Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 79

Sponsored links

Da sauri fatima zainab tayi kanshi tana kokarin shako wuyarsa kozata samu ta kasheshi ta wuta, kamar ana zugata so take kawai taga baya numfashi…..

 

Fuzgota yayi da karfi yana damke hannayenta da suke kokarin shakesa, hugging dinta yayi sosai yana mannata da bangon kofar…..

 

 

Fizge fizge tashigayi tana neman kwace kanta yasa mata karfi sosai ya matseta sannan yayi bismillah ya fara karanto suratul mulk kamar haka;

 

“Tabaarakal lazee biyadihil mulku wa huwa ‘alaa kulli shai-in qadeer

 

Allazee khalaqal mawta walhayaata liyabluwakum ayyukum ahsanu ‘amalaa; wa huwal ‘azeezul ghafoor

 

 

Allazee khalaqa sab’a samaawaatin tibaaqam maa taraa fee khalqir rahmaani min tafaawut farji’il basara hal taraa min futoor

 

Summar ji’il basara karrataini yanqalib ilaikal basaru khaasi’anw wa huwa haseer

 

Wa laqad zaiyannas samaaa’ad dunyaa bimasaa beeha wa ja’alnaahaa rujoomal lish shayaateeni wa a’tadnaa lahum ‘azaabas sa’eer

Wa lillazeena kafaroo bi rabbihim ‘azaabu jahannama wa bi’sal maseer

Izaaa ulqoo feehaa sami’oo lahaa shaheeqanw wa hiya tafoor

Takaadu tamayyazu minal ghaizz kullamaaa ulqiya feehaa fawjun sa alahum khazanatuhaaa alam ya’tikum nazeer

Qaaloo balaa qad jaaa’anaa nazeerun fakazzabnaa wa qulnaa maa nazzalal laahu min shai in in antum illaa fee dalaalin kabeer

Wa qaaloo law kunnaa nasma’u awna’qilu maa kunnaa feee as haabis sa’eer”………

Ihu tashigayi cikin wata iriyar murya mara dadin sauraro tace;

“Wayyoooooo, dan Allah kayi hakuri”….

Gyaran murya yayi yace;

“Da wani shaidanin nake magana tukunna”….

Cikin wata kalan murya tace;

“Ni ba shaidani bane, ni musulmi ne, ka fita sabgarmu”….

“Bazan fita ba! Waye kai!”…

“Yusuf ne”…….

“Menene matsalarka da ita da kake takurawa rayuwarta haka?!”…..

“Matata ce!”….

Hannu ya daga ze wanka masa mari dan ya shiga saitinsa, sai kawai ya naushi bango tuno da cewa ita zataji a jikinta ba dan iskan ba….

“Matarka a gidan ubanwa? Wani mahaukacin ne ya daura muku auren?”….

“Babana ne ya daura mana, aurenmu yau shekara uku, yayanmu biyu”….,

“Oh yanzu nagane, kaine wahalallen da nacewa ka fita sabgarta dazu ko, amma baka daddara ba kazo ka biyomu harda hada munafurci ko, toh zakaci ubanka yau”….

Cikin shesshekan kuka tace;

“Ka bani matata kawai mutafi, ni babu ruwana dakai”….

“Wallahi ka sake kiranta matarka saina kona duka danginku banza mugu kawai, in banda mugunta ta ina aljani zeyi tarayya da mutum?”…

Deen ya fada a zuciye yana kara mata rikon tsauri tsabar yanda ranshi ya baci, kai dole ma taji a jikinta daga baya…..

“Eh mu munayi, dan Allah kayi hakuri ka kyaleni”…,

“Kai har kasan wani Allah dan uwarka, idan kanaso na kyaleka toh akwai sharuda”…

“Yayi kyau,idan ka isa ka dawo nida kaine, yanzu ka fita ta inda kasan bazaka chutar da ita ba”…

“Toh na fita”….

Tana fadin hakan tayi wani atishawa me karfi sai kuma ta sume a jikinsa, rungumeta yayi yana shafa bayanta cikin tsananin tausayinta, zai iya cewa betaba ganin wacce yaji yana mugun tausayinta kamar itaba, he’s just imagining what she has been going through, how he wish zatayi hira dashi kamar yanda yaji tanayi dasu Umm dayaji dadi, he had always suspect there’s something behind her ashe he was not mistaken, yanzu kuma he’s feeling like bayan wannan aljani daya ke claiming ya aureta there’s another thing, da zata fadamasa ‘WACECE ITA’ da komai yazo masa da sauki….

Zaune suke su biyar a wani dakin taro gabansu dauke da lemuka da ruwa saidai babu wanda ya taba saboda tashin hankalin da suke ciki, ko wannensu kana kallon fuskarsa zagasan ba karamin tashin hankali yake ciki ba kadama daddy yaji labari da wani gumi yake keto masa kamar wanda yayi tsere…..

“Garin yaya kayi sake haka? Gashi yanzu komai na neman kwabe mana”…,

Cewar alhaji usman yana kallon daddy….

Gigiza kai daddy yayi yana sharce gumin dake kansa yace…..

“Banyi sake ba wallahi, bansan ya akayi abubuwa ke neman chabewa ba”…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button