Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 39

Sponsored links

“Rabbis samawati wal ardi ka shiryamin shi”

Ta fada hawayenta na zuba akan fuskarsa…. Sai kuma ta janye ta nufi gadon da fatima zainab ke kwance……

Wani mugun tausayinta ne ya kama Deen dan tinda ta tsaya akansa ya farka,saidai yaki bude ido,be karajin tausayinta ba saida yaji hawayenta na zuba akan fuskarsa,shida kanshi ya rasa yanda zeyi da rayuwarsa,shi sam baya ganin rashin jin da yake su kuma sai su dinga masa kallon tantiri,Fisabilillahi meyayi toh?,ganin ta nufi inda fatima zainab take yasashi binta da ido,sai a lokacin yagane a gadon asibiti suke,toh kenan accident sukayi?,toh ina take?,kodai itace a kwance…. Daurewa yayi ya mike a hankali duk da bashida lfy amma baze iya hakura ba,dole shima yaje ya ganta…..

 

Tinda ta karasa gaban gadon da fatima zainab take bugun zuciyarta ya tsananta,kasancewar an rufe mata rabin fuska ya sata yaye lullubin…. Sauran kadan ta zube a kasa da ganin fuskarta,Deen daya tawo ya tareta da sauri duk da bawani karfi yakeji sosai ba amma dayake yanada dauriya bazaka gane hakan ba,da sauri ta juyo ta kallesa tace

“WACECE ITA?”….

Be kulata ba dan besan meze ce mata ba,kawai ya karasa gaban bed din yayi yashiga binta da kallo……

Dafe kirjinsa yayi ya matsa gefe da sauri yana fadin

“Hasbunallahu wa ni’imal wakeel”…..

Ganin Deen be bata amsar tambayarta ba yasata fita da sauri,tana dialing number jamila,ringing uku Jamila ta dauka….. Baki na rawa tace

“Ya hayyu ya kayyum jamila you wouldn’t believe what I saw,anya bamu shiga uku ba kuwa?”….

A kideme jamila tace

“Ya allahu me kika gani,dan Allah fadamin yaya?”…..

“Nace ki fadamin abinda kika gani pls”….

Jamila ta fada tanajin kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a Nigeria…….

“Hmmm wannan maganar bata waya bace!,just come and see for yourself!”….

Numfashi ta sauke daga daya barin tana fadin

“Just tell me,I promise you I’m on my way today,koda hint ne ki bani,har kinsa zuciyata tinani iri iri wallahi”…

Sosai Deen yake kallonta kamar tsohon maye,ayanda yake karewa fuskarta kallo yasan tsap aka basa abun zane ze zanata,kyakkyawa ce ajin farko,irin kyawunnan me shegen daukan ido da kallo daya zaka yiwa mutum kasan yanada kyau,fara ce amma ba chanchan ba,color dinta kamar dai half cast,kallonta ya karayi tindaga goshinta harya karaso habarta,goshinta na dauke da dot din sallah kasancewarta ma’abociyar ibada sosai,hakan sai ya kawata kyawun fuskarta,gashin girarta baki wulik ne da saika dauka tayi brow tint,gashi da curve shaped me kyau,tsabar cika har hadewa girar keyi,it’s just a perfect curved brows!…. Murmushi yayi yana kallon dogon hancinta me kyau kamar ka cireshi ka gudu,ana cewa yana da dogon hanci yau sai yaga na wacce yafi nashi kyau?….

“Fatabarakallahu ahsanul khaliqeen”…

Ya fada beneath his breath a yayinda ya kara dora idonsa akan idanunta dake a rufe,ko a haka mutum na gani yasan manyan idanu ne da ita,toh inaga inta budesu?… Dafe kai yayi jin mere thought of bude idanunta is driving him crazy…

Ya fada yana sauke idonsa akan pouted cute lips dinta,ze iya cewa tinda yake be taba ganin cute attractive lips irin nata ba,infact shi be taba karewa mace kallo irin haka ba sai akanta,sai kuma ya fara tambayar kansa anya shi psychopath ne kuwa kamar yanda ake fada? Cuz what he’s feeling is a raw feeling,bawai sonta yake ba dan ba wannan a dictionary dinshi,but he’s actually feeling something unusual,kamar magic haka yaji abu na fizgarsa zuwa gareta especially her lips,he just want to know how they feel,a yanda yake kallonsu daga gani zasuyi laushi so he wants to confirm,ba wai kissing dinta zeyi ba,he just want to screen them with maybe his fingers,yasan idan ya shafasu ze gane,karasawa dab da ita yayi yana cigaba da kallonta……..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button