Hausa Novels and Stories

Abban Sojoji Chapter 23

Sponsored links

Ida sa iso wa inda suke sgr yayi idonsa yakai kan Jahan daya zare belt ruƙe a hannunsa, tunkan yayi magana jahan yayi hanxarin mayar da belt ɗinsa, mayar da idonsa yayi kan Abban nasu tare da cewa “Gm dad fatan an tashi lafiya,” murmushi Abban su yasaki da cewa “Lafiya Lou son ina fata kaima haka,”

 

Sgr yace “Alhamdulillah,” sannan ya samu wuri ya zauna saman ɗaya daga cikin dining chairs ɗin, kowa so ya ke yaji mai Babban yayan nasu zai ce, musamman haroon burinsa Sgr yace bai amince da zamanta ba, don yasan in dai yace hakan to Zaman sehrish ya ƙare a gidan

,  Ita kuwa sehrish hankalinta kwance saboda tasan yarda su kayi jiya dashi haka azmee ma, gyaran murya sgr yayi kafin yace “tsayuwar me kuke yi”? Ya tambaya yana kallon su jahan Ayaan da kanal yusif, koma wa su kayi kowa ya xauna junaid ma yasamu wuri ya zauna, sai Abban nasu dake tsaye sehrish na agabansa yaci gaba da cewa “daga yau kin zama ƙanwarsu kema ƴa’ ce acikin gidan nan, duk wani abu da uba keyi ma ƴarsa nima zan miki shi, kuma duk wani abu da junaid zaiyi acikin gidan nan kema zaki iya yin shi, kuma duk wanda yayi yunƙurin 6ata miki acikinsu ki sanar mun zaki ga yarda zanyi dashi,”

 

Zuru su kayi suna sauraron Abban nasu, sehrish kuwa murmushi kawai take saki koba komai yau tasamu Uba wanda zatayi prouding dashi a faɗin duniya,

ɗago idansa yayi ya kalli Babban yayan nasu, wanda azmee taci gaba da saving ɗinshi breakfst ya kira sunan shi “RAFAYET” amsa wa yayi da “Na’am Abba,” batare da ya juyo ba ya kalle su,

 

Abban yace “Ina fata kaji komai ga me da yarinyar nan ? bansan ko kana da abun cewa ba” ya tambaya yana kallonsa

,kowa ya saurara don jin ta bakinsa, haroon Allah Allah yake akan Babban yaya karya amince da zamanta,

 

Boss man ɗin sai da ya gama sipping Coffee ɗin dake hannunsa a natse sannan yace” Umarninka Shine abun bi” amsar da ya bayar kenan, wani irin farin cikine yaci ka Abban nasu saboda shi da yake tunanin zai ƙiya gashi ya amince da duk jawabinsa kai tsaye ma yace Umarninsa shine abun bi, wato duk abunda yace game da yarinyar ya amince,

 

“Kufa kuna da Abin cewa”? Abban nasu ya tambaya yana kallom su, cikin sauri suka haɗa baki wurin cewa “Abba ae magana taƙare kawai tunda Babban yayan mu ya amince mu su wanene da baza mu amince ba”?

Wannan maganar tasu tasa Azmee yin ƴar dariya ƙasa ƙasa,

 

Jinjina kai Abban su yayi sannan yace “hakan yayi mun, sannan ko da gigin wasa ban amince wani ya cutar mun da ƴa ta ba,”

 

“An gama magana Abba” suka bashi amsa atare yace “Yawwa haka nake son ji, sannan ya mayar da idonsa kan Sehrish wadda ke faman sakin murmushi tayi zuru tana cizar akaifar hannunta da takai bakinta, ba kowa take tunani ba face Haroon yadda zata Zazzaga mashi rashin mutunci, dama taci alwashin hakan

 

Muryar Abban su ce ta katse mata tunanin nata da cewa ” daughter ki zauna kiyi breakfast tare da Abban ki da kuma ƴan uwanki,” ɗan zaro ido sehrish tayi jin yace zata zauna taci abinci acikinsu cikin mamaki tace “Abba

anan,” tayi maganar tana nuna dining table ɗinsu,

 

