Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai Book 2 13-14

Sponsored links

Cele tana Palo ta tara Apple a gabanta tana ta faman ci,a fili tace na rasa wannan bala’i da ya sameni a kasar nan nidai ci ci ta sake ballar Apple tace ga dadi har Ido take lumshewa tace na daka bai kalli gari ba garin Dadi ba kusa ba uhmmmm…..tana taunawa tana ci tace ga sha’awa to sha’awar namijin na mene haka, aure nake so ta bawa kanta amsa tace Allah ka hadani da Kaka nace Kawai yayi min aure,to iyayena wasu iri ne nasan Baba ma ko cokalin silver bazai siya min ba bare gashi Kaka ba kudi ba ya zama dole na nemi kudin aurena.

Sallama Ahsan yayi Cele ta amsa ta kalli Maheerah ta rike hannunsa Kawai sai taji ba dadi bata so taga hanunsu rike ba tana shakar mata kamshin abokinta cewar Cele aa fili tana ballawa Maheerah harara tana Jan Tsaki,tafi tayi ta hau murguda baki tana fari da Ido irin na rashin kunya tana gatsinawa Maheerah fuska,karfin hali kenan tashi tayi tayi Kamar kitchen zata je ta tsakiyarsu tazo zata wuce ta tsinka hannun da Maheerah ta rike masa, Maheerah Kamar ta soke Cele da wuka,Cele Kuwa mamaki takeyi yau Ahsan fuskarsa ba Rahma gaba daya ya canja lafiya,Maheerah ce tace muje ka kwanta ka huta Noorul Qalb,bedroom suka shiga Kawai Yana binta sai da ya kwanta a saman bed sannan yace Dan Allah ko zaki iya fita nafi bukatar zamana ni kadai,Maheerah tace ba damuwa Habibi ta juya ta fita,Kansa ya dafe yana Jin azabar ciwon Kai da zazzabi ya rasa ma me zaiyi.

Maheerah Kuwa tv ma ta kunna abinta aka kawo Mata abinci lafiyayye taci abinda take so ko kula Cele bata yi.

Sadiya da mafi yawan matan da Suka Zo duk yanzu sunyi fari tas sun samu man bleaching a wajen takari suna siya suna shafawa sun Zama fararen dole,fari Kuma marar kyau mummunan haske marar kyan gani kana gani kasan farin Mai ne, Sadiya yanzu bakin balaraben Sudan zata aura shima kudi zata samu,yau mairo bata Kai tallanta ba sai ta kasa gumama a gefen kwalta hanyar harami,duk ga takari nan Mata da maza sun kasa musu Kaya a gefen titi abinda basa so,Motar ruwa ce tank tazo Kawai ta saki ruwa a titin Yana tafiya da kayan da Suka kasa gaba Daya Suka hargitse suna faman kwashe kayansu larabawan nan ma’aikata ba abinda ya dame su Kawai sun dauke su wasu banzaye Kawai titin ake wankewa ga motoci masu mopping suna tafiya a hanya ana goge titi ko Ina Kal kal,suna kwashe Kaya askarawa Suka Zo masu kame sai gudu takai takai ko wacce takari ko da Namiji ne sai gudu Kawai ba tsayawa,Mairo da kyar ta Sha sabo da cikinta ya tsufa gaba daya,Samira wacce suka dauki wankan Abaya sun fito kenan Suka samu ana kame wani Dan Sanda ya bisu suka Sha kwana Samira tabi ta wani lungu Wanda ashe baya bullewa Dan sandan Yana zuwa ya riketa tare da zaro waya Yana Kiran yan Uwansa ma’aikata su zo, kafin kace me Samira ta Masa wawan duka a hannun ta hambereshi ta fisge Wayar ta kwashe da gudu ta bar lungun tana gudu a haka ta kashe wayar gaba daya sai gidansu tana cewa na samu waya a banza.

Wasila kuwa ta dakko soyayyun kajinta zata Kai gidan bakake Kawai sai ji tayi an dauke daron kajin dake kanta tana juya taga Yan Sanda sun juye kajin a cikin shara suna cewa da larabci bata rufe abincin ba duk Kura da cuta ta hau Kai zata siyarwa mutane Suka taka zasu kamata itama ta kwashe da gudu tana gudu ta hadu da Khulsum itama takari ce Suka kwashe da gudu tare suna gaba Suka rankaya da wasu takarin Yan Sanda ta ko Ina sauran sun hakura sunga su Wasila baza su kamu ba amma wani Dan naci mutum daya ya bisu har layinsu ai Kuwa takarin Suka hadu tare da Masa dukan tsiya Suka kwace Masa waya da kudin Dake aljihunsa Suka fece,Wanda aka Haifa a can Kuwa Wanda ake Kira da Yan agulla suke yiwa babaken mu Yan uwansu dan Kira Kamar su ba bakake bane sabo da Kawai su sun Zama Yan kasa in Suka ga wasu ko aikin Hajji Suka je sai su dinga musu dariya Suna musu Dan Kira da fito kana ganinsu kasan basu da tarbiyya duk gashinsu sunyi kitso wasu sun Masa gyara na Yan iska.

 

Bayan kwana biyu Sadiya ce ta fito da Yamma likis zata je siyayya ta hango dandazon Yan agulla sunyi dandazo wasu a saman mota a zaune sunyi parking sun saki kida suna ta rawa wasu Kuma suna tsaye suna ganin Sadiya Suka Fara nunata suna sheka dariya suna siiiiiii,tsautsayi yasa Sadiya ta juya ta kalle su sai kuwa Suka Fara daga Mata gira suna kashe mata Ido,da larabci ta zage su duk Suka biyota tana gudu suna binta sai da Suka kamata Suka Mata dukan tsiya sannan Suka tattabe Mata nono Suka barta nan tana kuka suna ta dariya tare da tafawa Yan Uwa bakaken fata haifaffun can.

Santana a kitchen yake yana taya Jamcy girki duk wani shaye shaye ya gama sa wa Jamcy Ido bata Isa tayi kwakwaran motsi ba Yana kula tun bata Saba ba har ma ta saba, Jamcy tana kallonsa tace oh ashe haka ka iya girki? Santana ya kashe Mata Ido daya yace ai mace ma Sai dai ta biyo bayan mu,Saura kadan fa Dangote ya dauke ni na dinga Masa girki a gidansa Allah ya tsare Nawwar yazo yace Sam aure zaka yi Santana ban yarda ba,to abinka da me kudi Santana ya tafa hannaye yaci gaba da cewa nace sa ranka a inuwa Nawwar an gama Indai Santana ne ruwan sanyi ne,shine na taimakeki nazo neman aurenki Kawai dan muga karshenku ke da Sabreen Amma Allah ya taimakeki local government ta fanshe ki kina da sweet kin tafi da zuciyar Santana idan kinyi biyayya ba abinda bazan Miki ba amma idan Kika tsaya shirme da shaye shaye kishiya farilla,dariya Jamcy take yanda yake magana harda wani iyayi yake mata,lips ta turo Masa tace ungo ya bata kiss muahh tare da furta ko ke fa amma ki zauna kina shaye shayen banza kina biyewa Sabreen me kugun lion haba abu wani tsukakke ,

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button