Hausa Novels and Stories

Gaba da Gabanta Complete Hausa Novel

Sponsored links

Dattijo ne wanda a ƙalla zai kai shekaru hamsin, zaune akan benci hannunsa riƙe da ‘yar ƙaramar radio, yana saurara.

 

 

 

Wata Haɗaɗɗiyar mota ce ƙirar Annoconda, aka kwararo dogon layin da Ita, wanda gudun da motar take ta haddasa tashin wata ‘yar ƙaramar guguwa.

 

 

 

A ƙofar wani makeken gate motar tayi birki, aka fara wani irin horn, sai kace yaƙi.

 

 

 

A gigice ya yasar da radiyon da ke hannunsa, ya miƙe a zabure ya nufi gate ɗin, yana gaganiyar buɗe shi.

 

 

 

Yana buɗe gate ɗin, aka turo hancin motar, zuwa wani shiashi na gidan.

Wata matashiyar budurwa ce ta fito daga Motar, gata nan dai kamar bata cin abinci, ban da yanayin jikin ta da kuma kayan da suke sanye jikinta, ba ka ce mace bace, saboda tsabar rama, sai dai fatar jikinta za ka kalla ka gane ‘yar hutu ce, da ga ita sai doguwar rigar material, da hula a kanta tana sanye da wani uban takalmi me shegen tsini.

Ta nufo gurin da dattijon nan yake kokawar maida gate ɗin ya rufe tsigil- tsigil, tana zuwa ta ƙare masa kallo sannan tace “wai kai dan Allah wani irin mutum ne? Kai ta abu kamar mara jini a jiki ko wanda baya cin Abinci? Duk Abincin da kake ci kamar gara amma ba ka da wani Amfani iye?, wallahi daga yau na kuma dawowa, ka barni a waje ina horn sai na tatala maka rashin mutunci, aikin banza ni ban ga amfanin ajiye ka a gate ɗin gidan nan ba, Daddy ya nace lallai sai kai za kai gadi”

Shiru dattijon ya yi, ya sunkuyar da kai, yana jin yadda Yarinyar ke surfa masa fitsara, ‘yar da ba ta fi ‘yar cikin sa ba.

Ta buɗe jakarta ta ɗakko dubu uku ta zubar da ita a ƙasa, ta ce “gashi nan ka ɗauka ka siyo mini Irish, za’a dafa mini, na store ya ƙare”

 

 

 

Cikin girmamawa ya duƙa ya ɗau kuɗin yace “ranki ya daɗe sai dai ban gane me ki ka ce in siyo ba”

 

 

 

Ta kalleshi a wulaƙance sannan ta ce “Kai abun naka ma ya yi maka yawa, to dankali nake nufi, kai Allah ya rabamu da rayuwar ƙauye rayuwar jahilci”

 

 

 

Bace mata uffan ba, ya juya ya fara tafiya, ita ma ta nufi hanyar shiga cikin gidan.

 

 

 

Wani ɗaki ta shiga cikin muryarta ta iyayi take faɗin “Mummy, Mummy”

 

“Na’am har kin dawo?”

“Eh na dawo, ina wannan yaran suke?”

 

 

 

“Suwa kenan?”

 

 

 

“Maids ɗin nan mana”

 

 

 

“Suna sashin su”

 

 

 

“To na bawa wannan tsohon kuɗi ya siyo mini Irish, dan na gidan nan ya ƙare, ni kuma shi nake son ayi min fatensa da dafaffen ƙwai in yi lunch da shi”

Mummy ta ce “shikenan, Allah sa kar ya yi miki shirme”

 

 

 

“Wallahi kuwa, ni wallahi da za’a bi ta tawa kawai a sallami mutumin nan, shekara da shekaru ya ci abun da ya ci ai, Amma Daddy ya dage lallai sai shi ze din ga gadin nan, dan Allah Mummy ki ba shi shawara a canza tsohon nan”

 

 

 

Zare ido Mummy tai tace “ke Fadila rufa mini Asiri ina zaman zamana, ba ruwana”

 

 

 

Ɗan tura baki ta yi, sannan ta ce “Any way, bari in je in kwanta dan na gaji sosai, idan ya kawo sa karɓa, ayi mini fatensa a saka yaji sosai, sai a dafa mini ƙwai guda uku a ɗora a kai “.

 

 

 

Mummy ta ce “Ina fatan kin gaya musu da kan ki?”.

Fadila tace “Ai ni ƙarasawa kitchen ɗin ma wahala zai bani, ni dai kya gaya musu”. Ta ƙarasa Maganar tare da juyawa, ta bar ɗakin.

 

 

 

Tana zuwa nata ɗakin, ta jefar da takalmanta a tsakar ɗakin, ga gurin ajiye jakunkuna, amma ta yi jifa da ita wani gurin, ta cire hular kanta ta yar a ƙasa, ta haye kan ɗan matsakaicin gadonta tana hamma, tare da yin miƙa”.

 

 

 

*******

 

Zaune take a gaban murhu, tana tura busassun kararen tafasa, sai uban hayaƙi ne yake tashi, sai fifita wutar take da wani ɗan ƙaramin murfin bokiti, tana jan majina, ga idanunta sun yi jawur saboda yajin hayaƙi.

 

Can da ƙyar wutar ta kama, a hankali ta furta “Alhamdilillah” ta sake gyara zaman tukunyar da ke kan murhun.

Sai da ta tabbatar wutar ta kama sosai, sannan ta miƙe ta tattare duk tarkacen da ta tara a gurin, ta gyara gurin, ta bar iya murhu da kararen da ke cikinsa.

 

 

 

Ta koma ta ɗakko garin masara a cikin buhu, da ƙwarya da rariya, ta samu guri ta zauna akan tabarmar kabar da ke shimfiɗe a ɗan ƙaramin tsakar gidan, ta fara tankaɗe.

 

 

 

Wata farar mata ce ta fito daga wani ɗaki, hannunta riƙe da carbi, take faɗin “Masha Allah, yarinyar kirki wutar ta kama kenan?”.

 

 

 

Shiru tayi ba ta amsa ba.

 

 

 

“Ke Amina magana fa nake miki”.

 

 

 

Firgigit ta dawo daga tunanin da take, ta fara kokawar kwance buhun garin masarar nan.

Matar tace “Amina, wai tunanin me kike yi haka ne?”.

 

 

 

Wadda aka kira da Amina, ta yi ajiyar zuciya tace “Inno, Wallahi tunanin jarrabawar placement ɗin mu nake yi”.

 

 

 

Inno ta taɓe baki tace “Ai sai ki yi tayi, wannan bokon ko ita ce karatun shiga aljanna yaci ace kin haƙura haka”.

 

 

 

“Inno, dan Allah ki fahimce ni, ina matuƙar son karatun nan ne, dan Allah ko rance ne, ki aro kuɗin nan, in biya jarabawar nan, kafin Baba ya turo kuɗi”.

 

 

 

Inno ta ce “ba abunda zan aro Wallahi, shegiyar boko da bata da wani amfani, kin yi abun da ki ka yi, sai ki haƙura haka, ki dawo ki yi Aure, amma ana ta ƙananun maganganu akan ki a garin nan, saboda baban ki ya ɗaure miki gindin wani wai sai kin yi boko, har yanzu banda tarkacen takardu, ba uban da ki ka ajiye a bokon, shekara da shekaru kina galmashura a titi yawon boko, kullum sa dai ki kawo takaddun banza ki ajiye

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button