“Eh nan nake nufi” ya bata amsa sannan ya ruƙo hannunta gavan ta na faɗuwa suka samu wuri suka zauna tana gefen Junaid Abbansu kuma na gefenta sun sa ta tsakiya, Babban yayansu kuma Na a side ɗin Abban nasu, ta hannun dama yayin da suke facing Ayaan Jahaan da kanal yusif su da suke hannun haggunsu,

 

“Azmee ke ma ki samu wuri ki zauna A cikin mu,” abban su ya faɗi yana kallonta ,

 

da fara’a a fuskarta tace “ngde ssae Abba, amma ni nafison a barni a iya matsayi na, nafi jin daɗin kasancewata haka, dama damuwa ta Sehrish ce gashi kuma ta samu Ƴanci ka ƴanta ta, Allah ne kaɗai zai iya saka maka, haƙiƙa kai na musamman ne ka kasance ɗaya daga cikin mutanen da ake Alfahari dasu aduniya kuma ake alfahari da Ƴa’ƴansu kowa burinsa yayi koyi da kyawawan ɗabi’unka da halayanka Abba ba abunda zamu ce sai dai Allah yaci gaba da tsare mana kai, ya tsare zuri’arka, Ya kare ka daga sharrin mahassada da maƙiyan ka, Allah yaci gaba da ɗaukaka darajarka da ta ƴa’ƴanka a faɗin duniya, kamar yadda kake faranta ma wasu Kaima Allah ya faranta maka aranar gobe ƙiyama yasa Aljanna tazama makomarka…………….azmee bata tsaya ba haka taci gaba da yiwa Abbansu addu’oi’ dasu kansu , gaba ɗaya sunji daɗin addu’o’inta kuma dukkansu suke amsa mata da Ameen ameen,

 

daga bisa ni kowa ya mayar da hankalinsa ga abincin dake agabansa zanso kuka sehrish duk ta gaza samun natsuwa ba wai don bata jin daɗin kasancewarta atare dasu ba, sai don tsoran su ayaan da jahan da take yi, saboda wani irin kallo da suke mata Sam tagaza gane kallon menene wannan, dama fa su ƴa’ƴan Alexandra wuyar sha’ani ke gare su kamar uwarsu haka suke basu cika yarda da mutane ba ko kuma sake musu, junaid ne kawai mai sauƙin kai saboda kaf halayansa shigen na Abbansu ne,

 

shin wai ina haroon ? Ae tuni ya koma cikin bedroom ɗinsa cikin tsananin ƙunci ransa yayi mugun 6aci sai faman yawo yake a ɗakinsa cike da jin baƙin ciki aransa sai faman huci yake bakowa yafi bashi haushi ba face Abbansu da Babban yayansu saboda sune suka nuna Amincewarsu da ita, a can ƙasan zuciyarshi kuma bakowa yafi ƙuntata masa ba fa ce*JUNAID* Saboda shine silar komai daya fara sanar da Abbansu akan maganar yarinyar, dama junaid ya jima yana ci masa tuwo a ƙwarya don ya lura Yaron Abbansu yafi Son shi fiye da kowa tunda har bai iya 6oye son da yake mashi agaban kowa, Kuma ya Lura cewa Babban yayansu ya mutu akansa hakan na nufin shima Yafi Son*JUNAID* bama su kaɗai ba kowa na gidan in kana so kaga fusatar shi to ka ta6a junaid nan xaka ga tashin hankali, shiru yayi a lokacin ya koma gaban mirror ɗinsa yana kallon fuskar shi ta cikin madubi, a fili yace “saboda*Junaid* Abba da Babban yaya suka mare Ni, a gaban ƙanne na, mutun Uku da suka kasance maƙiya na acikin gidan nan muddin inaso In ƙuntata musu dole saina Cutar da *JUNAID* 😳

