Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 17

Sponsored links

Jin hannayenta kawai yayi a gashin kansa,ai besan sanda ya tureta ba ya haye sama a guje,itama ta bishi a guje dariya na taso mata tana dannewa……..

 

Kumm! Yaji ya bige da bango kasancewar haryanzu idonsa a rufe yake,be gama tance inda yake ba yaji alamunta a gefensa,da sauri ya tsuguna still idonsa a rufe yace “Dan Allah dan annabi kiyi hakuri,ki kyaleni,wlh na hakura”…….

 

Tabe baki tayi tace “Wlh bazan hakura ba,ka gama sani cikin wannan hali kuma kace in hakura?,aiko dai saika biyamin bukatata!”…..

 

Dafe goshinsa yayi wanda yayi kullutu kasancewar bugewar da yayi,cikin muryar tashin hankali yace“toh ai kinga dai nima ina cikin yanayin amma nace na hakura,toh dan Allah kema ki hakura,duk mu hakura gaba daya”…….

 

Koh kulashi batayi ba tayi dariyar mugunta ta sake sunkuyowa kanshi,jin haka yasa ya tashi a haukace ya nufi hanyar bedroom dinshi a guje,kafarsa ta bige da flower vase amma ko zafi be jiba ya shige,rufe kofa yake kokarinyi yaji ta banko,a guje ya shige toilet ya rufe kofar da sauri yana godewa Allah daya bashi ikon tserewa toilet,yanzu da ba toilet a dakin ya zeyi?🤣…

 

Toh ina ze iya da wannan masifa,yana zaman zamanshi ya debo ruwan dafa kansa,a yau ya yadda fatimah zainab tafi karfinshi,Ashe tatsuniya yaketa gayawa kanshi da yake cewa dan shi aka halicceta?……,jin tana buga kofa yaji wani gumi na karyo masa,sai gashi yana kuka wiwi yana bata hakuri daga cikin toilet din,Itako dagewa tayi saiya bude yasan yadda zeyi da ita haka kawai ya bata abu tasha kuma sai ya gudu ya barta a cikin yanayi?.…. Inaaa!

 

Bubbuga kofar ta farayi da karfi,sai ga shi yana sakin fitsari shaaa a wando,gabadaya yaji ya nemi banzan feelings din ya rasa,ashe komai ma samun guri yake?….. Cikin muryar kuka yace“Ki tausayamin ki min rai,kiyi hakuri ki yafemin,nasan ban kyauta ba,amma dan Annabi kiyi hakuri”…

Bata kulashi ba tace “Ko ka bude kofar yanzu,kona ballata!”……. Jin haka kawai ya zube kasa sumamme…

Jin shiru ne yasa fatima zainab kwashewa da dariya,ko a haka aka tsaya tasan kwalliya ta biya kudin sabulu,ita kanta tasan ko a haka ta gigita rayuwarsa,ta razanashi,ta dimautashi,gobe inya isa ya kara….. Tuno yanda khaleel yake kuka yana bata hakuri yasa ta kara tintsirewa da wata muguwar dariya (ni ko unique barakancy nace wai danma bakisan harda fitsari ya saki a wando ba😹)…. Zuciyarta fess ta fita daga dakin,dayan dakin tashiga inda ta sauka,toilet ta shiga tayi wanka sosai,sannan ta dauro alwala ta fito,dogon hijabi kawai ta zira ganin lokacin sallahr isha yayi ta tada sallah a nitse,ta daura da shafi’i da wutiri…… Shiryawa tayi sannan ta dauko regular dinta tasha,saida ta jita very high,sannan wani dauyayyan bacci ya kwasheta…….

Awan khaleel biyu a toilet sannan Allah ya bashi ikon farkawa daga suman daya yi,kalle kalle ya shiga yi tsabar rudewa sai yaga kamar ita yake hangowa ta gurin windown toilet,wani ihu ya rusa yana cewa “Wayyo Allah,azo a taimakamin,dan Allah kiyi hakuri na tuba,bazan sake ba wallahi kimin rai sharrin shedan ne,ki tausayamin ki rabu dani”……. Sai kuma yaga ya daina ganinta kamar wacce ta bace,ai saiya kara fashewa da kuka….. Kamar ance ya kalli gefenshi,sai yaga kamar ita,ihu ya sake zawo na zubo mishi ya kuma sumewa (nan ko duk hallucination ne tsabar yanda yasa abun arai,amma bata gurin,ita tana chan tana shan baccinta)……….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button