Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 83

Sponsored links

A nitse mami take driving bayan sun bar gidansu aliyu, babu wanda yake cewa wani abu a cikinsu dan har lokacin jikinsu a sanyayye yake, ashe akwai wa’yanda suke cikin talauci irin haka? Ba karamin tausaya musu sukayi ba suka kuma tabbatar da abinda yasa aliyu ya karbi offer din, 200k Umm ta bawa aliyu ya dan siyo musu abu dake tanada sauran cash din data cira lokacin data shigo Nigeria, mami kuma tace aliyu ya kawo takaddunsa zata bashi aiki suka kuma musu alkawarin zasu dawo gobe Insha Allah……..

After a short silent Umm ta dubi mami tace;

“Dama ana irin wannan talaucin a Nigeria? This is serious!”…….

Dariya sosai mami tayi tace;

“Ta ina zaki sani kin tafi UK kinyi zamanki for a decade, atleast da kina karban cases a nan you would know”……..

“Seriously I thought everyone is living normal, not all wealthy but not this poor!”..

“Tabb wani normal, you’re thinking that way because bakisan talauci ba tinda aka haifeki upto date, dama da kinyi aiki da first degree dinki na law anan Nigeria shine zakisha cases that will clear your eyes kika gudu kika tafi medicine”…..

“Toh befi min ba? So kike duk mutaru a court, I still handle some court issues ai, you know I own a chamber in UK”…..

Umm ta fada tana dariya…..

“To ai ba irin cases din Nigeria kukeyi ba”….

“Yeah hakane da wannan kuma”….

Haka sukata hirarsu har suka karasa gida…..

Bata rai mami tayi tana fadin;

“Au haka ma zakice? Kinfiso yayita taba yar mutane haka kawai, dama ke kike daure masa gindi yake abinda yaga dama”…..

Dariya tayi sosai tace;

“A’a a’a maida wukar ni wasa nakeyi, akan me zanso yana tabata ba muharramarsa ba, bari kiga in dubata ma”…..

Karasawa tayi ta bude back sit inda fatima zainab take kwance, nan ta hangota a zaune ta kifa kanta akan cinyarta…. Ganin kamar ta farka ne ya sata fadin;

“Hey baby!”…

Dagowa tayi da sauri ta kalleta…

Murmushi ta mata tana mika mata hannu tace;

“Ashe kin tashi? Toh tawo”…..

Hakanan ta samu kanta da mika mata hannu ko musu babu, ta taimaka mata ta fito daga motar….

Rike hannunta ta cigaba dayi har suka shiga ciki…..

Suna shiga main parlour idonta ya sauka akan katon picture din Deen dake yiwa mutane welcome, hankalinta taji ya tashi sosai, lokaci daya taji batasan shiga gidan kuma, tirjewa tayi tana kokarin kwace hannunta daga na Umm…

Ganin tana kwace hannunta yasa Umm juyowa da sauri tace;

“What happened?”….

Bude lumsassun idanunta tayi sosai ta kalleta irin dama danta ne take cewa zata kasheshi a gabanta? Ta kuma dinga zaginsa ashe mamansa ce? Amma shine taketa mata mutunci…. For the second time ta karajin ba dadi akan abinda tayiwa wani taji kuma tanasan bata hakuri amma bata san ta ina zata fara ba dan bata saba ba, cikin san faranta mata tace;

“When I said zan kasheshi I don’t mean it!”…

Dariya Umm tayi ganin yarinya zata tsarata tadai basar tace;

“Oh don’t worry dear, I know you don’t mean, badai bakyasan ganinsa ba? I’m assuring you that you’ll not meet him har ki bar gidannan, now let’s get in”……

Ba musu tabi Umm suka shiga…..

Mami ce ta ruko hannunta bayan sun shiga parlourn ta kaita wani bedroom da yake da komai a ciki, ta mata providing duk wani necessary abubuwa sannan tace ta shiga tayi wanka tayi sallah……

Idar da sallanta keda wuya taji ana knocking, tashi tayi ta ninke sallayar sannan ta karasa bakin kofar, tana budewa taga Umm a tsaye tana murmushinnan nata as usual..

“Umm”…

Ta samu kanta da fadin hakan…

“Yes dear, would you like your food serve here ko zakizo dining”….

“I’m not hungry”…..

“You must be joking tun safe har dare kice you’re not hungry?”…

“I hardly eat!”….

“Bangane you hardly eat ba, who does that? Come on let’s go to the dining”…..

Batace komai ba ta fita ta bita, haka kawai mutanen suke mata kwarjini, sam bata iya musu musu…..

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button