 

ya faɗi tare da sakin wani irin shu’umin murmushi yace “Haroon kenan Mai Fuska biyu ! Wasu suna mun kallon shashasha ɗan giya yayin da ni kuma nake masu kallon garori wannan Alwashi ne na ɗaukarwa kaina saina Tarwatsa farin cikin gidan nan kuma ba da kowa zanyi amfani ba fa ce *JUNAID* 👌💔

 

“na’am ” ya amsa yana Satar kallom sehrish da ta kira sunan shi ta wutsiyar idon shi, “nifa tsoro nake ji junaid nagaza cin abincin dake gaba ba,” murmushi junaid yasa ki tare da cewa “CALM DOWN your mind reesh, ke fa ynx ƴar gida ce, ki saki jikinki ki ci Abincin ki a natse,” murmushi tasaki yayin da ta sa hannu cikin plate ɗin dake gabanta mai ɗauke da fried chicken taci gaba da ci, ta6e baki Jahaan yayi yana kallonta aransa yace ” ƴar shisshigi da kutsu bansan daga ina aka samo wannan yarinyar ba yanzu haka bata Wuce Zariyya dama gata nan kamar Zararrriya sai faman zare ido take,’ ya yi maganar yana Hura hanci kamar wanda akayiwa dole yana Cusa bugger abakinsa, Ayaan kuwa cewa yake yi aransa “ƙarfin hali irin na Ifritanyar nan kalli yadda ta wani shige tsakanin Abban mu da junaid tana cin abinci ita ga isasshiya mai walkin sa, ala dole ga ƙanwar Sojoji zaki gane kurenki ! Jibi kunnuwanta don Allah kamar na Zomo falo falo sai faman ƴan ƙefce ƙefcen ido take kamar wadda aka aza A saman kujerar lantarki……,😂

 

Har cikim ranta sehrish duk ta tsargu da su Twins kamar tasan abunda suke cewa aransu, Azmee ce keyi mata alamar ta kwantar da hankalinta don itama ta lura da abunda su twins ke mata, wani irin Kallon hadarin Kaji 😾😼

 

Tuni sgr ya bar dining ɗin dama breakfast ɗinsa shaf shaf yake yinsa gyaran murya Abbansu yayi ya kalli azmee yana cewa “idan mun kammala ku shirya ke da sehrish da Junaid saboda yi wa daughter siyayyar kayan sawa da abubuwan amfani na mata, hada ma Saloon da gyaran jiki duka komai nake so ayi mata,’

 

Atare Jahan da Ayaan suka ɗago suna kallon Abban nasu, shima kanal yusif abun ya basa mamaki, Sehrish kuwa murmushi kawai take saki haka Junaid daɗi kamar ya rufe sa,

 

Azmeee tace “To Abba Insha Allah komai za’ayi mata,”

 

“Ke ma hada ke, azmee siyayyar duk zakuyi,” cike da farin ciki azmee tace “Mun gode sosai Abba Allah yasa ka da alkairi,”

 

mayar da idonsa Abban nasu yayi kansu Ayaan da jahan da kanal yusif yace “Bafa ni zan biya kuɗin siyayyar ƙanwarta ku ba, wannan nauyin ku ne, don haka kowa ya tattaro ya bada gudummuwa,

 

babu wasa a fuskar shi yayi maganar, shiru su kayi don baza suyi mashi musu ba, Abban nasu yaci gaba da cewa “Yusuf kai zaka biya kuɗin siyayyar kayan sawanta, Jahan kuma shi zai ɗauki nauyin kayan ado na mata da za’a siya mata, sannan Ayaan shi kuma zai ɗauki nauyin na gyaran jiki hada takalma da bags ɗin da za’a siya mata ina fata duk kunji,” sam takaici ya hana twins yin magana bawai kuɗin bane damuwarsu ba sam basu da matsalar kuɗi saboda bada albashinsu suka dogara ba, Mahaifiyarsu duk ƙarshen wata tana tura masu makudan kuɗi dollars wannan ba tare da sanin Abbansu ba ko Babban yayansu ba, haushin su yarinyar da aka ƙaƙaba musu wadda basu san daga ina aka tsinto ta ba, gashi kuma har ana ɗaura musu responsibilities ɗinta,

 

“Naji kunyi shiru”? Abbansu ya tambaya yana kallo su,

 

Kanal yusif yace “Atm ɗin yana a cikin side drawer ɗina, junaid yaje ya ɗauko in zasu tafi,”

 

Jinjina kai Abbansu yayi tare da cewa “Haka nake son ji ku fa”?

