Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 164

Sponsored links

Tana idar da sallar asuba ta fito a dan harzance, dan so take taje ta dawo kafin ya dawo da ga massalaci. Sashen Malikat Bushirat ta nufa a yanayin badda kamar data fito. Kasancewar da dan sauran duhun asuba duk da ko’ina zagaye yake da haske babu wanda ya fahimci wanene a cikin tsirarun hadiman da suka fara ayyukansu. Koda ta shiga sashen ma tsirarune a hadiman suka fito fara shara. Cikin dabara ta dinga wucesu batare data yarda kowa ya ganta ba. Koda ta iso kofar dakin da zuciyarta yafi karkata da samunta sal data dan nutsu a kofar domin tabbatar da babu motsin komai sannan ta murda handle din a hankali ta shiga. A hankali ta sauke ajiyar zuciya tana bin dakin da kallo, babu kowa a ciki sai Malikat Bushirat din da ke zaune jingine da gado tana sallah a haka. Da alama bazata iya yi a tsaye ba. Key ta murzama kofar sannan ta karasa shigowa cikin dakin, dai-dai da ta idar. A dan yatsine Iffah ke mata kallon mamakin gain yanda tai wani irin zuru-zuru, duk rashin gane abubuwan mutum idan ya kalleta yasan akwai matsala a tattare da ita….

“Miya kawoki nan?”.

Ta fada muryarta a shake sai dai cikin bacin rai. Baki Iffah ta labe itarna cikin tunzura ta bata amsa. “Kin san abinda ya kawo ni ai. Wai ke dan ALLAH bazaki dawo cikin hayyacinki ba. Inata nuna miki hanya, inata miki kanta farga amma kin kasa fahimta saboda son zuciya ya toshe tunaninki. Wai shin dole ne sai kin saka rayukan masoyanki cikin kunci da bakin ciki ne. Wlhy ki fadama bokanyarki ta fita a hanyata, danni nafi karfin ta da izinin UBANGIJI, hakama shi wanda kuke fadan a kansa yanzu duk da dank ne. Ta shiga hankalinta ta tsaya a iya kanki ke da kika gayyaceta a rayuwarki. Why duk randa ta sake gigin zuwa sashenmu sai kunyi nadama da ga ke har ita. Ni babu abinda ya shafeni da abinda zata miki matsalarkice wannan, tunda na nuna miki qujema irin wanna ranar tun kan tazo amma kika nun ban kai ba. Idan kuma ta cika cikakkiya dan ALLAH ta zo gareni a zahiri taga ikon ALLAH, wlhy sai na sauya mata kamannin halitta da tambarin da harta mutu bazai gogu a jikinta ba”.

Tana gama fada ta juya tal tafiyarta fuuuu ta fice tana bugo kofar. Da kallo kawai Malikat Bushirat ta iya binta, zuciyarta na.raya mata anya kuwa (wannan yarinyar mutum ce? Koma dai wanda aka kira uban nata bashi bane Aljanun Ammarah din ne suka mata cikinta).…… Fitowar Jasrah da ga bayi ya katse mata zancen zucin. Sai kuma yanda Jasrahn ke mata kallon tuhuma da rudani ya sata shan jinin jikinta, ita sai yanzu ne ma hankalinta ya dawo jikinta. Duk da abinda yarinyar nan ta fada kenan Jasrahn ta jisu tunda tana a cikin bathroom…

Jasrah ta katse mata tunanin. Dan firgigit tai ta dubeta. Sai dai ta kasa amsa mata. Babu alamar wasa tattare da Jasrahn ta sake fadin, “Akia kamarfa maganar Zawjata-almilk naji, shin wane maganganu take fada miki haka masu rudarwa? Mike faruwa ne?”

Dauke idanunta tai da ga kan Jasrahn zuciyarta na wani irin gudu a kirjinta……

“Hakan na nufin hasashena nakan gaskiya kenan,Akia akwai abinda kike boye mana tsakaninki da yarinyar nan? Taya kamarki da ke matsayin mahaifiyar mijinta, shugabanta amma tazo tana datsa miki irin mijinta, shugabanta amma tazo tana datsa miki irin wadan nan maganganun cikin kaushin harshe amma ko tari bakiyi ba. Anya kuwa Akia…..

“Jasrah!!”

Ta fada a zafafe cikin dakatar da ita, muryarta adan kausashe da bata fita. Shiru Jasrahn tayi sai dai ta kasa dauke idanunta da ga kanta. Babu abinda ke mata kai da kawo a zuciya sai kausasan kalaman Iffah masu nuni da akwai wata jikakkiya a kasa tsakaninsu. Sannan kalmar bokanyar nan ya matukar tsaya mata a kahon zuciya ya kasa fadawa…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button