Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 102

Sponsored links

Ta tarka sau daya yin titsari taga baya dakin, sai hakan ya kara mata nutsuwa. Sai dai kuma Can tikin dare ko tace gabanin asuba taji a mata wata irin runguma data sakata farkawa a firgice. Gabanta faduwa yay lokacin data tabbatar da shine. Muryarta har kakkarwa take na son magana. Sai dai ma kafin ta furta ya ce mata “Shilli!!” dole ta hadiye tai luf. Yamutsata ya dingayi da jagwalgwalata yanda yake so, ta riga ta gama kaiwa makura a rudewa. Sai dai bai mata komai ba har aka kwala kiran salla ya mike a gadon ya nufi bathroom. Kusan mintuna goma tana nan kwance lamo da share hawayen da tasha na tsoro ya fito da alamar wanka ma yayi.Luff tai bata motsa ba har ya gama tsane gashin kansa ya wuce wajen canja kaya. Wuff tayi ta tashi zuwa bayi, lokacin da ya fito cikin shirin massalaci ya nufi gadon da shirin tadata ya samu wayam. Shi yama zata barin akin tai, sai kawai ya fice abinsa gudun kar ya makara kuma.

Koda ya dawo da ga salla Gym ya wuce abinsa cike da kokarin danne abinda ke damun gangar jikinsa da ruhinsa. Wani irin mugun motsa jiki ya ringayi na tashin hankali duk dan ya samarwa kansa nutsuwar manta abinda ke bijiro masa. Sai dai maimakon samun nutsuwar da yake bukata hankalinsa ne make cigaba da tashi. Ya dauki tsawon awa biyu a Gym din kafin ya fito ,ya koyi zufa sharkaf kamar wanda iyo a cikin ruwa.Tana tsaye gaban gadon tana canja bedsheet ya shigo da sallamar nan tasa ciki-ciki. Dan juyowa tai kadan ta dubesa sai kumata dauke kanta. A can kasan makoshi ta ce,

Ya fada a takaice yana cigaba da mata kallon mamaki. Kamar zai share dai ya kasa hakuri.”Waya saki wannan aikin?”. A dan shagwabe tace, “Ni na sa kaina, shike nan mutum bazai motsa jikinsa ba sai dai komai ai masa ni banaso”. Takowa yay gabanta gab sosai, tare da riko hanunta da ke rike da filo.Dagowa tai ta kallesa.Zata maida ya girgiza mata kansa. Dole ta hakura, sai dai tai kasa-kasa da idanunta.Shikam dai idanunsa kyam kan kyakykyawar fuskarta da yau dai ta gama komawa normal kamar komai bai faru ba, ya dan matsa hannuna hankali yana dan huro iskar bakinsa kan fuskar tata. “Akwai muhimman ayyuka da yawa da zaki motsa jiki ai ba sai wannan ba Niger”.

Fuskarta a dan narke ta dago idanunta da kyau tana dubansa, “Wannan ma fa Mammy tace ni ya kamata na dingayi yanzu ba amintaccenka ba. Nima kuma kaga dai a gida Ummu ko mu bata yarda mu gyara cakin Babiy,ko Bata da lafiya sai tace bari ta danyi ko sama-sama”.

Gaba daya ta sake narkar da shi a halin da yake ciki, bai ma san sanda ya furta, “Kowane salonki kasheni yake autar mata”. Yanda ya fada a narke da kai hannunsa ya shafo jikinta sai taji kunya. Da sauri ta juya masa baya tana rufe fuskarta da tafukan hanunta. Shima murmushin yayi ya ajiye filon yana nufar bathroom. Sai da taji shigewarsa sannan ta bude idanunta ta cigaba da aikinta. Haka kawai take jin kanta cikin wani irin nishadi yau.

“Mammah wai yau ma zakije zaman kotun nan kema? Naga kamar kina jin kafar nan sosai fa?”.

Dan murmushin karfin hali Malikat Haseenat ta saki idonta akan Daneen Ammarah mai maganar. “Karki damu ai bawani ciwo take mai yawa ba. Ke dai yi sauri ki bani kunun nan nasha, kin sanshi dan ka’ida ne akan bin lokaci”.

Yar dariya Daneen Ammarah tayi kawai, Da ganta itama zaka fahimci tana cikin farin ciki. Daga ita har Malikat Haseenat din tun jiya fuskokinsu sun kasa daina murmushi, da dare kam zama sukai suka ding hirar Iffah. Su kansu sun kasa gane ta yanda akai yarinyar ta shiga ransu matuka har haka, kuma take ma kara shiga a kullum musamman ma ita Daneen Ammarah din da kwanakin nan taketa mafarkai da ta kasa gane kansu…

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button