 

har suna haɗa baki wurin cewa “akwai kuɗi cash a ɗakin mu junaid yaje ya ɗibi yarda zai ishe su,in kuma Atm suke so shima yana anan saman mirror muka barshi….” suna magana suna yatsina fuska irin an musu dolen nan,

 

Kanal yusif yace “A’a Abba ba sai sun bada nasu ba, kawai suyi using da Atm ɗina zasu ishe su har ma su rage,” acewar kanal yusif,

 

Abban su yace “a’a ni nafison su sauke nauyin dake akansu na ƙanwarsu yakamata tun yanzu su son yadda zasu ɗauki ɗawainiyar mace kafin Allah yasa lokacin auransu yazo,”

 

. atare suka haɗa baki wurin cewa”Aure kuma Abba,”

 

“Eh mana” ya amsa musu,

 

Kallon Ayaan jahan yayi tare da cewa “tashi mu tafi lokacin aiki yayi ” miƙewa Ayaan yayi yana cirar tissue yace “Abba mu mun wuce,”

 

Murmushi Abbansu ya saki tare da cewa “adawo lafiya, aure dae ba fashi in lokacinsa yayi mutun ko bai so saina ɗaura masa in yaso ya haɗiyi zuciya ya mutu, zan zauna in ta zuba muku ido ne,”

 

fashewa da dariya junaid yayi bashi kadae bama hada su azmee da sehrish, kanal yusif dae murmushi kawai yayi,

 

Na wani lokaci kowa yabar dining ɗin cikin zumuɗi sehrish ta wuce don ta shirya zasu tafi Shopping mall ɗoki har ba’ayi, shima junaid bedroom ɗinsa ya wuce don ya kimtsa yau zasu yi fita ta musamman da sehrish don ya tsara har ice cream sai sunje sha, haka itama azmee kimtsawar take yi don su fice,

 

Haroon sam yagaza fitowa saboda kunyar haɗuwarsa da sehrish baisan martanin da zata yi mashi ba, dama jiya ta yarda masa magana a cikin toilet ina ga yau da tasamu ƴanci Allah kaɗai yasan Zagin da zaisha, ga yunwa yana ji amma sai faman zarya yake aransa yana faɗin “Ke ma bazan ƙyale ki ba Yarinya saina ƙasƙantar dake kuma bazan fasa abunda nayi niyya ba akan Ki,*YANZU WASAN YA FARA* 🙆

 

Fitowa azmee tayi jikinta na sanye da doguwar riga ta atampha ta kashe ɗaurin kallabi, sai ƙamshi take cikin hanzari ta wuce kitchen saboda tunawa da Marshal Omar wanda bai fito yin breakfast ba kuma ba’a kai masa ba, shaf shaf ta shirya masa a tray ta wuce part ɗinsa ta shiga da Sallama babu kowa a falonsa hakan na nufin koma bacci bai tashi ba, ajiye masa tayi asaman ƙayataccen table ɗinsa sannan ta fuce,

 

Tana saukowa down stairs taci karo da haroon wanda ke tafiya cikin sanɗa zai shige kitchen wai don karya ci karo da Sehrish

 

girgiza kai azmee tayi aranta tace “Shi ko haroon ko lafiya yake faman tafiya cikin sanɗa haka kamar mara gaskiya, Ni wlh nama manta dashi ashe yana nan,’

 

