Hausa Novels and Stories

Idon Naira 21

Sponsored links

Tanajin dacin yanda suke rayuwar saidai shedan a kafirar zuciya irin tata yasa komai nasu yaqi gaba bare baya kullum suna tsaye guri daya

Dukkaninsu rayuwarsu Tana guri guda a tsaye

Koda Zainab ta fita Jin tayi zuciyarta na Kara daukan ‘daci da nauyi Dan haka umma takira ta sanar Mata komai tareda bada tabbacin matuqar Aqeel bai tafi karatun datakeso dinba Zainab zata bar Mata gidanta.

Hankalin umma ya tashi sosai da hukuncin Haj maryamah din sbd ko yayane batason su rabu gwara dai suna taren wata ran kila su hade kansu duk da dai kusan kaman an qurewa Hakan Tunda manyancin ya fara shigowa musamman maryamah da manyancin Kam yariga yazo ita kanta Zainab ta girma ai tafiya sawun Yan Mata ma.

Umma tsufa yazo batajin zata iya doguwar tafiyar da zata zo gurinsu.

Kwana biyu akai gidan bbu Mai dadin Rai sbd Haj maryamah ta dauki zafi sosai Kuma ko Aqeel din Bata bawa damar zuwa gurintaba bare ya lallabata yabata hakuri…

Zainab ma sosai ta bawa zuciyarta hakuri ta fara janyewa daga Aqeel din sbd kaucewa fitina da bacin rayuka kamar Hakan Dan umma ta kirata a waya tayi Mata fada sosai Dan haka duk sai taji a Karo na farko rayuwar tafara fice Mata arai.

Lamarin dai sai qara munana yakeyi sbd Kai tsaye Aqeel yasake tabbatarda bazai tafiba yabar Mamin tasa Dan haka Kai tsaye Haj maryamah itama ta sanar masa ko yatafi ko Mamin tabar gidan…

Aqeel ma kwata kwata bai dauka lamarin zaije can ba hankalinsa ya tashi matuqa da yanayin da Mamin ta shiga Dan haka shida Kansa ya Kira umma yasake fada Mata komai Dan ita kadaice zata tankwasa Mahaifiyarsa,

Hakama ya Kira hajiya Kaka mahaifiyar Dadynsa itama tazo tabawa haj maryamah hakuri Amma dai itama Tana Bayan Aqeel din yatafi karatu Bata yarda da karatunsa anan ba.

Rigima dai Bata qareba saida umma ta taso daga Cameroon tazo aka zauna akai magana tareda tone tone inda anan Aqeel yaji asalin matsayin Maminsa ba ‘yar aikin gidan bace qanwar mahaifiyarsa ce Uba daya.

Wani irin fitinannen tsoro da mamaki ya shiga na wannan mummanan alaqar da iyayen nasa Mata biyu suka gudanar tun qananun shekaru har manyanci….

Tsananin tausayi da sabuwar kaunar Maminsa ne ya shigesa Wanda a gabansu saida ya zubda qwallar wani irin ‘daci da raunin da zuciyarsa ta samu na Jin wannan babban lamarin.

Kai tsaye ya amince da barin qasar zuwa UK Dan kuwa bazai taba barin sbd shi Mamin tabar gidanba Dan kuwa yasan batada gurin zuwa…. Amma a gabansu ya shimfida wani kyakkyawan alqawari Mai girma na cewa duk ya dawo zai dauki Maminsa har abada nauyinta zai dawo kansa yadauke musu nauyinta tun daga na jini harna jiki.

Da farko Haj maryamah Bata fahimtaba saida umma tasake nuna Mata illar Hakan da gaba zaa samu Dan haka tace Bata yardaba

Zainab qanwarta ce a hannunta zata zauna sai aure idan tanada rabon yinsa kenan.

Kalmar ta Sosa zuciyar Aqeel yakalli Mamin wadda take zaune batada abin cewa sai yanda akai da ita.

Take wani ciwo da daci yakuma mamaye zuciyarsa Dan haka baice komaiba aka bar zancen ahakan.

Umma sai datai kusan wata daya kafin ta tattara ta koma Cameroon tabarsu Bayan tayi musu Yan nasihu Amma dai kusan kowa yanzu zuciyarsa ta cire Rai daga Dan uwansa.

Zainab gabaki daya yanzu tasake zama wata iri tayi sanyi sosai fiyeda baya Dan an ankarar da ita ko zaman datakeyi gidan alfarma ce akeyi Mata

Batada wani amfanin da zaa mutunta Dan shi saima tunatar da ita da akai ita din ba kowa bace face Yar Aiki a gidan wadda zaa kora aduk lokacin da akaso.

Shi Kansa Aqeel yanzu tsakaninta dashi sai idan yazo dakinta da safe gaidata kamar yanda ya saba Amma duk wani alaqarta dashi ta Dan ja baya dashi.

Wannan sabon halin data shiga ya sakasa damuwa shima Amma Kuma shima cikin nasa yanayin na damuwar yake Dan haka kowa dai yazama sai ahankali gidan.

Malam Sanda A yanda yakejin Aqeel shima tamkar shine ya haifesa musamman Dama baida da ko daya ba taba haihuwaba,

Asalinsa Dan Billiri dake gombe karatun almajiranci ne ya kawosa cikin gombe daga Nan aka ringa kaisu garuruwa almajirancin qarshe ya tsaya anan Jigawa harya girma yafara Dan sirkawa Dana Biko kadan kadan haryayi karatun secondary Amma daga Nan bai Dora ba saiya Dan ringa kasuwanci Yana karatun addinin sosai har Allah yasa ya Dan Yi suna a karatun Addininsa.

Tunda iyayensa suka rasu ya rage zuwa gida haryazo Yana jimawa sosai baijeba Dan kusan dangin kowa tayita kansa.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button