Hausa Novels and Stories

Alkawarin Zuciya Complete Hausa Novel

Sponsored links

 

1️⃣

 

~UK~

 

  1. Tundaga nesa take leke babban building din datake dumfara tana bin uban tulin cars din wajen da kallo kaman akwai abinda take nema kafin daga bisani idanuwanta su sauka kan wata white Bentley car, gashinan kar kar ko alamun a single dust babu ajikin motan, ajiyan zuciya tasauke ahankali murya chan kasa tace “Alhamdulillah he’s still around” sanan tashiga sauri takarasa gaban wajen da ake kira da Cozy, harzata saka hannu tabude kofan tashiga tadanyi jim tsaya kafin ahankali tabi jikin ta da kallo tana sanye dawani white jeans daya kamata tsam dawata yar dark blue top mai shegen kyau wacce da kadan tasauka daga kan cibiyanta, saidan gyalen data yana kanta white shima dayamata kyau sai gashin kanshi dakenan kusan rabi awaje anmata kalaba da attachment kanana dayamata kyau shima, hannunta rikeda wasu books guda biyu dakuma phone nata kirar iPhone 13, sai wata yar karaman jakan datake rataye da ita, ajiyan zuciya takara saukewa kana ganinta kasan she’s nervous sanan ahankali tasa hannu tabude kofan wajen tashiga ciki.

Hadaden eatery ne and bar mai shegen kyau, babu wasu mutane dayawa awajen wayanda suke wajen yawancinsu turawa ne fararen fata maaikatan wajenma fararen fatane hakan yasa zaka gane wajen na bature ne, ahankali take tafiya tanabin wajen gabaki daya da kallo da gefen idanunta, kafin takarasa gaban kanta taja kujeran wajen ta zauna sanan tasauke books dinta agabanta da wayanta, daidai baturen Bar attendant din yakaraso yana kallonta yace “what can I get you miss” dan waigawa tayi kaman tana neman abu awurin tace “Pierre Zēro Rosé please, two shot” ganin duk tana maganan ne batare datama kalleshi ba yasa yace “gotcha” sanan yajuya yakoma yadauko wine din datai order yazuba mata a cups guda biyu sanan yadawo gabanta ya ijiye yace “here we go” dan juyowa tayi da sauri takallai sanan tasauke jakanta da sauri tadauko kudi taba shi tace “keep the change” kafin ma yay magana tasake juyarda kanta tana bin mutanen wajen da kallo one after d other…..

“Kai Zayn look” wani hadadden chocolate guy daga tachan karshen babban falon wajen da aka cikada kujeru ne kowa na zaune yana abinda yake yataba wani kyakkywan thick farin guy dake zaune kan kujera ya lumshe idanu pipe din shisha na bakinshi yana zuka yana fitarda hayakin ta hanci, yana sanye da riga da wando both black na LV, farine shi kal yanada cikan jiki dayake rigan dayasa short sleeve ne hakan yafito da kakkauran murdadden hannunshi, irin guys dinan ne masu manyan gabobi dakuma murdadden jiki, dudda idanunshi a lunshe but idan ka kalleshi bazaka so kadauke idanunka ba dan yanada wani irin kyau kaman mace, lips dinshi sunyi wani kalan masifan ja kodan shishan dayake shane oho, yanada dogon hanci siriri dayazauna akan fuskanshi gwanin ban sha’awa, sai gashin giranshi baki sidik kuma acike yanada tabon salla agoshi sai gashin kanshi baki sidik shima dake kyalli sun nannade kaman na buzu sanan gawani kwantaccen saje a fuskanshi Masha Allah, koda ace shiyay kanshi bazaiyi kanshi da wanan kyau dinba ballema bashi yayba.