Gyaran murya tayi tare da cewa “barka da fitowa mlm haroon,” firgit yayi tare da juyowa ya kalle ta, ajiyar zuciya yasaki ganin azmee ce “Aunty azmee barka dae fatan an tashi lafiya, shine aka manta dani ina ta fama da yunwa yanzu da ban fito ba da shikenan sai dae yunwa ta kashe ni ko? Ya tambaya hada ruƙe qugu dama ransa a 6ace yake………

 

Azmee tace “Kayi haƙuri wlh ni sam na manta ban lura da baka fito ba ba,”

 

ta6e baki yayi tare da cewa “koda yake dama ae ni ba’a sona na lura, bama kallon mutun ake mun ba acikin gidan nan kowa ya raina ni,”

 

Murmushi azmee tasaki tana kallonsa tace “kadaina cewa haka bana jin daɗi, koda kowa zai guje ka amma kasan ina tare da kai ko? Ka ta6a ganin inda UWA ta Guji ƊANTA?” tayi maganar ne don ta kwantar masa da hankali ganin ya ɗan fusata,

 

Sakin fuska haroon yayi sannan yace “Shikenan nadaina aunty azmee tunda baki so, yanzu dai a haɗa mun breakfast ɗina wlh yunwa nake ji har wani jiri nake gani,

 

Wuce sa azmee tayi tana cewa “a ina za’a kaima abincin anan ko a ɗakin ka,” cikin sauri yace “Ki haɗamun kawai natafi da abuna ɗakina naci,Zai fiye mun kwanciyar hankali na”

 

Kitchen ɗin tashiga ta haɗa masa a tray sannan ta miƙa masa jikinsa na rawa ya kar6a ya wuce ɗakinsa,

 

Gefen gadonsa ya zuna hannunsa har kerma yake yi yana cusa abincin abakinsa, kamar daga sama yaga sehrish ta bayyana agabansa jikinta sanye da Kayan Sadaukai na Yaƙi, hannunta ruƙe da Zungureriyar wuƙa kanta na ɗauke da Kambun Sarauta, hankali atashe haroon ya fesar da donuts ɗin daya cunkusa abakinsa yana kallonta cike da tashin hankali, fashewa da dariya sehrish tayi tare da cewa “Kai Haroon! Ƙaryarka taƙare ! ka jima kana ƙuntatamun gashi yanzu Allah ya ɗaukakani, babu wata sauran barazana daga gare ka ta ƙare, nazo ne don na ɗauki fansa akan ka, yanzun nan zan fille kanka da wannan wuƙar ta hannu na,

 

Da ƙarfi sehrish ta ɗaga wuƙar zata fille ma haroon kai, aikuwa a firgice ya miƙe tsaye yana dafe saitin zuciyarshi a tsorace

 

Lokaci guda Sehrish ta 6ace masa 6aaat hakan na nufin ba ita bace idonsa ne ke masa gizau,amma shi tabbas ita yagani kodai yarinyar Aljana ce ? Ya tambayi kansa,.wannan ba kowa bace face Hafsat Bature Aljanar sehrish 👿

 

Koma wa yayi ya zauna yana ci gaba da cin breakfast ɗinsa anatse, yayin da ransa ke saƙa mashi abubuwa da dama game da mummunan ƙudirinsa

 

__________ 💪 ______________

 

OMAR a hankali ya soma buɗe idanunsa bakinsa na ambaton addu’ar tashi daga bacci, yayin da zuciyarsa ke cike fal da son ganin Tagwayensa, tun da asuba daya sha maganin mura bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi sai yanzu Allah yayi mashi ikon Farkawa daga bacci, a hankali yasa hannun sa ya janye blanket ɗin daya lullu6a dashi jikinsa na sanye da Night dress riga ce dai dai guiwa mara nauyi, fararen idanuwansa yafara kaiwa ya kalli agogon dake manne jikin bango ƙarfe 12 na safe yayi mamakin yadda lokaci ke gudu har haka, ko don yayi overdose na maganin muran daya sha ne yasa shi yin dogon bacci har haka,

 

