Hausa Novels and Stories

Zafin Kai 7

Sponsored links

Wani babban tashin hankali mafi tsoratarwa da Benazir ta shiga bayan wasu shekaru shine fara lura da sumayyah data fara samun ciwon qwaqwalwa kaman Annensu sbd

 

lokuta da dama haka zata zauna tayi shiru ta qurawa guri daya ido tana magana a hankali kokuma ta ringa kuka a hankali tana kiran sunan Ababa dana samirah sbd Safnah haka kawai Allah ya cire musu ita cikin ransu sbd abinda tayi din kafin guduwarta wanda kuma guduwar naya ya sake tsanananta musu komai daga gurin Ababa din.

Azabar dasuke ciki da qunci yayi nasarar taba qwaqwalwanta kaman mahaifiyarsu,

Wace qaddara mai girma ce wannan ta hau kanta?

Tayaya zataji da wannan masifar?

Ya zatayi da sumayyah din?

Tayaya zata ringa boye wannan lamarin?sbd komai tsananin tsanani bazata iya bari Ababa ko hande su san da wannan sabuwar qaddarar ba sbd Ababa komai zai iya aikatawa akanta sbd ganin itama tamkar wata asarar ce zaiyi na dukiyar daya kashe akanta.

Zubewa tayi tsakiyar dakinsu ta fashe wani irin kuka mara sauti dayake yankan kirjinta sbd tausayin kanta danasu sumayyah da Annen,

Inama itama zata haukace gabaki daya ta yanda zata dena jin radadi da kuncin dayake ranta ta manta komai.

Sumayyah dake zaune shiru tana magana ita daya a hankali ganin benazir din a hakan yasata tasowa ta dawo gurinta tana rungumota muryarta a hankali ba kuzari tace

“Benazir kuka kikeyi nima na fara samun matsala ko?

Karki damu nima mutuwa zanyi idan na mutu komai zaizo miki da sauki zaki iya samun damar dauke Anne ku tafiyarku ko bara kuyi zakuji dadi a gaba insha Allah…

 

Girgiza kai Benazir tafara hawayenta na tsananta gudu bata iya cewa komai sbd matukar Sumayyah ko Anne a yanzu ta sake rasa daya itama nata lokacin na zaucewa tayi.

Hawaye ne suka gangarowa Sumayyah ta sake rungume Benazir din jikinta cikin rauni da mutuwar jiki tareda sarewa tace”

Benazir nima banason na haukace ko na mutu amma da alama kaddarata ta haukacewan kafin mutuwar a kusa take,

Kuka mai sauti Benazir ta kasa riqewa ta fashe dashi tana cusa kanta cikin tafin hannuwanta dukkanin zuciyarta na karyewa dan Allah ya sani a jininta da tsokan zuciyanta take jin Sumayyah,

Itace qanwa sumayyah din ce yayarta amma a gareta kaman sumayyah din ce qanwa sbd jin takeyi alhakin kulawa dasu a ynzu duka a kanta yake.

Ita kanta sumayyah kukan mai sauti ta sake tana yin qasa da kanta sbd sanin lalura zasu zamarwa Benazir itada Anne dan haka har cikin ranta take rokon Allah idan zata zamewa Benazir ‘dinta da Annensu kaddara mai wahala da nauyi Allah ya dauki ranta ta huta.

Kaman Benazir tasan adduar da Sumayyah din keyi ta dago jajayen idanuwanta ta kalli Sumayyah kafin ta kalli Annensu dake gefe tana kallonsu cikin tsananin kukan da itama take rokon Allah ya dauki ranta idan har ‘yayanta zasu samu ‘yancin guduwa daga ukubar mahaifinsu su samu kyakkyaqar rayuwa a waje.

Insha Allah zamu rayu a tare mu sauyi a tare

Idanma mutuwar itace hutu garemu duka Allah ya kawo mata ita gabaki daya mu tafi garesa mu huta.

Sunkuyar da kai sumayyah tayi tanajin kaman itace kaddarar Benazir a yanzu sbd halin datake neman sakata na dawainiya da ita.

Benazir ganin naz tashin hankalinta akan lalurar sumayyah din na neman qarasa taba qwaqwalwanta dan haka ta sakawa kanta juriya ta danne ta nuna mata ba komai bane babu abinda yake samunta lafiyanta kalau hakama qwaqwalwanta lafiyanta kalau.

Hakan yasa kaman yarinya qarama sumayyah din ta yarda ta sake suka koma rayuwar wahalarsu a tare harda Annensu sbd sun gano a yanzu hadin kansu da girman kaunar dasu kewa juna shine qarfinsu.

Wannan gargadin nasa kusan kullum yayi sa sai sunji hankalinsu ya tashi saidai daman babu wata niyar kula kowa a ransu bare dasuka tabbatarda maimaicin gargadinsa akan maganar na nufin komai mai muni zai iya faruwa idan makamancin hakan ta faru.

****wannan dalilin ne yasa suka kama kansu acikin dubban mutane fiyeda kowa a makaranta,

Sun fara zuwa makaranta tamkar mujiyoyi acikin mutane ahakan suke zuwa su dawo,

Basu taba qara mintina ko biyu ba da an tashi suke dawowa gida sbd aduk lokacin da suka saka qafa suka fita Azabar Annensu ke farawa dawowarsu da wuri shine samun saukin azabarta dan haka da an fito lectures basa bata lokaci da sauri suke dawowa.

Da haka Ababan ya riqe lokacin dawowarsu kan lokaci batareda magana ba idan sun dawo Annensu ta huta idan basu dawoba tana cikin wuya.

 

 

 

 

Da zasu fara karatu Hande yabawa kudi ta siyo musu atamfo masu saukin kudi kusan guda biyar biyar sai jallabiya masu saukin kudi suka kusan guda uku uku shikanan sai mayafai biyu da hijab biyu kowannensu sai takarma daddaya.

Ahaka suka fara karatun cikin taka tsantsan da tsoro da fargaba,

Babu wani mutum daya dasuke hulda dashi a makarantar kaman yanda basa yarda ko bada fuskan ayi hulda dasu.

Sumayyah fara shigarta cikin mutane sai yake kokarin bayyanarda matsalarta ta cikin qwaqwalwanta a fili sbd a duk lokacinda ta shiga mutane sai take jin kanta na juyawa,

Sam tunda suka fara karatun bata wani gane komai sam sbd mummunan sabon da Ababa yayi musu bata iya shiga mutane tafi son zaman gidan.

Benazir kuwa sosai ta maida hankali ta qwallafa rai a karatun sbd samun Abin tsira daga mahaifinsu da yardar Allah saidai kuma yanayin Sumayyah yafara hanata kwanciyar hankali a yanda ya kamata a karatun.

A duk lokacin suka fito suka zo makaranta hankalinta yakan rabu biyu ne akan sumayyah da karatun,

Tin tana boyewa cikin kama kai daga kowa har kusan anfara ankarewa da Sumayyah din na dan da tabin kai duk da ba laifi wani lokacin takan gane karatu harma da tambaya.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button