Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 107

Sponsored links

Fitsari daya takura Iffah ne ya tilastata tashi har Daneen Ammarah ta farga. Da sauri takai hannu ta riƙota tana mata sannu, dauriya kawai Iffah tai na dannewa dan tunanin datai a ɗan farkawar nan Tata zuciyarta ta bata shawarar ɓoye sirrin ranta domin samun cikar burinta. Dan tayi alkawarin a wannan karon sai ta halaka Shahan-shan, ta riga ta ƙuna bata tsoron mutuwa. In har burinta ya cika danta mutu ba komai bane a gareta a yanzu ma tafi buƙatar mutuwar fiye da rayuwa tunda har ta rasa sauran ahalinta kuma miya rage mata.

“Ya akai na zo nan Mamy?”.

Ta faɗa cikin danne komai dake ɓoye a ranta. Daneen Ammarah da farin cikin farkawar Iffah ya sata sakin murmushi yaƙe da ita kuma Iffah ta fassara da wani abu daban ta amsa mata da faɗin, “Sakamakon abinda muke tunanin ya rikeki aka sameki a sume shine aka kawoki asibiti, amma Alhamdullah tunda gaki kin farka”.

Maimakon ta amsa mata wannan zancen sai ta jefa mata tambaya. “Mamy da gaske ta mutu ko?”.

Take idanun Daneen Ammarah suka cika da hawaye. Cikin ɗaci tace, “Sun kasheta Ibnati, sun sami damar da suke buƙata akansa. Gaba ɗaya ƙasa ta harmutse da bore akansa kamar yanda dama suke son cimma buri”.

Iffah ta ɗan lumshe ido ta buɗe zuciyarta na karajin tsanar Daneen Ammarah ɗin da mamakin salon yaudararsu, amma a zahiri sai itama ta marairaice fuska. “Mamy ban fahimta ba?”.

Hawaye Daneen Ammarah ta share, “Ibnati a yau ruman baki ɗaya a harmutse take, talakawa nata zanga-zanga a wasu jahohin akan sai Abni yayi murabus a kujerar Shahan-shan inba hakaba zasu ɗauki mataki. Gashi tunda abin nan ya faru babu wanda yaga idonsa ya kulle kansa a ɗaki anyi-anyi ya buɗe yaƙi”.

Iffah ta rumtse idanu da karfi tana taune lips ɗinta, yayinda take faɗi a zuciyarta da kakkausar murya. (Ni zan ƙarasa musu aikin da kawo musu ƙarshen matsalarsu. Dan ba murabus kawai ya cancanci yi ba mutuwa gaba ɗaya yabar duniyar ya cancanta da shi ba kujerar Shahan-shan da ƙasar ruman kawai ba).

Daneen Ammarah dake tunanin yanayin ma Iffah tashin hankaline kawai sai ta shiga rarrashinta. Dole Iffah ta cigaba da pretending da matsawa a sallameta taji sauƙi. Daneen Ammarah na rakata sashen ta wuce dan jikin Malikat Haseena ma dai babu daɗi sam. Dama Daneen Ammarah ɗin ta zauna

da Iffah ne domin saka ido kar wani ya cuta mata itama. Hakan yama Iffah daɗi, dan ya bata damar nutsuwa a kallon videon data ɗauka ɗazun. Sosai tai zooming gawar Zawjata-almilk tana kai bin jikinta ta inda yake a waje daki-daki. Wata irin zabura tai ganin abinda take ma ɗin kuwa a saitin wuyan gawar ta gefen kunenta na haggu. Wato alamar ɗigon sarin maciji har biyu. Innalillahi wa inna’ilaihirraji’un take ambata wata irin zufan na keto mata, dan kuwa tabbas zancen mutumin can ya zama gaskiya. Amma duk da haka tana buƙatar sake tabbatar wa. Cikin rawar da jikinta ke mata ta shiga laluben number ɗin Sir Fawzan. Bugu ɗaya kuwa ya amsa kasancewar dama a jirace yake da kiran, dan ya nemeta amma bai samu ba. Yaci kuka har ya godema ALLAH dan zatonsa ma ita suka rasa. Cikin rawar murya ya ambaci sunanta duk da yaji muryarta. Amsawa tai da kuka, bata jira cewarsa ba tace, “Sir kaji tsoron ALLAH ka sanarmin gaskiya akan iyayena. Na rokeka karka ɓoyemun komai”. Zufa ce ta shiga karyo masa tako ina, dan baiyi tunanin jin wannan tambayar bazatanba a bakinta.

Shirunsa ya sake tada hankalin Iffah, ta cigaba da masa magiyar da dole ya faɗa mata gaskiyar data buƙata. “Tabbas na ɓoye miki Iffah, amma tun bayan barinki gida baifi da kwanaki ba aka rasa ɗan uwanki da Babiy sakamakon……”

Ya zayyane mata labari tiryan-tiryan kamar yanda ya bincika. Babu kuma banbanci da abinda ta gani a wancan video ɗin na farko. Ya kare da faɗin, “Wlhy har yanzu akan binciken inda aka kaisu ake amma babu labarinsu. Nima kuma a yanzu haka ina yin nawa ta ƙarƙashin ƙasa amma har yanzu ban samu wani bakin zaren ba….”

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button