙowa tana ɓata fuska da turo masa baki. “Ni dai sanyi nake ji”. Ido kawai ya tsirama lips ɗin nata batare da ya iya cewa komai ba, kafin ya ranƙwafa a kanta slowly ya ɗauke ta cak ɗinta cikin hannayensa. Ba ƙaramin waro masa manyan idanunta tai ba. Ya ɗan harareta yana kauda nasa. Itama kauda natan tai tana kumbura bakin gaba sosai.

 

(Stubborn girl) ya faɗa a ransa, a zahiri kam fuskar ya sake tsukewa da kyau kai kace da ɗa duniya bai san miye murmushi ba. Yana direta yay fitowansa abinsa. Binsa tai da kallo, abubuwa masu yawa na mata yawo a zuciya game da shi….

 

Da ƙyar ta iya bin Season ngo ta fito bayan idar da alwalar, yana zaune a cikin kujerar idonsa kan television ɗin ɗakin. Kaɗan ya ɗaga idanunsa ya kalleta ta ƙasa-ƙasa. Duk da yaga yanda take layi tsabar baƙin hali da ƙasaitar mulki ya hanashi tashi ya sake taimaka mata. Harta ƙaraso inda ya shimfiɗa sallayar kamar bai ma san da fitowarta ba. Kallonsa ta sata ta kauda kanta, sai kuma hakan da yay mata ya ƙona mata rai. Cikin jin haushi-haushinsa ta ɗan ƙarfafa kanta, gyalen daya ajiye mata ta ɗauka ta naɗa a kanta, kasancewar abayar jikinta babu ta inda ta tawaya ta kabbara sallarta cike da nutsuwar da ke tabbatar da ta samu wadataccen ilimin addini. Shi kansa yanda take sallar a nutsu duk da wani lokacin jiri kanyi kamar zai kadata sai yaji wata nutsuwa ta ratsashi. Wani kimar iyayenta da sake ganin darajarsu na mamaye sa. A zahiri kam bama zaka taɓa ɗauka hankalinsa a kanta yake ba. Fuskar nan tai ciɗin-ciɗin ko ɗan yankar kanun mutane sai haka😏.

Tana idarwa ta zame a wajen ta kwanta hanunta dafe da kanta dake matsanancin sara mata, zuwa can kamar wadda aka zabura ta miƙe zumbur hanunta a baki, sai kuma ta nufi bathroom da ɗan gudu-gudu alamar amai.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button