Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 27

Sponsored links

Da sauri khaleel ya mike yaci kwalar rigar Deen yana hucin wahalar bugun da yasha yace;

“Kayi kadan ka rabani da wifey! Kayi kadan! Waye kai? Yaushe kasanta? Get the f**k off out of our life!!”……

Wani zazzafan mari Deen ya daukeshi dashi ya fizge hannun khaleel daga rigar shi yace;

“A gidan ubanwa ta zama wifey din? Naga kamar baka dakuba tinda kana da bakin gayamin maganar banza!!”….

Deen ze sake kai masa mari kenan kawai khaleel ya zaro bindigar daddy daya fito da ita ya saita akan Deen…….

Ganin abun nasu ya fara wuce na hankali tinda har bindiga aka fara zarowa yasa fatima zainab saurin shiga tsakiyarsu, murya na rawa tace;

 

“No khal karkayi haka, dan Allah karkayi haka, karka kasheki”…….

 

“Akanme zakice karna kasheshi? Ko son shi kike?”…….

 

“Wallahi bana sanshi, na fika tsanarshi ma, karka kasheshi because of his family”…….

 

“It doesn’t matter! To hell with his family!”…..

 

Ganin fa dagaske khaleel so yake ya harbi Deen yasata rungumeshi da sauri dan dagaske bata so ya kasheshi kodan Mami da Umm da suke nuna mata kauna sosai, a take jikin khaleel ya mutu jinta a jikinsa, abinda bata tabayi gashi kuma beji irin abinda yaji lokacin daya tabata ba saima wani sanyi da dadi dayaji ya saukar masa lokaci daya……

“Please ka kyaleshi, muda zamu barmusu kasar? Ka rabu dashi kawai”…….

“Okay wifey”….

Ya fada chan kasa jin yanda ta saukar masa da kasala lokaci daya……

“Give me the gun”…..

 

Fatima zainab da har lokacin hankalinta be kwanta ba tana ganin kamar khaleel ze harbi Deen tace ya bata…….

 

Ba musu kamar wanda ake controlling da remote ya mika mata bindigar…….

 

Kamar a mafarki Deen yaga ta rungume khaleel, sosai ya shiga shock har saida yaji komai na jikinsa ya tsaya, kamar statue haka ya tsaya yana kallonsu yanajin kamar yayi kuka wai a gabansa zasu rungume juna? Abun da ciwo gaskiya, kamar wanda aka mintsina ya dawo hayyacinsa, fuzgota yayi daga jikin khaleel sannan ya zare bindigar dake hannunta.

 

Janta ya shigayi kamar akuya yayi hanyar barin wurin da ita, nan khaleel yace masa be isaba, sai aka fara jaye jaye, wannan yajata wanchan yajata kamar dai rago, last last Deen yayi succeeding ya janyeta, sunkutarta yayi da sauri ya nufi inda yayi parking motarsa da ita, yana zuwa ya bude back seat ya wurgata ko tsoron taji ciwo bayayi tsabar yanda ransa yake a bace…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button