Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai Book 2 25

Sponsored links

Auta Yana gamawa ya karkade rigarsa yace sai nayi wankan tsarki ta shafa min najasa,Dariya su Wise Suka yi Wise tace ni da Kai Amana ne Auta you be better person,Auta yayi gaba abinsa ya bar Iyamami a tsaye Kamar gunki,yaro ya zage yaci mutuncinta haka ashe fadan ma duk wannan bala’in da yake Dan ance Masa yaro ne za a aike shi,Amma maganganun Auta na karshe sun taba zuciyar Iyamami,wa’azin Auta ya shigeta tabbas abinda ya fada gaskiya ne iyaye da dama suna raba Kan yaransu su watsa zumuncin zuriarsu da kansu gashi kowa ya tsaneta babu me sonta sai yaranta su ma Dole ce ta sa.

Sera dai tace to ke Auta ya Gama Miki aiki Saura naki idan basu hakura ba ki karasa da kanki,Wise sai Murna take Yi tace ai Dole nayiwa Auta kyauta.

Umma Umma na dawo fito ki sauke min markaden geron,matar ce ta fito da sauri,dittujuwa ce Fara kyakyawar gaske ta saukewa budurwar da baza ta wuce 18yrs ba katuwa da ita kyakyawar burdurwa zankadaziya son kowa kin Wanda ya rasa Yar jajir da ita,markaden aka sauke Mata,tace Umma Aunty Cele Ashe sunfi wata uku ma da tafiya ita da kaka,Umma Murmushi tayi tace Omaira kyale Rufaida bata Jin magana amma ni Banga laifinta ba ko kadan mahaifinku ne da uwarsa sune da laifi duk abinda tayi tana da hujja laifinta Daya da take hadawa dani,dariya Omaira tayi tace kin San Rannan daga naje nace Cele ta bani awara da kudina fa Umma wallahi ta kamani da kokawa Wai ubana nane ya bata jarin nima kin San bani da hakuri naki kyaleta Muka Yi ta kokawa a titi shine ta fasa min goshi ta min dukan tsiya Wai na rainata shike nan duk inda ta gani sai taci ubana har bana so mu hadu a hanya da Cele sabo da bata gajiya da fada Allah ya taimaka ma ta tafi makkah,Umma tayi dariya tace ku dai na rasa inda kuka yo gadon masifa sai dai ubanku kuka yo, ku goma na Haifa cif duk Mata Kuma duk Babu me sauki duk da ban San dayar ba tana raye ko tana mace oho ko tana gidan marayu Ina aka jefar min da ita oho sabo da Kawai Ina haifar Mata amma ai Alhmdllh tunda dai Ina da guda Tara na suna nan bazan yiwa Allah Butulci ba akan daya ta bace,Cele ai Dole tayi masifa an cuceta ne bana ganin laifinta wlh,Nima Kuma an shiga hakkina an yiwa Allah shishigi,Omaira tace karki damu Umma gamu dukkan mu zuciyar maza ce da mu mace daya ma gayya ce a cikinmu dan ma duk sunyi aure yanzu mu hudu ne Kawai a gabanki Banda Cele da taki aure yanzu maga shegen da zai taba Mana uwa da anyi tsiya.

