Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 87

Sponsored links

Daukan wayar yayi ze fita kenan yaga kamar wani ya motsa a cikinsu, da sauri ya matsa gefe yana boye wayar a aljihunsa…….

Sai daya tabbatar babu wanda yake motsi sannan ya sake fita ya kuma haurawa ta inda ya shigo yabar prison din gabadaya……

Saida ya bar area din sannan ya kunna wayar amma taki tashi saboda rashin charji……

“Shit!”….

Deen ya fada yana dafe kansa….

Ganin bashi da yanda ya iya ya shiga tsaida cab dan ya tafi Transcorp yayi charji….

Haka akayi kuwa saidai ko kafin ya isa Transcorp Hilton shadawa ta kusa, dole ya hakura ya bari sai washe gari zuciyarsa cike da taraddadin yanda mami zasuji idan sukaje basu gansa ba, be gama fita daga wannan ba ya sake daukowa kansa wani, duk abinda ze faru ya faru kawai…..

Karfe ukun dare ta farka as usual, alwala ta dauro tazo ta tada sallah kamar yanda ta saba duk dare…. Hawaye take sosai tana addu’ar Allah ya yaye mata damuwarta kaman yanda ta saba duk sanda zatayi addu’a, gashi ko zaa kasheta batasan meye damuwarta ba, tasan dai tana cikin damuwa sosai…

Tana zaune tana karatun qur’ani har aka kira sallar asuba, tashi tayi tayi sallah sannan ta dora da azkar…

Mikewa tayi tana ninke sallaya bayan ta idar, haka kawai taji tanasan komawa bacci ranar abinda bata saba ba….

Har zata kwanta wata zuciyar tace ta tashesu suma suyi sallah, bed din eesha ta nufa dan batajin zata iya wahalar tashin sauran dan tasan bata lokacinta kawai zatayi ba tashi zasuyi ba…..

A hankali ta janye blanket din eesha ta dan bubbuga kafarta….

Bude ido eesha tayi tana kallonta tace;

“You want something?”….

“Sallah!”

Ta bata amsa tana mikewa….

Tashi tayi tace;

“Shiyasa nayi missing dinki wallahi, harna manta when last nayi sallar asuba da wuri”…..

Fatima zainab batace komai ba ta koma ta kwanta eesha na cigaba da surutunta….

Itama sallah tayi tazo ta kwanta kamar tacewa fatima zainab yau bazata fita da wuri bane tadai ja bakinta tayi shiru….

9am dot haka agogon dakin ya nuna, farkawarta kenan ta fito tana shirin yin wanka…

Sai 10am sannan ta gama shiri, shirye take tsap cikin wani maroon abaya me ratsin gold, kanta sanye da wula golden, sosai tayi kyau kamar ka saceta ka gudu….

Tana jin ido na rakata duk inda tayi amma tayi kamar batasan sunayi ba, gabadayansu sun kasa dauke ido akanta kadama billy taji labari, ita kadai tasan me takeji aranta, ta maimaita dama haka take aranta yafi sau a kirga…..

Sosai take jinta wani iri yau kamar wacce aka chanja, abu daya ke damunta irin kallon da ake binta dashi baga yan hostel din ba baga yan dakinsu ba, ta rasa mene a jikinta da ake kallo? Saidai kuma abinda taga dama shi zatayi, sanda take lullubinta waya sata? Babu! Toh yanzu ma da taga damar denawa ba wanda ya isa ya hanata….

Dan karamin veil din abayar ta yafa sannan ta dauki car key ta fita…..

“Hmmm kedai bari wallahi an tashi kaina, yo akanme bazata dinga boye kanta ba, eesha kinga abinda nagani kuwa?”……

 

“Ai dama kinfi kowa ganin abubuwa, toh me kika gani?”…..

 

“Yanzu idan na fadi abinda nagani sai kicemin yar iska, but seriously I need a hookup with her, wallahi ko nawa ne zan biya”……

 

“Umaima ana magana dan wannan zance yafi karfina kinga wai ko nawa ne zata biya”……

 

“Bar yar is wannan tafi karfin tsohonki yarinya bare ke yar iskar karshen zamani, if e sure for you kije ki sameta ki fada mata, mu ba ruwanmu”….

 

“Ya isa kar ki kuskura ki sako min uba a wannan lamari inba hakaba sai insa a dauremin ki yarinya inga uban da ze iya fito dake, kuma duk yanda zanyi in sameta sai nayi kawai ku zuba ido kusha kallo”….

Tana fadin haka taja tsaki ta fita daga dakin………

Tun asuba Mami tazo tashinta tayi sallah, tafi minti goma tana knocking ba’a kulata ba hakan yasa tayi sallama tashiga…. Saidai me? Kamar ba’a kwanta a gadan ba, murmushi tayi tana tinanin maybe tana toilet, probably irin mutanennan ne masu gyara gado kafin suyi alwala, tinanin haka yasa ta fita kawai……

Wata maid aka tura taje ta kirata suyi breakfast around 10am dake sun makara ranar……

Suna zaune basu taba komai ba suna jira tazo, sai ga maid din ta dawo tace musu bakuwar is no where to be found….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button