Hausa Novels and Stories

Maraici Ne Ja Min Complete Hausa Novel

Sponsored links

Rahama! Rahama!! Ya dinga kwala mata kira da kakkaurar muryarshi.

Wata matashiyar mace ce ta futo a kitchen da sauri sauri tana amsa kiran shi, “na’am Abban Hanan gani nan zuwa”. Ta fad’a tana ajiye tukunyar hannunta gaban shi.

Da sauri ya matsar da k’afarshi don saura k’iris ta d’ora mishi tukunyar a kai, yayi squeezing fuskarshi yace, “Wai meye haka rahama kina kallo zaki zuba mun abinci mai zafin nan kan k’afa, sannan in don nine ma kike duk wannan saurin ba tsayawa yin break zanyi ba don already nayi late, abincin kine dama in nace sai naci kullum zan futa to watarana sai futar ma ta gagare ni”.

Shiru tayi tana kallon shi, sai taji kuma ya bata tausayi, yau kusan 5days yana futa office ba tare daya karya ba, duk yadda take son ganin ta mishi bajinta kafun aje da nisa take sarewa. Saita k’ak’alo murmushi a fuskarta tana kallon shi ta sake cewa, “please Abban Hanan ko ba da yawa ba ka tsaya kaci”.

“Kinga bani sak’on nan zan huce nagode da k’ok’ari”.

“Don Allah ko tea ka tsaya kasha please”. Ta sake fad’a tana rik’e da tukunya a hannu har lokacin, ganin ta takura sai yace, “okay amma ki had’a da sauri”. Cikin jin dad’i tace, “yauwa ko kaifa! Har naji sanyi a raina wallahi ko ba komai k’ok’arina bazai tashi a banza ba”.

“Saura k’iris dai ya tashin”. Ya fad’a yana zama kan stool da take k’ok’arin gyara curtains dasu areef suka wullo mata kafun hucewarsu school.

Tana had’a mishi tean wata matashiyar budurwa ta futo sanye da wata yaloluwar rigar bacci daba abinda ta b’oye har shatin pants d’inta ana gani🙈 tayi mik’a da kiran “Auntie! Auntie!! Auntienaa”. Kusan su duka a tare suka waiwaya suna kallon direction da yarinyar take, rahama ta girgiza kai tana ci gaba da aikinta tace, “ko sai zuwa yaushe Aysha zata san ta girma ta daina mun wannan kira kamar na yaran goye?”.

Mukhtar da yake k’ok’arin amsa waya, sake maida kallon shi yayi gare ta, sai ya lumshe idonshi ya bud’e yana jin sautin daddad’ar muryarta daya jima baiji ba yana kai mishi har can k’arshen zuciyarshi, kafun a hankali ya maida akalar duban shi gareta duba irin na tsaf da tsana ki, saida tsigar jikin shi ya zuba a lokacin da yaga yaloluwar rigar data futo da ita. Itama sai lokacin ta lura dashi a parlon, ganin mayen kallon da mukhtar ke mata yasa taja tsaki tare da komawa cikin d’akin barcinta da sauri had’e da banko k’ofa. Sautin tsakinta ya d’auki hankalin rahama har ya assasa mata d’ago kanta tana kallon sashen da take zaton yarinyar take, sai taga wayam babu ita a gurin, ta sake girgiza kai kurum ta nufi inda Abban Hanan yake zaune ta mik’a mishi tean. Mik’ewa yayi ya d’auki keys d’inshi ba tare daya kalleta ba yace, “bar shayin nan rahama kawai ki bani takardun nan zan huce”.

Meyasa Abban Hanan? Yanzu fa kace zaka sha kuma bayan na gama had’awa kace ka fasa?”.

“Rahama! Bani takardun nan na tafi”. Ya sake fad’a ba wasa sam.

Itama sai bata sake ce dashi komai ba ta nufi d’akin gadon shi, yabi bayanta da kallo cikin zuciyarshi yana jin wani abu yana tab’a ranshi. Har ta dawo yana gurin ta mik’a mishi ya karb’a, suka k’arasa yin sallama ya tafi ita kuma ta fara k’ok’arin k’arasa had’a gidanta kafun azo karb’an abincin yaran can don yau basu tafi da lunch ba na break ma da biscuits ta had’a su cox kwata kwata bata jin dad’in jikinta cikin ranakun.

Around 11:30 ta sake futowa cikin shigar doguwar riga maroon data zauna jikinta sosai, kanta ba d’ankwali sai wani irin k’ananan kitso da akayi shi da attachment ya sauko har kafad’arta, ta futo tana k’ok’arin d’aure shi a k’eyarta. Yarinyar d’azu ce, naturally ba fara bace amma ta hanyar amfani da tsadaddun mayukan k’ara hasken fata yanzun ta koma fara sol kamar yayarta rahama, za’a iya kiranta kyakkyawa duba da bata da wata makusa a fuska, tana da k’aramin jiki, ga wanda ya mata kallon tsoro ma zai iya ce mata siririya. That’s Aysha y’ar gayu kuma ma’abociyar aji da son kwalliya kamar d’aweesu.

A lokacin rahama

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button