Hausa Novels and Stories

Idon Naira 9

Sponsored links

Sanyin AC da qamshi tako Ina tashi yakeyi Dan haka sai jikin Zainab ya sakeyin sanyi Dan kwata kwata rayuwarta Bata taba zuwa irin guraren Nan ba.

Can hanyar kitchen aka nufa da ita matar tace ta jirata anan bara taje ta sanar da Haj maryamah din.

Saida Zainab tayi kusan mintuna ashirin agurin kafin Maryamah ta fito sanye cikin wata maroon jallabiya

Fuskarta da fatarta sai sheqi sukeyi tayi haske sosai taqara wani irin lafiyayyan kyau da kiba duk saita sauyawa Zainab din kwata kwata kaman wata balaraba.

Saurin sauke Kai Zainab tayi cikin girmamawa ta gaidata tareda yimata sannu da jiki na rashin lafiyar datai.

Ganin nayi masu aikin Nan idan aka biye halayensu haka zakiyita canjawa batareda kin samu yanda kikesoba gashi kina fama da laulayin Nan gwara ita din datake ‘yar uwarki zata Miki duk yanda kikeso anhuta da neman kowace me Aiki Zainab zata iya duk wani aikin gidan..

Duk Wanda zaiyi magana yayi a bayana badai gabana ba Dan kuwa Babu mai iko da ita sai ni

 

Ni ubanta ya barwa amanarta hakama akwai wanda ya taba damuwa da ita ko kulawa da itane bayan mu din?

Idan bamu qaru da junaba to meye amfanin riqon nata danayi.

Rashin buqatarta a gidanki kuwa hakuri zakiyi ta zauna da itace kawai zatai Miki Aiki yanda kikeso ba qirsa koba komai ai mijinki ne me biyan kudin karatunta Dan haka Kuma kwa fanshe guminku anan.

 

“Umma to ke kuma wa zai dinga miki duk ayyukan da ta ke yi ɗin?”

Sai alokacin Umma ta sauke numfashi tana tausasa murya tace,

“Maryamah ko jiya da mu kai magana a asibiti na sake maimaita Miki cewan Cameron zan koma can gida cikin ‘yan uwana tunda bani da kowa anan Kuma dai Tunda ba aure yanzu nakeyiba anan din gwara na koma can din cikin dangi shiyasama na sake yanke shawarar kawo Miki Zainab din Nan Dan Kinga bazan dauketa naje da itaba acan idan dangin mahaifiyarta sun sake zuwa ki miqa musu ita idanma basuzoba Tana samun miji ko wane iri ne aura mata taje nata gidan mijin kowa ya zauna lafiya shekenan.

Shiru kawai maryamah tayi sbd batasan abinda zataceba Kuma Dan haka sukai sallama kawai ta fito Kai tsaye tasa Inna Karima takai zainab Dan madaicin dakin dake hanyar kitchen Wanda masu Aiki yakamata su zauna anan Amma maryamah dayake batason qazantar masu Aiki dakin yanan sabonsa Babu me aikin data Taba zama acikinsa komai nasa na Nan sabo

masu aikin Kuma dakin boys quarters take kaisu Dan ko Inna Karima acan take yanzu hakan.

Dakin da aka bawa zainab qatuwar katifa ce aciki sabuwa da wardrobe sai madubi da toilet me girma sai Kuma zanin gado har biyu da daddumar sallah da fanka qarama ta tsaye sbd gidan koina pop ne Dan haka AC ne ako Ina Banda dakunan masu Aiki.

Inna Karima ta nuna mata ta saka kayanta cikin wardrobe

Inna Kariman ce ta shimfida mata bedsheet a katifar da kanta takuma share mata dakin tai mopping tareda wankin toilet din dayake tamkar dakin wani basarake sbd kyansa da girmansa.

 

 

 

Duk aikin da Inna Karima tayi mata tayi mata ne dan taga yanda akeyi ta koya tun yanzu din Dan a daukarta sabuwa me aikice aka kawo wadda zata karba ragamar tsaftace koina ita Kuma taji da aikin girki.

Duk aikinda Inna ta nunawa zainab din tagane Tunda Dama aikin wahala shine rayuwarta ba Wai sabon Abu bane.

Kitchen takuma janta can ma ta nuna mata yanda zatai wanke wanke a kitchen din tareda tsaftacesa.

A taqaice dai Tunda zainab ta iso gidan a ranar Bata zaunaba sai dare sbd aikin da aka fara tarbarta dashi gashi Bata Kuma ganin maryamah ba sai dare data fito tace zainab din ta dafa mata ruwan shayin datake dafo musu da suna asibiti.

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button