Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 112

Sponsored links

Idanunsa da ke lumshe tun sanda ta daura hanunta saman fuskarsa ya bude a hankali,sunyi zajur fiye da yanda ya shigo da su a dan birkice. Hannun ya kamo yana kallonta, cikin tsananin kasala ya daura lips dinsa a tsakkiyar tafin ya sumbata. Sai da ta matse jikinta tsabar vanda lininta vAv wata irin vamuitsawa har cikin fara son kwatar kanta. Sai dai kuma babu hanyar samun wanna damar da ga jarum Shin yaya lafiyar giwa da ma. Balle kuma ita da kanta ta balle likin.

Duk yanda taso tuna masa dinkin dake a tare da ita babu alamar yana ma iya jinta balle fahimta. Burinsa kawai yake kokarin cimmawa a cikin rufewar idanu

Da karfi, karfin karfi yake buga kansa a bangon dakin kurkukun mai tsananin duhu da ta iya karamin windown kawai ake iya gain dan ziririn haske. Gaba daya zuciyarsa ta bushe, zafi

yakeji a cikinta mai tsananin tururi dake kona zuciya. Shi shi Jasim ibn Abdul-majeed Aliy Qutb ne wata karamar yar iskar yarinya yar cikin cikinsa tai sanadin kawowa cikin kurkuku. Shi Arshaan da ya koya sanin kansa a wajensa zai yima cin amana? Shi hadiminsa da ya dauka tsahon shekaru yana kyautatama zaici amanarsa a gaban makiyansa. Wace irin wannan, mai tsananin duhuwa da babu lissafinta a cikin duka lissafe-lissafensa. Ta yaya shi Jasim in Abdul-majeed Aliy Qutb zai yi irin wannan faduwar bakar tasan a gaban karfin ikon dan makiyansa kuma makiyinsa.

Cigaba da buga kan yake da karfinsa yana ihu mai tsananin karaji da ya saka masu tsaron dakun kurkukun nasa da Tajwar Eshaan ya bada umarnin bama tsar mai tsananin tsauri tsora. Cikin karfin hali daya a cikinsu ya dan leko, ta dan hasken da ya hasko da ga karamin windown ya hango fuskar Miran Jasim da tai wani irin jage-jage da jini dan ya fasa goshinsa. A zabire yay baya yana zazzaro idanu. Yan uwansa ya sanarma, babu bata lokaci sukai kiran shugaban jami’ai suka sanar masa dai-dai da yanke jikin Miran Jasim da jini ke rinjayarsa va fadi kasa….

Rungumeta yay tsam-tsam a cikin jikinsa idanunsa a lumshe. Jin kukanta yake har tsakkiyar zuciyarsa. Dan kuka take sosai five a daren shekara jiya kasancewar yau fami yay akan ciwo.

Ta fada cikin kuka. Yanda tai magana tana sake barke masa da kuka ga hawaye shabe-shabe harda su majina ya sa yaji dariya na yunkuro masa. Kamar ba yanzu ta gama iyayi a kotu ba,dan duk abinda ta dingama Miran Jasim akan idonsa ne tsaf. Amma jiba yanzu a dan abinda bai taka kara ya karya ba ta koma abin tausayi.Ya fahimci sai ya dage matukar dagewa akan dorata a irin layin da yake bukata ta hau inba hakaba ragguwa za’ai, bakinne kawai cike da zance da tsiwa. Bashi da burin sake wani auren bayan ita, dan haka dolene ta shirya karbarsa a duk sanda yazo. Murmushin da ke neman kufce masan ya hadiye da kyar da saka hannu yana goge mata fuskar data kwabe da hawaye. Cikin dadisashiyar muryarsa data kara komawa can kasan makoshi a fusge ya furta, “Am sorry bazan kara ba”.

“Why zaka kara, ranar ba sai da kace bazaka sake ba amma yau ka kara, ni bazan sake zama a sashen na a kasheni kwana na bai kare ba”. Ta kara barke ma sa da kukan tabara.

Yanzu kam kasa rike dariyar yayi, dole ya Murmusa har jerarrun fararen hakwaransa masu è da siririyar wushirya na bayyana Bashi da zabin da ya wuce sake rungumeta a jkinsa tsam-tsam yay murmushinsa iya san ransa. (Shi kam wannan Fitinanniyar yarinya ALLAH ya bashi, kuma yana so da kaunar abinsa fiye da zaton mai hasashe). A zuciyarsa yake maganar yana bata sumbata masu kyau a wuya. Kafin ya mike ya dagata cak zuwa bathroom. Idanunta ta rumtse sosai da kankamesa ita a dole karya gammata jiki kar kuma ta gansa itama.

Gashi yay mata mai kyau bayan ya duba yau baiyi barna ba dan ciwukan wancan ranar ma sun warke sai abinda ba’a rasa ba, taimaka mata yay tai wanka, hawaye kuwa da ya ga ba dainawa zatai ba bai sake ce mata komai ba kansu. Da zasu fito cewa tai ita why bazata iya ba sai dai ya dauke ta. Baice komai ba, illa murmushi da yay a zuciyarsa ya dauke ta cak suka fito tana faman tura masa karamin bakinta.Ga idanu sunyi luhu-luhu na kukan da tasha.

“Idan baki bar turamin bakin nan ba zan maimaita ni babu ruwana”. Ya fada yana tsane mata laimar ruwan kanta da towel. Narai-narai tai da fuska zata sake masa kuka ya daura yatsansa saman bakinta ya ce, “Shilli!! Harda kuka ma”. Babu shiri ta hadiye abunta da maida bakin da sauri.Murmushi ya saki ya cigaba,Da tsane mata mata gashin…. kiran da ya shigo ta sashi dakatawa su duka suka dubi wayar, kamar bazai daga ba dan har tana gab da tsinkewa sai kuma ya kai hannu ya dauka batare daya matsa da ga gabanta ba ko dauke towel din da ga kanta.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button