Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 82

Sponsored links

Mami ta fada dan a iya saninta dashi komin dacin abu fadarsa yake ba ruwansa shiyasa ta tambayesa ko yana san yarinyar dan tasan in yana so kai tsaye ze fada…..

“I’m not lying, munyi dashi yau zebar kasarnan and probably ya tafi by now”…

“Oh kai ka bashi shawara ya gudu kenan? Yayi kyau, go get the mask”….

Bece komai ba ya shiga yasa face mask din ko kallon fatima zainab beyiba dan bayasan ya karawa kansa damuwa…..

Fitowa yayi suka bisa da kallo da jinjina wayo irin nashi na kawo idea din mask, ta ina zaka kallesa kace Deen ne when the mask looks so perfect kamar face din real mutum? har colour din skin dinsa yayi rhyming da mask din…

Dauke ido yayi be damu da kallon da suke masa ba ya sake komawa motar ya daukota ya sata a back seat din motarsu sannan ya sake dawowa cikin motar ya bude dashboard ya dauki wani abu a kulle a leda ya zira a aljihunsa sannan ya kashe motar ya zare key din ya boye a aljihunsa yana addu’ar Allah yasa kar mami tace ya kawo…

“Wayace ka daukota ka sata a motarmu?”….

Cewar mami bayan ya dawo inda suke….

“Naga kince tafiya zakuyi da ita”…

“Sai kuma akace ka dauketa? Naga you have legalized taba yarinyarnan kamar wata muharramarka, wani kalan sakalci ne wannan?”….

“Wallahi mami bada wani abu nakeyi ba, naga ku bazaku iya daukanta bane”

Saida suka gaisa da securities din gurin da har lokacin basu gane komai ba sannan suka shiga ciki…

Tinda suka tafi ya kasa zaune ya kasa tsaye, ganin yake kamar zaa zo a kashesa anytime kamar yanda Umm tace what if a aiko a kashe Deen a kashesi a madadin Deen?… Ko dan kara yaji saiya rikice ya fara kalmar shahada, gashi sunce yanzu zasu dawo amma shiru basu dawo ba, hakadai ya cigaba da zagaye dakin…..

Yana cikin wannan hali yaji sallamar mutane, saida gabansa ya fadi dan bashi da tabbacin ko sune suka dawo….

Wani ajiyar zuciya ya sauke da suka shigo, ya tsuguna har kasa ya shiga gaishe su……

Deen be bi takansu ba ya dauki kaya daga cikin kayansa dake gurin ya shiga toilet ya chanja ya fito, cire mask din yayi ya mikawa guy din….

Bayan sun gaisa suka cemasa shima ya shiga yayi changing ya fito su tafi…. Kamar jira yake ya tashi da sauri ya shiga ya shirya….

“Yanzu ya zamuyi dashi?”…

Cewar Umm bayan sun iso parking space….

“Inaso muje gidansu badan haka ba danasa driver yazo ya mayar dashi gida, zaki zauna da yarinyar ko ni in zauna da ita sai ya shiga front sit?”….

“That’s not an issue bari na zauna da ita,let’s go”….

Front sit mami ta bude masa tace ya shiga, cikin dari dari ya shiga sannan ta shiga driver seat…..

Umm kuma ta shiga back seat inda fatima zainab take, zama tayi ta daura kanta a cinyarta ta shiga shafa fuskarta, haka kawai takejin son yarinyar a ranta, ita kadai tasan yanda taji da Saif yace bayason yarinyar, taga rashin hankalinsa na rejecting kyakkyawar yarinya haka though abun baa nan yake ba, watsar da zancen Deen tayi ta hau yimata addu’ar Allah ya bata miji nagari da ze sota ya kula da ita sosai…..…..

Tada motar mami tayi tana tambayarsa sunansa…

“Aliyu”….

Ya fada yana sunkuyar da kai

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button