Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 59

Sponsored links

Sai kuma ya kalli fatima zainab ya harareta yana fadin;

“Ashe a cikin kwashe kwashen naki harda shaidani? Ba dole kita abu kamar mara hankali ba, zamu gamu ne in kika farka, saina saitaki da kyau kafin in kaiki gun iyayenki!”..

Sai ya maza ya zuge glass dan bayason jin abinda wanchan wawan zece, wani cassette din Quran yasaka ya kunna suratul baqarah yayi bismillah ya sake tashin motar, cikin ikon Allah ko motar ta tashi, figarta yayi a guje ya bar wanchan da sakekken baki……….

Kuka yakeyi sosai cike da nadama, tsugunawa yayi har kasa yana basu hakuri akan su taimakeshi su rufawa masa asiri…..

Mami kuwa har lokacin bata gama dawowa daga shock din data shiga ba, she always know Deen as a stubborn person amma bata dauka rashin jinsa ya kai haka ba, wani kalan hatsabibin yaro ne Allah ya bata haka? Like how could he even think of this? To ina ya tafi haka…..

Dawowa daga tinanin tayi jin Umm na fadin;

“Idan zaka fadamin gaskiyar abinda ya faru na kumayi bincike na tabbatar gaskiya ne, I’m assuring you that abinda ze sameka”…

Da sauri cikin kuka yace;

“Wallahi zan fadamiki, bazan yi karya ba”…

“Good, now tell me how you got here, in full details!”…..

Nan ya shiga basu labarin yanda wani ya hadasa da sameer, da irin matsalolin rayuwar da suke ciki, da rashin lafiyar mahaifiyarsa wanda shine main abunda yayi pushing dinsa ya karbi offer din, da irin alkawarikan da sameer ya masa idan ya gama aikin, har zuwa yanda aka barsu sukazo inda Deen yake, sukashi anan su kuma suka fita……

Kamar hadin baki Umm da Mami suka sauke numfashi dan harga Allah sunji tausayinsa saida as an interrogator bazaka gane hakan ba akan fuskar Umm…….

“For how long sukace zakayi replacing dinsa”

Umm ta fada with a serious look…

“Banji ba gaskiya, kamar dai budurwan dayan ce, wanda yake gurin nan kamar rakasa yayi”….

 

Tafi kai Umm tayi tana kallon mami tace;

 

“Shit! Kinsan Allah yaya haka kawai naji hankalina be kwanta da visiting din da kikace abokinsa ya kawo masa ba, see the way they fooled us dan Allah!”…..

 

“They fooled us absolutely, amma karki damu we’ll get them soon, sai sun gane shayi ruwane, I’ll make sure I deal with them mercilessly! Sameer ya bani mamaki, ina masa kallan nittsatse kamar yafi Saifuddeen hankali ashe duk kanwar jace?”….

Mami ta fada cike da takaici….

“Ai ko ni this time around bazan ragawa Saif ba, he’ll see the very other side of me!!”…

Umm ta fada tana daukan mask din data fuzge a fuskarsa, mika masa tayi tace;

“Wear dan in wani ya ganka a haka you’re in big trouble! Wait kasan nature of crime dinsa ma kuwa?”….

Girgiza kai yayi alamun be sani ba

“Ah lallai your dumbness isn’t in this world, how could jump into a job like this without asking for the person’s crime? Imagine a hada baki da yan gurin nan azo a kashesa anan inda kake do you think they’ll give you the chance to claim yourself”….

Cikin kuka ya shiga kada kai dan ba karamin ahigarsa maganarta tayi ba….

“Toh an kashe banza dan shi bashi da asara and I’m very sure ko addu’a bazena maka ba dan mantawa zeyi da kai, hankali kwance ya cigaba da rayuwarsa, so don’t ever try this stupid act okay?”..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button