Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 165

Sponsored links

Koda ta koma ta iske ya dawo sai dai ya wuce Gym.Ajiyar zuciya ta dan sauke ta canja kayan jikinta ta nufi kitchen. Yau ma da kanta ta hada masa abincin breakfast din, suko masu girkin duk sun tsargu duk da tare da su take yi. Sai dai aikinsu kawai bani kaza yankamin kaza wanke mun kaza. Amma komai ita da kanta ta hada abunta. Ta kuma tsaya a kansu har sai da aka kawo komai dining room din.

Ya fito da ga wanka kenan ta shigo da sallama hanunta dauke da tray mai dauke da kofin shayi da keta faman turiri. Ido ya dan tsira mata har ta iso gabansa ta ajiye. “Good morning “. Ta fada tana zuba zuma kadan a shayin. Cikin dan lumshe ido da budewa ya amsa mata da “How Are you”.

“Alhamdullah”.

Ta amsa masa itama tana mika masa kofin shayin.Amsa yay dan dama shi yake jira. ya ce, “Thanks”. Kai kawai ta dan jinjina masa tana murmushi. Da ga haka ta wuce bathroom dan yin wanka. Kallo ya bita da shi kasa-kasa zuciyarsa na masa kaikawo.

Lokacin da take fitowa har ya kammala shiryawa,dan haka ya taimaka mata itama ta shirya cike da tattali da kulawa. A tare suka fito cin abincin gwanin sha’awa. Duk abinda take kallonta kawai yake cike da so da kauna harta kammala hada musu komai. Bismillah ta masa tana masa nuni da abincin da ido ya make kafadarsa yana kauda kai gefe. Hannu ta kai ta dan ja masa kunne tana murmushi, sai hakan yay dai- dai da fitowar amintaccensa da basu san da shi ba da ga cikin karamin falonsa ya gyaro. Da wani masifar sauri ya juya har yana cin ban tuntube dan idonsa ras akan hanun Iffah da ta ja kunnen Shahan-shan din nasu. Itama idanu ta waro da sauri ta mike da sauri ta rungumesa. Dan harga ALLAH bata san bayan su akwai wani a wajen ba. Da kyar ya danne dariyar dake taso masa ya danna mata mintsini a gefen ciki shima, tako zabura gaba dayanta ta haye saman cinyarsa

Yau din ma kotun ta cika sosai,harma wanda basu halarta a jiya ba yau kam sunzo, Sai dai babu Malikat Bushirat. Dan tana can wani irin zazzabi mai masifar zafi da ciwon kai sun lullubeta har sai da Jasrah ta sake kiran likita ya dubata. Ta gama shirya ana gama zaman kotun nan gida zataje, dan ita kam har yanzu a cikin rudani take. Zataje ta sanar da babban yayansu da a yanzu shine kamar uba a wajensu komai tunda ita taki fada mata. Maybe su sai suzo su binciki wane irin TAKUN SAKA ne tsakaninta da surukar tata da har irin wadan nan maganganu ke shiga tsakaninsu. Yanke wannan hukuncin ya sata nufo kotun kamar yanda kowa ya hallara. Iffah tare da su Daneen Ammarah da su Ummu yau ta shigo. Dan suna kammala breakfast sashen Malikat Bushirat taje ta gaishesu kasancewar lyyani da Ummu a can suka kwana. Barrister Abdallah Aas da Abu Zainab kuwa tun a jiyan suka wuce gidajensu da iyalansu. Kaka ma kin kwana yay, sai suka wuce gida shi da Babiy da Hanash akan yau sa dawo. Ya kumayi hakane dan yana so suje su tattauna inda za’a nemawa Daneen Ammarah (Mammy) wajen zama itama. Saboda Tajwar Eshaan ya sanar musu ana yanke hukuncin nan zuwa jibi insha ALLAHU Mammyn (Daneen Ammarah) zata tare gidanta.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button