Hausa Novels and Stories

Idon Naira 18

Sponsored links

Tun Haj maryamah na tafiyenta da basa wuce kwanaki zuwa satittika yanzu wasu lokutan takanyi doguwar tafiya qasashe Wanda suna share wata daya,biyu,uku,har fiye Basu gantaba,.

Ana cikin hakan Wani aminin Alh Asad dayake babban Justice dake Abuja ya fito neman auren,

Da farko Bata aminta ba Amma ummanta da hajiyar su Alh Asad suka tilastata tareda nasihu tukuna ta amince akai auren Amma shi Yana can Abuja da iyalinsa itama yabata ware Mata nata gidan Amma Bata wani zama sai can can idan taje abujar ta Dan zauna tayi kwana biyu kokuma idan shi yazo Mata

Haka dai aure yake kamar Wadda akaiwa Dole a auren

Shima Justice Ayub Nasir din bai wani damuba sbd sanin uzurirrikanta da Kuma dama shima baya wani som zama.

Ita Kuma Zainab Hakan yasa ta sake dagewa sosai gurin tarbiyantar da Aqeel Wanda yaketa qara girma Yana cigaba da karatunsa Tunda yazama dai itace tamkar uwa Kuma ubansa.

Aqeel Kyakykyawar Yaro ne Mai nutsuwa da rashin son shiga cikin mutane sosai bare Wasa cikin yara ‘yan uwansa,

Kasancewar yanayin yanda rayuwar tasa ta taso yasa yake shiru shiru mara son hayaniya,

Baida mahaifin dazai tsaya masa ya zama jagorarsa,

Wadda itace ta haifesa Sam batada lokacinsa bare nuna Masa kauna da shakuwa,

Wadda yakewa kallon uwa Kuma mahaifiya agaresa Tana cikin wani irin qunci da rashin yancin Kai dazasu sake suyi rayuwarsu,

Duk gata da daular da ake kashewa gidan kamar baasan zafin nemansuba bai saka Aqeel din ya taso cikin Jin cewar ba Maminsa ce mahaifiyarsa ba shiyasa maimakon yayi rayuwar Jin dadi saima yake rayuwar kadaici kaman Maminsa suna rayuwarsu da Jin basa buqatar komai

Ita Zainab batada wani buri ko kwadayi bare shaawar wata rayuwar

Ko Aqeel dinta aka Barta dashi baa rabasuba batada doguwar damuwa.

Dukkanin wahalar da ta sha tun yana ƙarami har kawo yanzu da ya fara zama babba bata taɓa jin daidai da rana ɗaya ta gaza ko ta gaji da hidimarsa ba,

Shi AQEEL Yaro ne me tsananin son a kula dashi tareda lallabasa,

Hakan wata dabi’arsa ce data lura ta fahimta tun Yana qanqani shiyasa tafi basa mahimmanci da kulawa fiyeda komai a gidan.

Duk masu aikin da ake kawowa gidan basa wani zama tafiyarsu sukeyi sbd dagasu sai Zainab

Aikin kawai akeyi Babu Mai gidar gashi duk da batanan aikin Babu Wanda aka Dena saima qaruwa Dan kuwa har kullum baa Dena karatu a gidanba saima qaruwa da jamaa sukai kusan duk manya Yan anguwar dake karatun da ‘yayansu manya a gidan Malam Sanda ke basu karatun kullum tsakanin magriba zuwa ishai,

Hakama dangin Alh Asad maza kusan dukkaninsu anan gidan ake karatun dasu kullum Wanda sbd sakawa rayuwar gidan ido yasa suka maida sallar magriba dinsu zuwa ishai anan suma suna qaruwa da karatun.

Duka wannan lamarin dayake faruwa a rayuwar gidan har tsawon wannan lokacin babu Wanda yasan Zainab jinin Haj maryamah dince

A matsayin me Aiki suka santa tun kuruciya har kawo yanzu data girma zama mace shiyasa Babu Wanda yake ganin girma ko wani mutuncinta saima mayyar kwadayayya dasuke kallonta Dan uwar wahalar datakesha suna ganin kwadayi kawai zaisa ka zauna irin wannan rayuwar.

Qarin abinda yasa wasu masu aikin da Dama dasuke tafiyarsu shine duk wahala da biyayyar Zainab Haj maryama Bata yabawa bare nuna wani Jin dadi sai jikinsu na mutuwa da tsoron Hakan,

Wasu Babbar sata suke zubawa su gudu wasu Kuma salin alin suke tafiyarsu Dan Zainab dasuke karkashinta meta zama duk shekarun bare suda abin duniya suka fito nema ba Wai zaman bautar banza ba.

Babban abinda yaqara saka Haj maryamah yiwa Zainab tsanani akan rashin barinta fita shine gudun tasamu mijin aure a lokacin tayi aure tabar Aqeel Wanda tasan bazai taba zamaba Zainab ta tafi tabarsa

Tasani Sarai bin Zainab din zaiyi Koda zata hauka ne akan bataso tasan saiyabi Zainab

Itakuma bazata iya Bari danta yayi rayuwa a qazamtaccen guriba.

Sabuwar dabia Mai karfi data shigeta shine tsanar duk wani Abu daya shafi gwagwarmaya da mutanen daba nagartattuba…

Ta tsani zuwa ko irin guraren dasuka shafi irin Hakan shiyasa ma gidanta yasake samun tsaro da dokoki

Ko masu aikin da ake kawowa batason wadda Alama ta nuna tagama lalacewa da sanin maza,

Sam Bata kaunar irinsu

Qyanqyaminsu takeyi tareda musu fatar shiriya daga nesa shiyasa duk tsanani idan Tana gida batacin abincin kowa saina Zainab itama sbd tanada tabbacin tsarkinta da tsaftar rayuwarta da Bata gurbata tako Ina.

Rayuwarsu tafara sauyawa ne lokacinda haj Maryamah ta nemawa Aqeel wata tsadaddiyar makarantar boarding Amma Kai tsaye yaqi yarda da makarantar bakuma sbd kowa yaqi makarantarba sai Dan Maminsa wadda yasan wanu gata da sanyin datake ji duk sbd shine Dan haka akai akai Amma yaqi yarda.

 

 

 

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button