Ganin baida niyyan amsashi yasa Mamu ya fizge pipe din shisha dake bakinshi yace “kafara ko ina maka magana kamin banza” ahankali yabude idanunshi dasuka wani lumshe sukai yaushi da idanda zai kalli mace dasu sai lissafinta yarikice sanan yazubasu kan Mamu kaman ance yay magana dan dole yace “what”? Dan murmushi Mamu yayi da hannu yamai alamu yace “look over to the counter ga budurwanka chan, stalker dinka tazo sai kallon ka take wlh, haba Zayn kaiko bazakaji tsoron Allah ka kula yarinyar nan koda sau daya bane tunda dai ta kasa maka magana for morethan 2months yarinyar nan kullum binka take tana stalking naka tana kallonka u know she really really likes u waikai maisa kacika wulakanta mata ne eh? Anyway I don’t blame you ni wlh in mace ne banmaga abin so ajikinka ba mutum dukgaka nan kalan asibiti farin fata kalan cuta, duk baku da karfi” dan murmushi yayi dan yasan Mamu so kawai yake yajashi suyita surutu this afternoon shikuma baida time dinan, hannunshi yamikamai alamun yabashi shishi shi, ijiye pipe din shishan Mamu yayi kan table din gabansu yace “Ya isheka hakanan gashinan duk idanunka sun chanza launi, munada lectures yanzun nan fa I think in the next 5min” dan tsaki yaja yasa hannu yadauki pipe din shisha yacigaba dasha abinshi yana daddanna wayanshi yana hura hayakin ta hancinshi batare dayama daga kai ya kalli inda Mamu yacemai yarinyar nan takeba Mamu nabinshi da kallo yarasa yanda zaiyi yaraba Zayn da shisha, shima bawai bayasha bane no but occasionally yakesha, shiko Zayn zai iya wuni yanashan shisha hakanma yasa baya iyacin abinci sosai, ganin yasake lumshe idanu yasa Mamu yaja tsaki yamike tsaye yace “dalla Malam wuce mutafi” bude idanunshi yayi dasuka dan kankance sukaija sanan ya watsama Mamu harara kafin ahankali ya ijiye pipe din yamike tsaye dogon namiji ne nagaske, budadde sanan kuma cikakke irin mazan nanne da ake kira da burin mata, car key dake kan table din yadauka yana rikeda wayanshi yay gaba abinshi batare daya cema Mamu komi ba yay hanyar kanta.

Murmushi Bartender din yayi inda sabo yasaba yasan yanda yarinyar nan ke crushing on that guy like hell, not just her da many other ladies ma, sabida guy dinan cinikin dasukeyi yanzu a eatery dinan is mind blowing, dazaran ansan yana ciki yammata zasu fara tururuwa suna shigowa from no where so koshima he’s happy for her at least yau yakulata, he hope suyi relationship dudda guy din dumping yammata yake anyhow kaman trash kuma ko ajikinshi dan yasan yanda suke binshi, he just hopes wanan will not be one of his victims, dan yana using babes kaman yanda yake using pen na rubutu idan yagaji da wanan ya yar yadauki sabo.

Tadade awajen ita kadai sai murmushi take tana daddaura handkerchief din akan fuskanta tanajin dadi daga bisani wayanta yashiga kara, dasauri ta kalli wayan ganin Juliana Munari ke kiranta yasa dasauri tadauka tana murmushi sosai tace “Hi Babe ya” daga tachan bangaren wata yarinya tace “ina apartment dinki amman bakinan Ayshu where are you? Ba tundazu muka gama lectures ba” murmushi tayi sosai tace “ina Cozy” dan jim Jully tayi tace “for Godsake Aisha when will u get sense? Eh, look at the way Kabeer ke binki Ayshu yaron nan loves you like a mad man amman kina nan kina stalking wanan heartbreaker da the worst part baimasan kina existing ba” dasauri Aysha tai fari da ido tace “says who, wayace miki baisan ina existing ba? Wlh yasani infect right now ma yanzu haka handkerchief dinshi nake kallo a hannuna it feels warm and smells succulent, OMG it smells just like him wlh, I feel kaman Zayn dina ne anan wajen” shiru Jully tayi saikuma chan tace “Ayshu I am ur friend and I will always tell you the truth,

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button