Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 125

Sponsored links

A ɓangaren Tajwar Eshaan kam tana fita tari ya sarkesa, jin saukar abu a tafin hannunsa da yake tare bakin ya sashi saurin kallon hannun. “Jini..” ya ambata a hankali saman lips, sai kuma ya saki wani irin wahalallen murmushi da mai da kansa ya kwantar jikin gadon yana ambaton “Sunci nasara, sun sami nasara ta dalilinki *_My Sohaa_*….” tari ya kuma sarƙesa a hankali, sai dai murmushin na nan maƙale a fuskarsa har yanzu, sai faman lumshe idanunsa da suka birkice yake yana ƙoƙarin buɗesu da ƙyar fuskar Iffah da hawayenta ne tsaye ƙyam a cikinsu. Ba mutuwa yake tsoro ba a yanzu, baya da ƙurar da zai barta a ciki, ya tabbatar itace zata sha wahala, wahala irin wadda ba ita yay mata tanadi ba. Hakanne ya zaburar da shi, yaja jikinsa da ke saki gaba ɗaya da ƙyar zuwa telephone..

 

Ana ɗagawa ya fara magana cikin son ɓoye yanayin da yake ciki. “Duk wani cctv footage na safiyar yau zuwa yanzu na sashe na ka kwashe sa, amana ko kai na haramta maka ganinsa ka ajiyesa gareni, idan kuma na rasa raina ka damƙashi ga Zawja Fareedah….”

 

Bai bada damar cewa komai ba ya yanke kiran, da ƙyar ya maida akalar wani zuwa Malikat Bushirat….

Yanayin tashin hankalin da masarautar ke ciki koma a ace ƙasar baki ɗaya dan yau mutanen da suka fito zanga-zanga akan murabus ɗin Tajwar Eshaan sunfi na kullum yasa ko fita batayi. A kallo ɗaya zaka iya ƙirga damuwarta saman ƙyakykywar fuskarta data koɗe matuƙa a cikin kwanaki ukun nan. Tayi duk wani ƙoƙarin ta iya iyawa domin ganin gudan jininta amma al’amarin ya gagara. Kuka bata san iya adadin da tayi ba ba kuma ta san wanda zatayi a gaba ba, dan anzo gaɓar da ko’a mafarki bata taɓa sakata a lissafin ƙaddararta ba…..

 

Shigowar kira a landline ɗin ɗakin barcin nata ya sata zabura dan yazo mata ne a bazata, dole ta ambaceshi da bazata dan Tajwar Eshaan ne kawai ke da wannan hurumin. Har tuntuɓe taci amma bata damuba ta caɓi kan wayar tunkan ta karasa gareta da ƙyau. Rawar jikinta dana harshe na faruwa ne a lokaci guda, sai dai muryar data doki tsakkiyar dodon kunnenta ta saka numfashinta tsaiwar wucin gadi….

 

“Ammie!…”

 

Aka faɗa da ƙyar cikin kuma rawar harshe mai fidda sautin nakasashshiyar murya mai tabbatar da amon razani ga mai saurare.

“Saiful-malik!!…”

Ta ambata itama tare da fisgar numfashinta dake kaikawo a iya maƙoshinta zuwa cikin baki kawai. Shi bai sauka a huhu ba, bai kuma fita ta hanci ba. Bata ma san ta saki wayar ba ta fice…

“Ya ALLAH Akia!…”

Jasrah dake shigowa ta faɗa da sauri tana riƙo Malikat Bushirat da gaba ɗaya idonta ya rufe da ruɗani. Son ƙwacewa take tana ambaton “Eshaan.. Jasrah Eshaan.. Eshaan zasu kashe min shi”.

Sam Jasrah bata fahimci inda ƴar uwar tata ta dosa ba, dan haka tai saurin katseta da faɗin, “Na shiga uku Akia dan ALLAH nutsu kimin bayani, mi ya dakesa?”.

Ina Malikat Bushirat ta kasa amsata, dan numfashinta ma har ya fara fisga. Bata haɗa soyayyar Tajwar Eshaan da komai ba a duniya. Tana masa wani irin makahon so mai wahalar fahimta. Duk yanda Jasrah taso tanƙwarata ta kasa, sunan Eshaan kawai take ambata da son fisgewa ta fita. Bazai yiwu ta barta ta fita a haka ba, dan haka tai saurin danna ƙofar bedroom ɗin da ƙafa. Hankaɗata Malikat Bushirat tayi, duk da taji zafi dama gata ba wani ƙwarin jikin take ji ba amma haka ta daure ta murza key. Da ƙyar ta iya zarewa ta sake riƙo Malikat Bushirat tana mai fashewa da kuka. “Akia dan ALLAH ki sanar min, fitarki a haka ba itace mafita ba, idan ma akan masu zanga-zanga ɗin nan ne ki kwantar da hankalinki jami’an tsaro bazasu barsu su ɓalla koda gate na farko ba……..”

“Jasrah ki fahimceni…..!!!”

Malikat Bushirat ta katseta cikin ƙaraji sai kuma ta fashe da kuka. Tabbas babu lafiya, ƴar uwarta a haka lallai akwai matsala. Har taune harshe take wajen ambaton, “Zan fahimceki faɗamin ko a taƙaice ne Akia dan ALLAH”.

Da ƙyar Malikat Bushirat ta sanar mata a dunƙule, nan fa hankalin Jasrah ya tashi itama babu shiri ta zabura ta buɗe ƙofar……

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button