Cikin sauri ya yunƙura ya miƙe direct toilet ya wuce , brush yafara yi yana tsaye agaban wash basin amma idonsa Fuskar Jahad da Hosana take hasko masa ta cikin mirro ɗin gabansa, shaf shaf yayo wanka ya fito jikinsa sanye da Bathrobe(rigar wanka) fara, wadda ta tsaya masa adai-dai guiwarsa, Marshal Omar kenan Son kowa ƙin wadda tarasa 😉

 

kai tsaye wuce wa yayi ya ɗauki wayarsa dake a saman gadonsa, sak irin ta sgr ce, Company ɗaya ce waya ce ta musamman domin Manyan jami’an sojoji irinsu kirar Companyn Iphone Ce, hamshaƙiyar waya haɗaɗɗiyar gaske wadda kuɗinta sun haura 30millions, ba kuɗinta bane abun mamaki ba a’a amfaninta shine abun dubawa, ƴar bala’en wayace bakowa ma zai iya Controlling ɗinta ba sai mamallakinta.

 

dannata ya soma yi Contact ɗinsa ya shiga kai tsaye numbar aunty BABBA ya laluba, ya buga mata Calling ta shiga ringing, burinsa tayi picking yasanar da ita cewa Zai shigo kaduna don ya duba su Hosana da Jahad, almost 3 times ba’a ɗaga kiran ba, domin kuwa wayar tabar ta agida, canza ra’ayi yayi ya dannawa Wayar Hafsat kira,

 

Suna a asibitin nan zaune saman waiting seats, bacci duk ya kwashe su daga zaune don daren jiya ba wanda ya runtsa sai da sassafe wurin ƙarfe 10 suka samu baccin wahala shima saboda likita yasanar dasu cewa Yarinyar da ranta bata mutu ba, farkawa ne kawai batayi ba doguwar suma tayi, shine suka ɗan samu natsuwa suka baje suna bacci kamar wasu shanaye ga uwar yunwa na cinsu, kiran Omar ne yashigo da ƙarfin gaske a wayr hafsat dake acikin purse ɗinta data aza saman cinyarta, a firgice suka farka su duka wuri wuri da ido, cikin hanzari hafsat ta zura hannunta cikin purse ɗinta ta duba me kira sunan MARSHAL OMAR ne ya bayyana, dafe ƙirjin tayi hankali atashe tace “MUNSHI GA UKU ! MOMMY YA OMAR NE KE KIRA”😳

 

 

 

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

 

Kar amanta da paymemt wanda suka shirya sumin magana 08103884440, 300 ne VIP kuma 700 ga wanda basa ra’ayi a grp

 

Related Articles

Matar Makaho Part 12 Complete Hausa Novel

22, April 2023

Labarina Season 5 Episode 5

22, April 2023

Sanda Episode 1 Season 2 || with English Subtitles

22, April 2023

Ban saketa ba Complete Document

22, April 2023

Yan Sanda sun kama maharan da suka kashe masallata a jihar Nijer

22, April 2023

Yaro Ne Page 21-30 Hausa Novel Complete

22, April 2023

Follow us

Facebook

Twitter

WhatsApp

Google news

You might like

UNCLE DATTI JIKINA YAKE SO PART 2 Hausa Novel Document

22, April 2023

Illolin Da Yawan Shan Ruwa Mai Sanyi Yake Yi Ga Lafiyar Jikin Dan Adam.

22, April 2023

Wace Ce Ita Chapter 17 Complete Novel

22, April 2023

Hattara: Kada Ka/Ki Karanta Idan Baka/Ki Da Aure – Yadda Zaki Gamsar Da Mijinki

22, April 2023

 

NIHAAD Chapter 11 By Khaleesat Haiydar

18, July 2023

Search for:

Search …

Abban Sojoji Complete Census Education Free browsing Hausa Novel Hausa Novels Hot Romantic Hausa Novel Idan ba ke Kannywood Maganin sanyi Mtn Scholarship Sirrin rike miji Tusar gaba Wace ce ita warin gaba warin kashi Zafafa 2023

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button