Hausa Novels and Stories

Idon Naira 13

Sponsored links

Ahankali sukaci gaba da renon babyn itada Anty Maryamah din Dan kuwa saidai ace su biyu ke renon.

Wata uku Da haihuwar Maryamah tafara fita Aiki a babban guri Mai kyau da matsayi a kamfanin mijinta Dan haka kusan renon Aqeel da dawainiyarsa yadawo hannun Zainab Dan tsakanin Maryamah da jaririn nata sai dai ta bashi Nono da Yan sauran kauna da kulawar da baa rasaba Amma ko Aiki Bata zuwa dashi sbd Bata wani dadewa take dawowa sbd shayarwan datakeyi.

Zainab ce ta zama uwar renonsa da Dole da qarfi da yaji ta koya komai na kulawa da babys da hidimarsu,

Tun Tana tsoro da fargaba tareda taka tsan tsan akan kada tayiwa ‘dansu ba daidaiba harta fara sakewa tana iya Masa wasu abubuwan,

Wanka ne kawai Bata iya Masa sbd shima Tana tsoron abinda zai iya faruwa Tunda har lokacin yarone sosai Amma Bayan wanka itace goyansa,

Basa Madara,Sauya Pampers da sakasa bacci.

Ayyukanta kokuma ace nauyin dayake kanta saiya Ninku sbd lalurar renon yaro wani sabon aikine Mai wuya da taka tsantsan Amma haka take daurewa tayi dukkanin aikinta Yana bayanta Yana bacci wani lokacin Kuma Yana daki ta kwantar.

Sam batajin damuwa ko gajiyar kulaw da renon Aqeel sbd tsananin kaunar datake Masa har cikin ranta,

Jinsa takeyi kaman itace ta haifesa Kuma wahala ko Wace irice zata iya Masa Dan haka Sam batajin komai akan dawainiyarsa.

Da farko ganin yanda Zainab take shaquwa da kaunar Aqeel yasa Maryamah daukar me Reno Tana zuwa dashi gurin Aiki ta rabasa da Zainab ganin yafara wayo Yana gane Zainab din fiyeda kowa gashi shi Dadynsa ko ajikinsa Dan haka ta rabasu dan kada yayi mugun sabo da Zainab fiyeda ita.

Tashin farko Aqeel din kullum rigima yake musu harsu je Aiki su wuni su dawo baya zama

Bayan rigima Babu abinda yakeyi ko cereals dinsa da nono daqyar yake karba

saidai idan yayi barci ne kawai suke samun sukuni Amma ahakan ta dage taqi maidawa Zainab renonsa duk da ta fahimci rashin Zainab ne ke sakasa wannan rigimar ta tashin hankali.

Ita kanta zainab kusan har qaramin zazzabi tayi da aka rabata da renon nasa Dan kuwa ta shaqu dashi fiyeda komai da kowa data sani rayuwarta Bayan mahaifinta Aqeel shine Dan Adam na biyu datake tsananin ji har cikin ranta.

Mai renonsa Rabi’a tsabar rigimarsa yasa idan Maryamah Bata kusa ubansa takeci tayita yi Masa tsawa harda marin kumatunsa ko bakinsa duk tanayi tareda zare Masa idanuwa Tana zaginsa duk tabi ta firgitasa Sam ko ganinta yayi sai kuka.

Taurin zuciya Maryamah tayi taqi maidawa Zainab renon nasa duk kuwa da yawan kukan tashin hankalin dayake Mata a gida da office qarshe haka ya shide sai gasu a gadon asibiti.

Hankalin Dadynsa ya tashi sosai sbd baisan abinda yake faruwaba kwata kwata akan hakan Tunda bawani zama yakeyiba koyaushe Aiki

Idan Kuma Yana gida suna harabar gida gurin karatun addini Dan shi din maabocin karatun addini ne Yana kaunar zurfafa iliminsa akan addininsa.

Alh Asad dinne dabai San meyake faruwaba Amma dai yasan akwai shaquwa sosai tsakanin Zainab da Aqeel din Dan kuwa harshi wasu lokutan idan Yana hannun Zainab qyuya yake Masa baya yarda da kowa indai Yana hannun Zainab.

Baisan Maryamah ta rabasu ba da haka yasa driver yakawo Zainab asibiti sai gashi itama Zainab din Tana Jin kaman zatai kuka lokacinda ta ga Aqeel din kwance a gadon na asibiti Yana bacci da Alama har yunwa akwai ataredashi.

Tana zaune gefensa ya farka Yana bude ido da ita yafaracin Karo sai kawai ya fashe da kuka Yana Kiran sunanta cikin rashin iya fadan sunan sosai Dan bai wani dadeba da fara koyan magana.

Dole uwar naqi tasaka Maryamah barwa Zainab din jinyarsa qarshema daga wannan jinyar sai kawai aka yayesa daga nono Daman yayi shekara daya harda watanni goma.

Tun kuma daga ranar bata ƙara ƙorafi akan kulawar da Zainab ke bai wa AQEEL basai ma tafi jin nutsuwar zuciya akan gwarama Zainab ɗin ta dinga rainonsa don ta fahimci ta fi Rabi’a iya bashi kulawa cikin nutsuwa hakama Rabi’a komai nasa aka Ba cinyewa takeyi tace shine yaci Bayan tasan qarya take Masa Dan rigimarsama Bata Bari Yana cin komai.

Zainab kuwa daman ita hakan takeso renon nasa yadawo hannunta Dan haka taci gaba da kulawa dashi da gidan harma da masu gidan Dan yanzu Anty Maryamah din Bata zama sosai itama kullum Tana office sai yamma take dawowa idan ta fita tun safe,

Rayuwar gidan da kula da gidan duk ya dawo ya rataya akanta yanzu har cefane itace mai zuwa tayo sai a hadata da driver abasu kudin cefanan zuje har wani qaramin kauyen dakeda manyan lambuna acan suke ciko Bayan motar dasuke zuwa cefanan.,

Itace tsaftar gidan,

Itace girkin gidan,

Itace Reno dakuma wankinta Dana Aqeel harma da wasu daga cikin kayan Anty Maryamah din.

Masu Aiki kuwa saidai can can a dauki daya idan aka kwana biyu sukaga bazasu iyaba su tafiyarsu ko suyi sata su gudu Dan babu Wanda zai iya aikin gidan me shegiyar wahala idan ba itaba Dan haka Tama Dena tsayawa adduar aringa samo masu aikin sbd ganin zuwan nasu baida amfani Dan haka saita share ta maida hankali gurin bautar data saba.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button