Hausa Novels and Stories

Abban Sojoji Chapter 29

Sponsored links

Tsawa tayi tana faman sauke ajiyar zuciya, after some minutes sai gashi ya fito jikinsa sanye da jeans da t-shirt, hannunsa ruƙe da wayarsa ya samu wuri ya zauna saman Sofa, cikin sauri sehrish ta gaishe shi “Barka da safiya, fatan ka tashi lafiya,” a tunaninta bazai amsa ba amma sai ji tayi yace “Alhamdulillah Am well,” murmushi ta ɗan saki, kafin ta shiga haɗa masa Tea a cup mai ɗan xafi ta tura masa agabansa, hannu yasa ya ɗauka yakai bakinsa yana kur6arsa a hankali, ci gaba da saving ɗinsa sehrish tayi, kamar daga sama taji yace “Meyasa jiya ba’a kawo min fruits dana buƙata ba”!?

 

Murya na rawa sehrish tace “na same ka kana bacci ne lokacin dana kawo maka,” ta ƙarasa maganar tana kallon fine face ɗinsa,

 

Bayan wasu mintina ya kuma cewa “daga yanzu inaso a rinƙa kawo min Coffee or Tea wit fruits around 12 pm,”

Cikin hanzari ta amsa mashi da cewa “Insha Allah,” jinjina kansa ya ɗanyi yayin da yake ci gaba da cin pancakes ɗin data haɗa masa da Zuma,

 

tsayawa sehrish tayi tana jiran ya kammala ta zuba mashi wani abun,

 

Wayarsa dake ajiye a gefensa ta soma ringing cikin sauri takai hannu zata cirar mashi tissue ya goge hannunsa adai-dai lokacin shima ya miƙa hannunsa zai cira karaf suka haɗa hannunsu cikin na juna 😌 zaro ido sehrish tayi cikin tsananin jin tsoro tana ɗan kallonsa,

 

Shi kuwa bin hannun Yarinyar yayi da kallo sam ba’a yi masa irin haka amma yayi mata Uziri ne saboda da alama batasan ko shi wanene ba, gata kuma ƙaramar yarinya,

“Am sorry,…’ sehrish ta furta aɗan tsora ce yayin da ta janye hannunta, shi kuma ya ciri tissue ɗin a natse yace “Don’t repeat that mistake again,”

 

Cikin sauri tace “Insha Allah,” goge hannunsa yayi sannan ya ɗauki wayar ya ɗaga kiran tare da karawa a kunnansa, taso taji mai zai ce acikin wayar amma sai dai kash cikin wannan harshen taji yana magana wato Espanol da alama yafi jin yaren sosai ko kuma shi ya taso yana ji,

 

Zuba mashi ido tayi tana kallon shi tun daga shafaffen cikinsa har zuwa saman wide Chest ɗinsa haɗaɗɗiyar ƙira, maganar haroon ta tuna dayake cewa Zaren ba Kalar yadin bane Iska ce kawai zata wahalar da mai Kayan kara, tabbas kuwa yayi gaskiya amma in ta tuna wannan karin maganar da ake Cewa

DUK KYAN TAKALMI ƘAFA CE ZATA TAKA SHI* sai taji wata irin natsuwa tazo mata, tana tunani tana ci gaba da kallon fuskarsa yadda yake Moving pink lips ɗinsa yana magana tamkar baison yi, da kuma yarda yake faman lumshe sexy blue eyes ɗinsa ba ƙaramin Yanayi yake jefa ta ba,

“Allah yasa bada budurwarsa yake waya, koda yake aunty azmee tace baya soyayya, To Allah yasa dai bada mace yake waya ba,” ta faɗi acikin zuciyarta saboda ganin yarda yake ta faman lumshe idonsa kamar wanda ke waya da mace cikin shauƙi.

tana cikin yi mashi wannan kallon ƙurullan nata ya kamata, adai dai time ɗin ya ɗan ware idonsa direct suka sauka kan na sehrish dake faman Zuba masa ido tana kallonsa abunda ya tsana arayuwarsa ba, sam bata lura daya kamata ba saboda idonta na akan Sumar kansa, har sai da ya ɗanyi gyaran Murya cikin sauri ta wurga kwayar idonta kan tashi aikuwa har sai da ta ɗan Razana ganin ya aza idonsa acikin nata Unexcepted,

 

ƴar harara ya wurga mata sannan yace “Stop looking at me, i don’t like,’ ya faɗi tare da cigaba da yin wayarsa,

 

Sunnar da kai sehrish tayi cikin jin kunyar Kamatan da yayi tana masa kallon kurulla, amma wannan hararar daya sakar mata ba ƙaramin kashe mata zuciya yayi ba,

ya jima yana wayar kafin ya kammala ya ture ta gefensa, sehrish ta cigaba da saving ɗinshi harya kammala cin breakfast ɗin nasa sannan ta tattare komai ta fuce dasu kitchen ta ajiye agefen Kitchen sink yadda in tadawo wankewa kawai zatayi,

 

Daker ta iya fitowa daga kitchen ɗin saboda taga duk sun Hallara suna yin breakfast, tunkarar su tayi gabanta na faɗuwa saboda ganin hada HAROON zaune ga kuma Twins duk suna zazzaune, tunkan ta isa junaid na ganinta yasoma sakin murmushi kamar gonar Auduga, sallama tayi masu suka amsa sannan ta kalli Abbansu wanda keta faman sakar mata murmushi tace “Ina kwana Abba, fatan kun tashi lafiya,” Abban nasu yace “Alhamdulillah My Only daughter, yanzu nake tambayar azmee take cemun kin shiga kaiwa Babban yayanku Abinci

Eh hakane,” ta bashi amsa sannan ta juya ta kalli sauran ta gaishe dasu duk suka yi tsit sai kanal Yusif daya ce “Ae nayi tunanin bazaki gaishe da yayyen naki ba, yanzun nan nayi fushi dake,”

Murmushi sehrish tasaki tana mai mamankin hali irin na kanal Yusuf sam bakamar na sauran ba,

“Samu wuri ki zauna mana,” Abbansu ya umarce ta kujera taja ta zauna zuciyarta na ɗar ɗar, tana a jerin inda Abbansu yake gefensa junaid daga shi sai ita, a ɗayan side ɗinta kuwa haroon ne tabbas tasan dole ya hantare ta, ga kuma AYAAN Da JAHAN da take facing ɗinsu duk ta tsargu saboda tasan halinsu suna jere tare da kanal yusif,

azmee da kanta tayi saving ɗinta acikin plate ta buɗe saving dish ta zuba mata Chicken pper soup

 

Sannan ta haɗa mata da Cofee acikin Cup☕ Sehrish ta kalli azmee tare da cewa “nagode aunty amzee”

hararar ta amzee tayi alamar cewa bata son godiyar,

 

..a hankali take kurbar coffee ɗinta duk da kermar da hannunta ke yi, muryar haroon taji a ƙunnanta yayi ƙasa ƙasa da Voice ɗinsa don kada wani yaji yace”Su acici mala’ikun tauna, an fa samu wurin zama, to adai ci ahankali kar a shaƙe,” banza tayi dashi batace komai ba, amma sam tarasa cin chicken ɗin dake agabanta shaƙe cikin plate,

 

Sanyayyiyar muryar junaid ce ta ratsa kunnanta da cewa “Sehrish ya akai naga yanayin ki ya canza? ko breakfast ɗinki baki fara ci ba,”

 

tace “bakomai junaid kawai bana jin daɗi ne, inaji kamar na tashi na tafi ɗaki kawai,”

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button