Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 57

Sponsored links

Suna level two wata rana sun fito daga cafeteria zasu shiga mota su wuce gida Abubakar(dad) ya hangonsu lokacin yazo gurin wani abokinsa lecturer, tinda idonsa ya sauka akan mami yaji notikan kansa sun kwance yaji kamar an zuba masa zazzafar soyayyarta lokaci guda, yana kallonsu har mami taja motar suka bar gurin, ba bata lokaci ya fasa abinda ya kawo shi ya bi bayansu, saida ya bari suka shiga gidan sannan yasa ayi masa sallama da me gidan dan dagaske yazo ba da wasa ba shiyasa kawai ya zabi yabi ta sama, har parlourn baffa aka kaisa bayan an masa izinin shiga, gaisawa sukayi cikin mutunci kamar sun san juna, ba boye boye dad ya masa bayanin abinda ya kawosa da kuma inda ya ganta, nan da nan baffa ya gane mami yake nufi dan Umm tana senior secondary school a lokacin, sosai baffa ya yaba da hankalinsa da tinaninsa na yadda ya fara tinkarar iyayenta kafin ita, saidai ya sanar masa shi baze aurar da yayansa ba sai sun gama degree kasancewarsa rikekken dan boko daya rike muka mai kala kala yake kuma matsayin ambassador na nigeria gabadaya, in yaga ze iya jiranta ze bashi dama su sasanta kansu, ba bata lokaci dad yace ya amince, ya kuma nemi a bashi izini iyayansa suzo suyi gaisawa idan sun sasanta da ita dan a tabbatar dagaske yake sannan asan da zamansa karta gama a mishi take over, ce masa baffa yayi wannan ba matsala bane in har sun sasanta kuma tana so, godiya ya shigayi sosai kamar ance masa an basa ne, fita baffa yayi yasa aka turo masa mami………

 

Dad besha wahala gurin samun soyayyar mami ba kasancewarsa mutum gwanin iya tsara kalamai, ga kyau gashi kuma dan babban gida kamar yanda itama take dan lokacin mahaifinsa ne gwamnan kano shiyasa shima ya taso cike da san harkar siyasa, soyayya me karfi ce tashiga tsakaninsu cikin lokaci kankani har takai suna jin kamar a daura musu aure basai anjira ta gama ba saidai dole suyi hakuri ta gama………

 

A lokacin da mom tayi finding out suna soyayya ba karamin bakin ciki bane ya kamata saboda dad ya kai a kira shi saurayi na kece raini gashi kyakkyawa dan gwamna kuma, sai ta fara zuga mami akan dad batareda mami ta sani ba, haka zasuyita samun sabani su rasa me yake janyo hakan, da badan jajircewa da nacin dad ba da tini basu kai haka ba dan mami tasha cewa su rabu idan mom ta zugata cikin siyasa dama mom gwanar iya tsara magana ce tin suna yara saidai dad yaki yarda yace soyayyarsu mutu ka raba ne babu rabuwa…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button