Hausa Novels and Stories

Idon Naira 19

Sponsored links

Kiran Zainab Haj maryamah din tayi tai fada sosai tareda cewa lallai saita rarrashesa tasa ya amince ya tafi makarantar Dan tariga ta kashe maqudan kudi sosai akan karatun nasa.

Da farko Zainab rarrashinsa tayi tareda nasihu da Jan hankali iri iri Amma Sam yaqi yarda

Duk da bai fadaba itama tasan sbd itane

Qarshe dabai yardaba hakura tayi ta qyalesa Dan Bata son takura Masa Tunda baya gardama da duk abinda ta sakasa sai wannan karon

Dan haka bazata takurasaba Dan Jin take kamar tace a qyalesa karsu takura Masa Amma Kuma ba Dama Tunda uwar data haifesa ce take magana akansa.

Issue din makarantar yasa ran haj Maryamah baci sosai qarshe ta dorawa Zainab din lefin Bata basa tarbiya Mai kyauba tunda har zai iya qin abinda tace ita data haifesa.

Fada da bacin rai sosai akai akan maganar makarantar tasa Wanda dukanin laifin akan Zainab aka dorasa karshe kukan datake dadewa bataiba sbd bushewar da idanuwanta da zuciyarta sukayi Amma wannan karon saida ta kwana Tana kukan bacin ran da lamarin ya kawo Dan kuwa ko umma ta Kira wayarta Babu kalar fada da gorin da baayi Mata ba Hakan ta Basu hakuri Dan batada komai na fada.

Aqeel kuwa abinda sukaiwa Mamin yasa yace bazai taba zuwa makarantar ba Dan farko harya fara sauka akan zaije din ganin Maminsa nata lallabasa.

Tunda akai wannan tashin hankalin sai haj Maryamah tafara Jin buqatar raba danta da Zainab tun kafin lokaci ya qure Mata Dan kuwa da Alama ‘danta tanaji Tana gani zai bijire Mata

Wato dai kamar Zainab ta haifawa Dan kenan.

Ita kanta Zainab sake kame kanta tayi tareda shiga taka tsan tsan sbd ganin ran su umman da Haj maryamah ya baci sosai.

Aqeel baije boarding school dinba Amma Hakan daya faru yasa Haj maryamah yanke shawarar daukesa daga qasar kwata kwata zuwa wata qasar yayi karatunsa acan sbd da gaske take buqatar rabasa da Zainab yanzu sbd zuwa yanzuma tsoron irin kaunar dayakewa Zainab din takeyi Dan kuwa yafara maganar abawa Zainab qananun abubuwa zuwa gaba yayi girmanda zai karba dukiyarsa ta tabbatarda zai iya mallakawa Zainab komai nasa data Gama yawo da wahalar kular Masa da kare Masa.

Ta bangare daya malam Sanda ne ya zama malami na musamman ga Aqeel tareda cusa Masa akidu na so da kaunar karatun addnini sosai sbd harda shi acikin burikan mahaifinsa akansa,

Mahaifinsa yanada tsananin shaawa da buqatan ‘dan nasa yasan Addininsa sosai yayi zurfi acikinsa Dan haka ahankali sai shima Aqeel din Hakan ya shigesa yafara zama Mai tsananin son addini da karatunsa sosai.

Kokarinsa da nutsuwarsa akan Hakan yasa malam Sanda maida hankali gabaki daya akan Aqeel din Dan cika burin Alh Asad dakuma Dan samun qarin Wanda addnini zai qaru dashi.

Ahankali shaquwarsa da malam Sanda tayi zurfi sosai har yake Masa kallon mahaifi sbd shima ya manyanta yazama dattijo mai nutsuwa sbd ilimin addini daya ratsasa,

Sam baya tsallake maganar malam Sanda sbd ba qaramin girmansa yake ganiba musammam daya kasance ta wani bangaren kamar shi kadaine Bayan Maminsa Wanda yake fahimtarsa.

Yazama matashi Mai cikakkiyar nutsuwa da kamun Kai Kuma har lokacin Babu Abu daya rage na shaquwa da girman kaunarsa da Maminsa saima abinda yayi gaba,

MUHAMMAD AQEEL ASADULLAH yazama wani irin saurayi da kallo daya zakai Masa kasan ‘dan gatane daya taso cikin gata da nitsatsiyar rayuwa,

Kyakkyawane Wanda ya dauko kamannin mahaifiyarsa sak wacce itama kyakkyawar tun asalinta.

Zainab Kuma zuwa wannan lokacin sosai ta fita a sahun matasa masu ‘yan shekaru Dan kuwa tazama mace sosai gashi har Haj Maryamah data girmeta nesa sosai ta fita kyan gani da jikin kuruciya sbd Hutu da Jin dadi

Itakuma wahala duk ta sauyata tasa manyancin zuwar Mata da wuri.

Har wannan lokaci Babu wani Wanda yataba sanin matsayin Zainab agun Haj maryamah acikin gidan

Shi Kansa Aqeel Asad har lokacin Baisan alaqartaba agurin mahaifiyarsa wadda yanzu Yana girmamata sosai sbd girma da hankali dayayi tareda sanin matsayin uwa data wuce kowace irin Wasa da reni.

A fadin duniyarsu shi kadai ne matum daya dayasan Maminsa ciki da bai,

Shi kadai ne yasan menene abinda ranta bayaso da Wanda ranta yakeso duk da Sam batada wani raayi ko buqatar kanta sai tasu Amma ahakan yasan kowane yanayinta abinda yake nufi Dan haka yafara tsayuwa sosai akan duk wani lamarinta Dan kuwa ankai bagirenda shine da Kansa yasa aka kawo masu Aiki a gidan har uku yakuma daukewa Mamin tasa Aiki ko daya na gidan.

Zainab taji dadin Hakan Amma duk da Hakan tasaba da ayyukan wasu aikin Dole itace takeyi dakanta

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button