Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 107

Sponsored links

tare da kwanciya luff a faffadan kirjinsa tana shakar daddadan kamshin turarensa mai saka zuciyar mai shaka nutsuwa

_Oh oh su Iffah an waye an manta da mu dangi

Mammah duniya abin tsoro ce why, duk da mun jima da sanin Jasim baya kaunar Abni sai yau din da komai ya fito fili ya bani mamaki. Har zuciyata iya abinda nake kallonsa da shi shine nuna adawa kawai ga mulkin tunda shine burinsa. Amma why ban taba kawo zai iya shirya halaka rayuwarsa ba haka. Wace irin rayuwa ce wannan wai dan uwanka jininka ya zabi cutar da kai akan abin duniya mai yankewa. Wai ina mahaifinmu da ya zama sanadin kawomu duniyar ma? A da shine a wannan kujerar, amma ya shude kamar ba’ayisa ba, aka daura dan uwanmu, shima ya shude kamar baiyi ba, idan sukai hakuri shima wataran bashi bane anan din. Bazan boye miki ba Mammah,zuciyata ta fara min sake-sake da kokwanto akan rasuwar Haysam Akhi, haka Zawjata-almilk da muka rasa, anya kuwa hakan baida alaka da su Jasim Akhi ya karba makamancin tayin da muka jima da tsigesa a cikin jininmu?. Dan zuciyata ta fara rabuwa biyu bayan zargin mushirakar can data dade da shudewa a tarihinmu kamar akwai wata mai irin al’amuranta a yau zagaye da wani namu”.

Malikat Haseenat da ke ta faman jinjina kai taja ajiyar zuciya mai karfi tare da fesar da iska zazzafa da ga bakinta. “Tabbas duniya ta cancanci zama abar toro kam Ammarah, nima kuma kamar ke zuciyata ta fara rawa, ta fara rawa da wannan gabar har inajin ni kaina ban yarda da kaina ba. Tabbas mushirikar can ta shude ita da tarihinta, amma sai zuciyata ta gagara nutsuwa da hakan duk da tsahon shekarun nan da suka shude da kasancewarta.Babu abinda Jasim bazai iya aikatawa ba,musamman idan na kalla irin mugun zaman da mukai da mahaifiyarsa a masarautar nan. Dan haka shima kam yanzu abin tuhuma ne. Sai dai akwai wani furuci da yarinyar nan tayi yafa tsaya mun a rai, tun dazun kuma yake mun kai kaWO….

“Wane furuci kenan Mammah?”.

“Furucin bibiyar gawar Zawjata-almilk ta karshe da muka rasa, inda ya zama sanadin haduwarta da Jasim. Lallai ina bukatar ganawa da Zawjata-almilk”.

Shiru Daneen Ammarah tai tana kallon Mammah, sai kuma ta nisa itama zuciyarta na mata kai kawo akan hakan. Eh tabbas wannan furuci abin a bibiya ne, dan sai a mahanga ya ke da nasaba da abu biyu. Shi kansa Jasim suspect ne a wannan case din shima. Duk da dai duk Zawjata-almilk na baya da suka rasa ransu suke fara zuwa su ganta kafin kowa.

Firgigita ta daw hankalinta sakamakon tabatan dan Malikat Haseenat tayi, taja ajiyar zuciya mai nauyi da sauke numfashi. “Yi hakuri mammah, why na tafi wata duniyar tunan nima. Za’ai bincike ga Ibnati dinne? Ko kuwa ya kike nufi?”.

Kai Malikat Haseenat ta jinjina da fadin, “Fara nemo min ita a waya”.

*Har yanzu Iffah na kwance a kan gado cike da farin ciki da nishadi kira ya shigo a landline din dakin. Wayar ta kalla kamar bazata tashi ba. Sai kuma ta mike lokacin da take gab da yankewa ta daga. Kin yin magana tai, sai da Daneen Ammarah tai sallama sai kuma duk ta rude. “Lah Mamy kece, Barka da wannan lokaci a gafarceni”. Murmushi Daneen Ammarah ta saki mai sanyi da ga can tamkar Iffah’r na gabanta, tana matukar kaunar yarinyar nan ta yanda ita kanta ma bata san adadi ba. A hankali ta nisa da sakin ajiyar zuciya ta ce, “Ba komai Ibnati, Mammah ce ke bukatar magana da ke daman”. Tamkar Iffah na gaban Malikat Haseenat ne cike da girmamawa ta gaisheta duk da yanzun nan suke rabuwa da ga zaman kotu. Da ga can ta amsa mata cike da nutsuwa da dattakonta, kafin ta aura da fadin, “Mijinki ya shigo ne?”. A hankali Iffah da kalmar ta bama kunya da yi mata nauyi ta ce, “A’a Mammah”.Murmushi Mamma ta sakeyi da gyada kai da fadin, “Idan har bakya wani uziri bayan sallar isha’i ina son ganinki”. Cike da girmamawa ta ce,

“To Mammah insha ALLAHU”.

Shiru tai tana kallon wayar bayan ta yanke.Zuciyarta sai faman mata kaikawo take da tunani kala-kala. Sai kuma ta dage gira da dan tabe baki tana ajiye kan wayar ta mike. Ficewa tai da ga dakin ta nufi can saman ginin dan wajen na matukar kayatar da ita. Tana kaunarsa fiye da kowane waje a masarautar.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button