Hausa Novels and Stories

Idon Naira 24

Sponsored links

Haj maryamah ta nufa dan Bata hakuri akan lamarin Amma Kuma bacin ran Haj maryamah din yafi na Umma Dan kuwa Kai tsaye ko wannan karon tabata zabi akan idan hartayi auren Wanda baasan asalinsaba Babu ruwansu da ita sun rabu kenan har abada

Hankalin Zainab ya tashi Dan haka Bata tsaya shawara ko tunaniba tace ta hakura da auren ta fasa.

Hakan ya daki ran Aqeel sosai tareda Jin bacin rai da kunyar halayen mahaifiyarsa…

Daga umma har Haj maryamah Babu Wanda yayiwa Zainab sassaucin bayyanarda bacin ransa Dan haka tashiga wani mummanan Hali na damuwa da qunci tareda ‘dacin zuciya Mai tsanani.

Halinda tashiga yasa Aqeel akaro na farko tsayawa da raayinsa akan na ummansa da ummarta.

Dukkanin harkar tafiyarsa karatu ya sokesu da Kansa tareda sanarda mahaifiyarsa ya fasa tafiya koina.

Babbar sabuwar rigima lamarin ya koma Wanda ya haddasa bacin rayuka tareda koke kokenda yawanci Zainab ce tafi Yi Dan ita aka yabawa laifin wannan karon har dangin mahaifin Aqeel din ita suka dorawa aka ringa tofa Mata maganganun gori marasa dadi.

Karshe dai da rigima taqi qarewa har saida umma tazo da nata bacin ran hakama haj Maryamah har gadon asibiti sbd jininta daya hau sosai Dan kuwa tashin hankalin da bacin ran Aqeel babu wanda bai ganiba qarshe dai kusan Zainab din yakeda niyar zaba akan kowa Dan haka tashin hankalin Zainab da baqin jininta saiya qaru.

Dangin mahaifin Aqeel dinma sai suka maida zancen Kuma akan Haj maryamah suna sukar tarbiyarta da wadda tabawa Aqeel din tako Ina duk sai komai ya qara lalacewa.

A ranarda taga yanda Haj maryamah ke zubda hawaye akan Aqeel zai jikinta yayi sanyi Dan kuwa tasan zubar hawayen uwa ga danta fitinace garesa Dan haka ta yanke shawarar dakatar da duka tashin hankalin dayake gudana….Dan haka ta amince da auren Malam Sanda tabar gidan har abada kamar yanda Haj maryamah tace..

Amincewarta zata sakata nesa da Aqeel Wanda Hakan zai basa damar jituwa da shakuwar kauna da mahaifiyarsa dake ganin itace ta zama sanadin da Babu kauna Mai tsanani tsakaninta da danta.

Daga umma har haj Maryamah da Aqeel din Kansa Babu Wanda bai girgixa matuqaba da matakinda Zainab din ta daukaba a Karo na farko a rayuwart datai ikon kanta.

Kasa gasgatawa umma da haj Maryamah sukai farko

sbd Babu Wanda acikinsu yayi tunanin zata iya bude baki ma tayi wata maganar Bayan ban hakuri dazataitayi.

Magana fa ake akan Aqeel da duka tarbiyarkice da kikai masa anan yake nunawa Babu Wanda ya Isa dashi sai ke

Haka kika nuna Masa ko Zainab?

Babu me mahimmanci agurinsa sai ke da kikai wahala dashi

Mu duk bama sonsa,

Uwarsa data haifesa ma bata Sansa saike Tunda kece kika haifesa

Gashi yanzu ana magana Zaki zaqe kice aurenki kika zaba zakiyi Bayan kin lalata alaqar uwa da ‘danta Zaki tattara ki tafi ko????

Ni ban Isa ba akanki da bazaki tsaya kiji raayinaba a zancen auren idan na yarda idan ban yardaba kin zaba aurenki da kanki.

Daga qarshe dai gashinan duk Rikon amanar danai Miki kin nunamin ba nice na haifekiba.

Maganganun umma ba zuciyar Zainab kawai suke duka harda gangar jikinta datayi sanyi Tana daukar rawa da zafi sbd acikin bacin Rai da mamakin butulcin da ita ake ganin tayi ummar ke maganar,

Haj maryamah kuwa idanuwanta jajir suke sbd kukan datai na bacin Rai da Dana sanin barwa Zainab danta da Yana qarami.

Aqeel kuwa Kansa a qasa yake yanajin ciwo da radadin kalaman da ake fadawa Mamin Amma Kuma tarbiyarsa ba irin wadda zai iya musu ko sai’insa da manyansa bane,

Yasani komai zai fada bazasu bar Mamin da fada da maganganu marasa dadi ba

Yayi yayi sun kasa fahimtarsa saima laifi dayake qarawa Mamin idan Yana tsaya Mata Dan haka yayi shiru zuciyarsa data Mamin dake tsayayar hawaye da girmamata suna dukan zucuyarsu.

Har abada bazata taba son Aqeel dinta ya samu raunin karatun da su Haj maryamah din ke cewan shine ci gabansa,

Wannan sadaukarwar ta amincewa da auren ta zabi subarta har abada sbd Aqeel din tayita sbd matuqar Basu aminta da aurenba tasan kome zaayi bazai tafiba Dan shi din Dan kaifi daya ne,

Suma Kuma tasan bazasu taba amincewa da auren nataba sbd Babu Wanda zai iya yiwa Haj maryamah din bauta yanda takeso har abada kamarta….

Dan haka wannan hukuncin data zabarwa kanta shine mafita da maslahar ahalin gidan gabaki daya da hankalinsu ya tashi akan fashij tafiya karatun Aqeel din.

Sbd su Kansa dangin mahaifinsa a yanda suka dauki zafi da akace itace take zigasa Hakan

Sun bada tabbacin matuqar Aqeel bai tafi karatun ba zata bar gidan.

 

 

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button