Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 2

Sponsored links

Tafiya yake majestically amma bada sauri ba,wani irin perfect silence da taji ne yasa tagane maybe lecturer din ne yazo,a hankali ta dago idonta ta cikin niqab din ta kalleshi,saida taji kirjinta ya buga,tayi saurin dauke kanta………. Kasa kasa taji ta bayanta nagawa ta gefanta “shi nagani,wlh shi nake gayamiki”….. Dayar ta zaro ido tace “Da gaske?”… Ta bayanta ta sake cewa “Wlh shine,harfa summoning courage nayi na tambeyeshi digit dinshi……….

 

“Mtseeeeww” Jinta kawai tayi taja wani uban tsaki,abinda ko magana bata tabayi a class din ba,sai wannan dan takaici da bata masan tayi ba,ba abinda ta tsana a rayuwarta irin taga mace na stooping low akan namiji dan ita bata dauki maza a bakin komai ba……. Karab tsaki a kunnensa da duka yan class dinma sbd yanda ajin ya dau shiru,kowa ma mamaki ya dinga yi sbd tsakin ya fito sosai,gashi da niqab a fuskarta bare ace ko wani abu aka mata,barema su basu taba ganin tana magana da wani ba……..

 

Dauke kanshi yayi daga kallon niqab din nata yace “Get up” a nitse….. Ba tare da ko dar ba ta mike dan ita kai tsaye take abu….. A nitse ya kuma cewa “Unveil!”…… Saita dago da sauri tana kallonshi ta cikin niqab din….. Kokarin controlling kanshi ya farayi dan yanzu zeyi losing kanshi,a nitse ya kuma cewa “Unveil and explain to us what cause that loud hiss?” …… Jin haka ko kowa sai ya bada attention dinshi a kanta, dama sundade a cikin curiosity dinnan,har planning suke aje a mata mgn,ana zuwa kuma sai a kasa,sun kasa gane wani irin kwarjini ne haka da ita…….Ai jitayi kamar kafafuwanta bazasu dauketa ba tsabar yanda ta kidime,ita tasan duk abunda yace Bame yiwuwa bane,amma kuma ya zatayi handling situation din,kawai sai wata dabara ta fado mata,duk da madai ba zai mata solving completely ba,ya dai fiye mata tayi unveiling a cikin mutane ta fara bayani….. “Impossible!” Ta fada a ranta……

 

A hankali ta fara takawa zuwa stage din,dagowa yayi yana kallon ikon Allah dan as long and he’s concerned shi bece tazo gaban podium din ba,cewa yayi ta tsaya tayi bayani anan…. Saida ta karaso dab da shi sannan tadan janye niqab din yanda zaana ganin idonta kawai,ta shiga kallonshi da bold eyes dinta da suke a lumshe,tsabar saka niqab bata ko iya budesu sosai………. “Ya Salam” ya fada yana tare handout din da saura kadan su zube daga hannunshi,For once ya manta cewa he’s a psychopath! Ai be san sanda ya daka mata wani mugun tsawa ba yace “GET OUT!!”……

Fita tayi da sauri saboda tasan inta cigaba da tsayuwa komai zai iya faruwa…..

 

Wayam yagani kamar wacce ta bace,sai kawai yabi iska da kallo yana mamakinta a ransa,yana kuma fadin duk addu’ar dayazo ranshi,gashi ko zaa kashe shi bazaice ga wani mugun abu dayagani a tattare da ita ba,saima perfect roundish-almond eyes daya gani,ajiyar zuciya ya sauke,beneath his breath yace “she’s indifferent!” sannan ya cigaba da lectures…..

Da karfi ta bude back seat tashige,tanajin wani zazzabi na kamata meanwhile ranta na kara baci,itafa tsap saita hakura da school din gabadaya,dama ganin damanta ne harta maida hankali tana zuwa class,tunda tasan kano duniyannan ba ubanda ya isa yamata dole a komai,tsaki ta kara ja aranta tana bawa kanta hakuri,at the same time tana fadawa kanta this is a minor thing,ta kyaleshi kawai,saboda tasan in tasa a ranta toh wlh sai yaji a jikinshi…..

 

Zira hannunta tayi tana kokarin zare car key din ganin beja motar ba,ai da sauri ya zare kafin hannunta ya karasa,a kidime yake cewa “I’m so sorry ma’am,I’m really sorry,let me drive you”…. Hannu ta kuma mika mishi alamun ya bata car key din…… Shiko ko marinshi zatayi ya gwammaci yayita bata hakuri harta hakura ta barshi yaja motar,dan yasan idan takarbi car key dinnan tashi ta kare…….. Marairaicewa ya sakeyi ya hade hannunshi biyu alamun roko ya sake cewa“Please ma’am help my life,I’m extremely sorry,let me drive you”………. Janye hannunta tayi badan ta tausayamai ba kotaji wani abu a ranta saidan kawai batasan jayayya,kar kuma abinda ba ruwanshi ya shafeshi…….. Wani ajiyar zuciya ya sauke a fili yana godewa Allah a ranshi,dan haryayi give up wlh,kawai dai yayi trying luck dinshi ne yayi insisting,sarai ya santa no nonsense woman ce!… Yaja motar a guje suka bar wajan………….

Parking yayi a gaban Transcorp Hilton,ya fito da sauri ya bude mata yana mika mata jakarta daya zuba drugs din da suka tsaya suka siya dan jakarma a motar take barinta,karba tayi batace komai ba tashiga hotel din… A fifth floor lift din ya tsaya kamar yanda ta saita,tsayawa tayi bakin guest room 302,ta dauki key a jakarta ta bude tashiga da sallama chan ciki……… Kulle kofar tayi ta hau kan bed tana zuge jakar hannunta,ta dauki drugs din ciki,har zata rufe jakar sai kuma ta hango wayarta,wayarda sai tayi wata bata tabata ba,gashi ba wanda ya isa yace mata dan me?,kuma sarai indirect ana fadamata badai zaa fada straightforward bane,tabe baki tayi sannan ta zaro wayar,tana jujjuyata,tana kuma kiyasta wani abu a ranta,taji wasu na hira suna cewa anyi har 14 pro max,amma shine aka barta har saida taji a gari ita bata mallaketa ba!……. Sai tayi tsaki ta kunna 13 pro max din dake hannunta……. Tashi tayi ta nufi mini fridge din dake dakin while wayar na kunnuwa,ordinary bottle water ta dauka dan batasan abu me sanyi kwata kwata shiyasa ko connecting fridge din bata tabayi ba….. Glass cup ta hado dashi tana zuba ruwan a ciki ta balli drugs din ta cire niqab din ta watsa a baki tana lumshe ido,she’s so addicted da intayi kwana daya bata sha ba gabadaya saita fita hayyacinta,ta sani sarai tana abusing drugs,to amma ya zatayi da abunda ta tashi taganta tanayi for years?………

Ringing din wayarta ce yasa ta dan bude ido,shiyasa fa bata san kunnawa saboda batasan damuwa,Shikuma dama yayi connect da wayarsa duk sanda ta kunna waya sai anyi alerting dinsa kawai sai dai taga kiransa…….

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button