Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 50

Sponsored links

Sai kawai khaleel ya fadamasa sun amince, sosai Abby ya nuna musu jindadinsa yayita shi musu albarka sannan yace ze aiko a daukesu gobe da safe kawai su zama cikin shiri…….

Deen yaso yaga manager asibitin a ranar amma abun ya gagara saboda baya kasar, haka ya kwana yana zagaye asibitin amma be gansu ba, sai gabannin asuba sannan ya fita ya samu wani hotel dake kusa yayi lodging, wanka yayi yayi alwala ya shirya sannan ya tafi sallar asuba, a masallaci suka hadu da Abby da ba karamin jindadin ganin Deen yayi ba, dan tattaunawa sukayi akan yanda tafiyar ze kasance sannan suka sake rabuwa……

8:00am dot Abby ya aiko da mota aka dauki su khaleel, ba bata lokaci suka fito suka shiga dama a shirye suke, sunyi balakin kyau cikin matching outfit kamar yanda sukeyi kwanannan, fitted abaya tasa daya fitar da kirar jikinta sai mayafin abayar data yane kanta dashi…..

Har cikin landing area aka kaisu, aka kuma saukesu daidai inda jet din yake, sai a lokacin suka gane private jet ne, mamaki ne ya kama khaleel dan be taba tinanin mutumin yanada arziki haka ba ganin yanda yake da balakin saukin kai…….

Demarcation biyu ne a cikin plane din sai aka kaisu na ciki bayan sun gaisa da Abby dake cikin na farko…..

Suna shigewa Deen ya karaso, nuna masa kusa dashi abby yayi sannan ya zauna, addu’a akayi plane din yayi taking off……..

Sun danyi tafiya me nisa Deen ya mike tsaye, kallonsa Abby yayi yace;

“Where to?”….

“I want to use the rest room”…..

Ya bashi amsa…….

Suna zaune suna shan soyayyarsu kamar yanda suka saba a yan kwanakinnan, kullum ji suke kamar su chinye juna, sai kawai fatima zainab taji gabanta yayi wani mugun faduwa, ruko hannun khaleel tayi tace;

Sai a lokacin fatima zainab ta zame jikinta daga na khaleel jin abinda takeji ya ragu saidai har lokacin tanajin kirjinta na bugawa kadan kadan…….

“Relax love, Nothing’s gonna happen, relax okay?”……

Khaleel ya rada mata a kunne cikin tausasawa……

Gyada mishi kai kawai tayi sannan ta lumshe ido kamar me jin bacci, khaleel be kara cewa komai ba duk a tinaninsa bacci take nan ko wani tashin hankalin takeji a ranta…….

Tinda Deen ya dawo ya zauna ya nemi nitsuwarsa ya rasa, ko dazu daya shiga toilet yaje ya danyi clearing mind dinsa ne saboda false abu da take gayamasa, ya ma zaayi ace yanajin irin abinda yake ji idan tana kusa dashi bayan yasan daga shi sai Abby a cikin jirgin, abun mamaki koda ya dawo be samu nitsuwar da yake so ba sai ma bunkasa da abinda yakeji yayi, daurewa yayi ya cigaba da kame kansa dan in zebi ta zuciyarsa tashi zeyi ya duba lungu da sako na jirgin saidai hakan babu tsari sam tinda Abby na nan, abin ne yaci karfinsa ya fara juye juye be sani ba, rikicewa yayi ya fara kalle kalle daga zaunen da yake kamar wanda yake neman wani abu

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button