Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 162

Daudar Gora Book 2 Page 162

Sponsored links

Dariyarta mai tada masa tsigar jiki tayi da fadin, “Nima fa kadan birgeni a ranar, dan kamshinka ya tafi dani matuka da wadan nan fararen idanun masu kyalli kamar madara. Kawai dai ranar haushin kowa nakeji ne sai na samu na sauke akan yaranka. Wai kuwa suna ina ma?”.

Murmushi kawai yayi baice komai ba, sai da ya mula da kansa sannan ya magantu. “Uhm ashe nayi babban kamu tun a ranar faro amma aka tsiwaceni tas. Ke ta dabbance yar kanwata. Su Azaan suna nan abinsu, ma’aikata ne a gidan jaridata ta AFRICAN EYE. Inda kika so zuwa ki tone mun asiri da min zigidir a bainar nasi ALLAH ya taimakeni”.

Hankalin Jasrah ba karamin tashi yay ba da yanayin data samu yar uwarta. Rasama abinda ya dace tayi tai, a rikice tai kiran number likitan Malikat Bushirat din. Cikin kankanin lokaci kuwa sai gashi. Shima hankalinsa ya tashi, dan shi abinda ma zuciyarsa ke raya masa da ban da wanda ke a hakika. Zai zauna bin ba’asi Jasrah ta katsesa da fadin, “Yanzu ba lokacin sanin miya faru bane. Ceto rayuwarta shine mafita first”.

 

 

 

“Hakane”

 

 

 

Ya fada cikin gamsuwa. Da taimakonsa suka maidata saman gado, babu bata lokaci ya shiga aikinsa, ya samu nasarar tsaida jinin, tare da ceto numfashinta da tuni yabar gangar jikinta. A tare suka saki ajiyar zuciya bayan daidaiton komai. Jasrah ta dubesa cikin roko ta ce, “Doctor Please wanna al’amarin ya tsaya da ga ni sai kai dan ALLAH. Dan yana da kyau mu fara sanin abinda ya faru da ga bakinta karmu tashi hankalin mutane. Musamman ma Shahan-shan abubuwan zasu masa yawa. Ga wanna rikicin da yake ciki ga kuma wannan. Shima mutum ne kamar kowa yana bukatar sassauci”.

“Gaskiya ne ranki ya dade. Insha ALLAHU baki da matsala. Dan aikina ne wannan. Ki dai kasance a kusa da ita dan zata iya farkawa a firgice kasancewar daga suma muka maidata barci, Sannan gaskiya ya kamata kusan abinda ke damunta Kinga wanna fa shine karo na biyu, zata iya samun matsala idan haka ya cigaba da faruwa. Dan yanzu haka da kyar na samu bugun zuciyarta ya daidaita, ga jininta ya hau matuka sai tana samun kulawa lafiyarta zai samu daidaiton da muke bukata”.

 

…..Bayan wucewar Doctor jagwaf Jasrah takai zaune idonta akan yar uwar tata. Abubuwane da yawa ke mata kaikawo, ga dunbin mamakinta da al’ajabin wai mike faruwa haka? Ko ita dake a cikin halin tashin hankalin hallayar mijinta batajin tana a rabin wannan yanayin. Amma ita da bata nema komai na rayuwa ta rasa ba tarasa mike faruwa da ita. A kwanakin nan fa har rama tayi, sannan zaka ganta jigum kamar mai tunani duk ta hargitse. Gaskiya ta fara ji a ranta lamarin ya fara zarce na kiyayyar Iffah kawai. Akwai dai abinda take boye musu da ya kamata ace sun sani, dan al’amarin ma kamar gaba- gaba yake. Jiba dai yanda ta hargitsa dakin yau gaba daya, ta fasa abubuwa masu daraja da tasan ko sanda suna yara bata bari su taba mata. Tashi tai da kanta ta gyara komai, dan kiran wata hadima ta gyara kamar yana nufin fitar zancen ne, dan hadimai da yawa dake akowane sashe zaka samu an leken asirin wasu ne. Musamman ma ita da girman ikonta yasa kowa kunnensa bude yake da son jin labarin wani al’amari ya bullo da ga gareta makamancin haka. Tana cikin gyarawar doctor ya kirata ya dawo, ajiye aikin tai taje ta amso magungunan ta daw sannan ta karasa gyara komai ya koma need.

Gabannin asuba ta farka a wani irin firgicen da yafi wanda ma Doctor ya ce zata iya tsintar kanta a ciki. Yanda jikinta ke rawa haka gadon ke rawa, ta fasa wata irin gigitacciyar kara ganin halittun da suka firgitata a cikin barcinta zahiri muraran a cikin dakin. Gaba daya sunma gadon zobe ga wani kalar kuka da sukeyi mara dadin saurare a cikin kunne., Sotake ta ambaci sunan ALLAH koda sau daya ne amma bakinta ya gagara furtawa, sai rawar da lips dinta keyi kamar yanda jikin nata ke rawa. Duk da sanyin ac dake dakin ita a jike take sharkaf da zufa kai kace wanka tayi.

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button