Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 100

Sponsored links

In banda innalillahi babu abinda Mami da Umm ke maimaitawa, ko masifar da Deen yake basaji burinsu kawai a gano inda take, abun mamaki kuma mai gadi ya tabbatar ko nan da chan be motsa ba bare ace ko ta fita be saniba, bama wannan ba duk uban securities din dake gidan ba yanda zaayi ta fita wani be ganta ba…….

“Waya turoku gidannan?”….

Mami ta tambayesu…..

“Mun santa she’s our roommate, itace wacce nake baki labari mami, that unknown girl that is always covered”…..

“Really? Toh amma taya kuka gane itace bayan baku taba ganin fuskarta ba”…..

“Recently munga fuskarta mami, abinda naketa so nazo na fadamiki kenan, wallahi itace wannan din”…

Tsaki Deen yaja yace;

“Duk wannan sa idon na menene? Meye damuwarku da ita harda wani so kizo ki fadawa mami gaki gulma na cinki ko!”……..

“Toh sarkin masifa, bakaji tace she’s their roommate ba dole ko su damu ai”……

“Yanzu Umm kawai dan tana roommate dinsu shikenan sai susa mata ido, how sure are you itace wannan dinma?”……

“All this isn’t necessary, yanzu dai ta ina zaa fara neman yarinyar shine!”…….

A hankali Khaleel ya bude idonsa after almost three days of unconsciousness, sosai ya rame fuskarsa tayi fayau kamar bashi ba saidai babu abunda ya ragu daga kyannan nasa me ruda yan mata, ga mamakinsa sai gashi ya mike tsaye akan kafafunsa wanda rabonsa da tashi batareda an taimaka masa ba harya manta, toh shi in banda abinsa me kwanciya a asibiti ya kara masa? Wacce yakeyi domin ita kilama batasan yana kwance a asibiti ba, in akwai abu daya daze iya chanjawa a rayuwarnan toh tabbas weakness dinsa ne, kwata kwata be iya facing challenges ba, abu kadan sai yayi breaking down memakon yayi man up and fight for it, amma Insha Allah daga yanzu ya zama jarumi, he’ll fight for her love with all his soul, a take yaji wani strength yazo masa ya kuma kudirta a ransa this time around ba gudu baja da baya harsai ya mallaketa a matsayin mata……..

Zaune yake a katafaren parlournsa hannunsa dauke da newspaper daga dan gefensa kuma coffee ne me zafi sai tiri yake daga cikin kofin, a zahirin gsky idan ka kallesa zaka dauka karatu yake a newspaper amma ba hakan take ba dan ya dade da fadawa duniyar tinani… Besan meyasa ba kwanannan maslaha yake nema tsakaninsa da hajiya fatima amma taki bada hadin kai, in banda provoking dinsa babu abinda takeyi, yanzu gashi yace zeyiwa dansa aure tace tariga ta masa mata kamar ita keda alhakin aurar dashi, idan tana wasu abubuwan har mamaki take bashi dan shi shedane ba haka take ba saidai besan meya chanjata haka ba dan tsakina da Allah shi ta cuta amma yaga harta fishi daukan zafi akan abun alhalin itace batada gsky….. Gashi ya bata zabi akan Deen ya auri duka zabinta da nasa amma taki yarda, shikuma idan ya bari Deen ya auri zabinta ai ya zama looser kenan!…. Abun haushi kuma da yacewa Deen ya bisa su koma gida saice masa yayi akwai important abinda yake son clearing a hospital dinsa na abuja so baze iya binsa ba amma ya masa alkawarin zezo in the next three days, tsabar renin hankali harda fadamasa sudaina fada da mahaifiyarsa tunda sunki gayamasa dalilin fadansu, maganar datasa ransa ya baci kenan har yace masa karya zo masa gida tinda bayan uwarsa yakebi suje chan su karata… Gashi yanzu ya dawo abun na mugun damunsa……

Yana cikin wannan hali Mom tashigo, kamar ko yaushe murmushi dauke akan fuskarta, karasowa tayi ta zauna a hannun kujerar da yake, cikin kwantar da murya tace.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button