Gyaran muryar me gidan suka ji ya shugo Yana muzurai wani fari dogo me Dan jiki tun kafin ya karaso ya fara tsawa Kai Kai….hayaniyar me nake ji ne haka ne baki da aiki sai dai kisa Yara a gaba kina zance gashi Nan duk yaranki ba na gari aikin banza wannan ba tarbiyya bace ki dinga munafunci da yaranki,duk Wanda yaci namana ban yafe ba nasan gulmata kuke yi,Umma tace na rasa gulmar Wanda zanyi sai Kai Ina abin gulma a wajenka,Hanifa ce ta shigo sanye da uniform ta dawo daga school tayi sallama ta wuce dakinsu,Can sai ga Rahma da Raheema sun shugo su biyu Yan matasan mata sun shugo suna fada akan biro daya ta sacewa daya biro,Omaira ce babba a ciki tsawa ta musu Kai dalla kuyi Mana shuru muna fama da talaucin mu Kun dame mu,Abbansu ne yayi magana yace ai ni rabon da naji dadi a duniya tun kafin nayi aure gaba daya banyi dacen mace ba,gashi yaran ma banyi dace ba gaba Daya an cika min gida da gwari Mace ai gwari ce, Ni kenan kudina su Kare a siyen gado da katifa kullum a bikin Yara nake har an gaji da zuwa daurin aure gidana,gaba Daya Kuma ba wacce ta auri me kudi duk talakawa suke kawo min ko wacce da kyar take Sha a gidan aurensu Ina za a iya taimakon Iyaye, Uwa ce ta fito daga dakinta mahaifiyar Abba kenan tana wani gadara tace Kai Kam sai dai Allah ya biyaka a lahira mace bata da aiki sai haifo Yara mata da wannan haihuwar ai gwara babu, sai da tayi Yan biyu a jere sau uku sabo da bala’i, su yaran ma da suna da kashin arziki da sai ace da sauki amma duk talakawa suke kawo mana, gashi duk wacce ka aura Suma duk matan suka haifo ta Gama cinye su da baki, Abba yace ai gashi nan wlh sai an aurar dasu tas Zan dinga ciyar da ita tunda haihuwar Mata ta zaba to sai dai su ci da kansu abinda Naga dama shi zan bayar a gidan,Umm ta kalle shi tare da tabe baki tace jahilci yafi hauka ciwo Allah ya ganar da ku, dake Umma itama bata da tsoro bata barin ko ta kwana Indai aka Mata.

Maheerah tayi tayi ta fita Cele ta tare hanyar haka ta juya ta koma Palo ta zauna tace Kuma Ni Zan fita ba ke ba gantalalliya Albakaratun,Al Himarun jaki to ke jaka ce me kawo mazan banza tana jinta Maheerah tayi Shuru tana saka muguntar da zata hadawa Cele,Cele Kuwa shiri tayi cikin Abaya tayi rolling ta bude kofa ta fice tare da cire key din kofar ta kulle Maheerah ta baya tayi ficewarta daga gidan gaba daya, ta fito taga hadadden gari ta bude hannaye tare da daga Kai sama tace iskar yanci haba har naga rana ai na samu sinadarin vitamin D a jikina,ta Fara tafiya tana nishadi tana zaga layin gashi layin manya ne tana tsoro Kar ta bace sai da ta gama yawonta mutane sai dai daiku ta gaji da yawon ma tace bari na koma gida Banga kowa ba ta juya kenan taji ance ke daga ina,sai data tsorata ta zaci gamo tayi ta juyo da sauri taga mace dattijuwa bahaushiya baka da ita tana yawo da katuwar jaka,harshen larabci ta juya taga Cele Fara ko ruwa biyu ce bata Jin hausa,Cele tace Sannu bakuwa ce ni ban fara Jin larabci ba,matar tace kin San a state din nan kazamin kame suke Yi idan Baki da sheda wallahi ki daina fitowa,Cele tace asibiti nake so naje wallahi bani da lafiya Kinga cikina kullum sai Naga ya Kara girma Kuma ayi ta motsi a ciki,Matar tace ni kin ganni Yar Jigawa ce ni mijina ne ke aiki a nan ya taho Dani muke zaune Amma unguwar da muke ba irin wannan bace ta manyan larabawa unguwa ce ta Yan fake fake, Cele tace okay Ashe kina Jin larabci? Matar tace ae Ina ji ni,tace Dan Allah ki Zama Aunty na Zan dinga zuwa kina koya min,Matar tace hmm baki da shedar Zama a kasar su wlh kamaki zasu yi matsayinmu na hausawa Zan dai dinga zuwa duk sati Ina koya Miki ki tanadi biro da takarda Cele tace na gode,Matar tace Sunana Hajiya Hauwau,Cele tace Rufaida Cele sunana,Zo muje na nuna Miki inda nake aiki Ni Yar aiki ce,Hajiya Hauwa tace to Suka taka Cele ta nuna Mata gidan,Matar ce tace muji cikin naki da yake girma ta taba cikin Cele tace Kan Uba ai ke ciki ne dake,waye ya Miki ciki Yar Nan? Cele tace ban gane ciki ba nifa bani da lafiya wallahi ban san da Namiji ba ma Sai dai idan ciwon koda ko Hanta ne ya kamani ko ciwon sanyi,Hajiya Hauwa tace wanne irin ciwon koda haihuwata bakwai nasan ciki nasan komai haba yarinya

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button