Hausa Novels and Stories

Abban Sojoji Chapter 28

Sponsored links

Ita kan ta Hafsat ba ƙaramin tashin hankali tashi ga ba ganin halin da yarinyar ta shiga, da alama ma raunukan nata sun ɗuri ruwa dole sai an fitar da ruwan Ya Salam, Yarfa hannu kawai take yi tana zabga uban kuka, hankali atashe JAHAD ta kalli hafsat tare da cewa “Aunty dan Allah ki taimaka mu mayar da ita asibiti aduba ta…..’ ta ƙare maganar tana faman zubda hawaye,

 

Ita kanta hafsat tunanin da take yi kenan can ne kawai mafi ta, ta shi tayi jiki na rawa ta ɗauko hijab ta zura sannan ta ɗauki mukullin motarta da ta bari a saman mirror,

 

da kanta ta cuccu6i hosana daker ta ɗauko ta a kafaɗarta, ta fuce da ita cikin sauri itama jahad tabi bayanta a babban falon suka samu aunty babba saman Sofa hannunta ɗauke da plate ta dafa taliya sai faman ci take a tsiya ce saboda yunwar da ta taso ta, duk ihun da hosana take yi a kunnanta amma batayi yunƙurin tashi ba, balle taje ta dubo meke faruwa,

Ganinsu afujajen yasa ta miƙewa tana cewa “Hafsat ina zuwa cikin daren nan? Ina zaki kai ta?

 

Batare da hafsat ta kalle ta ba tace “Zan mayar da ita asibiti ne,” hankali atashe aunty babba tace “Saboda me !! Acikin daren nan ! Ki barta kawai inyaso gobe dr yazo ya duba ta har gida,”

 

tsoki hafsat taja dama a ƙule take da Mommyn nata saboda duk ita taja mata halin da suke ciki,.

 

Wuce ta tayi tana cewa “da yake ba jikin ki bane ae dole ki ce haka,’

Bin su kawai aunty babba tayi da kallo har suka fuce, abayan mota hafsat ta kwantar da hosana, sannan suka shiga gaba ita da jahad, taja motar da gudu ta fuce da ita a wani privet hospital takai ta, cikin sa’a suka karbi hosana kuma nan take suka shiga bata taimakon gaggawa,

 

Yayin da hafsat da jahad suka samu wuri suka zauna nan waje suna jira saman waiting chairs, runtse ido kawai jahad ke yi tana faman karanto addu’a, tsigar jikinta har tashi take yi saboda jin yarda ihun hosana ya cika asibitin gaba ɗaya baiwar Allah, ita kaɗai tasan azabar da take sha,

 

Ita kanta hafsat dake gefenta jikinta duk ya gama mutuwa haƙiƙa taji tausayin Yarinyar fiye da tunanin mai tunani,

Jim kaɗan suka ji tsit babu kukan hosana babu alamar shi, jin hakan yasa jahad yin zumbur ta miƙe ta tunkari ƙopan ɗakin da suka kwantar da ita, tsoranta kar ace hosana ta mutu ne shiyasa suka ji shiru,

 

turo ƙopar Nurse tayi ta fito cikin sauri jahad ta tare ta tana cewa”dan Allah sister ya jikin nata yake? ta tambaya a ɗan ruɗe

 

Nurse ɗin tace “Alhamdulillah, kada ki sa damuwa aranki, jikinta da sauƙi sosae anyi mata dressing na raunukan nata sannan Mun taimaka mata da pain relievers yanzu haka allurar bacci mu kayi mata, addu’a kawai zaku ci gaba da yi mata,’ tana faɗin hakan ta wuce gaba,

Ajiyar zuciya jahad tasaki har hankalin ta ya kwanta sosai, komawa tayi ta zauna gefen hafsat wadda ke ta faman yin gyangyaɗin bacci,

 

Rufe idonta kawai tayi tana faman ci gaba da yiwa hosana addu’a, bata jin zata iya runtsawa a daren nan,

 

tsawon awanni suna anan jugum time ɗin hafsat ta jima da yin nisa a baccin ta, jahad kuwa na nan ido buɗe, kamar daga sama taji hosana na kiran sunan ta ƙasa ƙasa da farko tayi tunanin gizau muryarta keyi mata amma daga baya ta tabbatar da cewa ita ɗin ce ke kiranta,

 

Cikin hanzari ta miƙe ta shiga ɗakin samun ta tayi ta tashi zaune saman gadon, ba ƙaramin farin ciki bane ya cika jahad, ganin yadda fuskar hosana ta sa6e an mate

mata ruwan anyi dressing ɗin wurin ga bandage nan a forehead ɗinta da saman hancinta, duk da fuskar ta canza sosai kamar ba ita ba,  idanuwanta sun buɗe sosai tana ganin jahad takama Murmurshi 😥

 

Faɗawa saman gadon jahad tayi ta rungumo ta sosai ajikinta tana faɗin “Allah sarki hosana ashe kin farka ban sani ba kina ta kiran suna na, ya jikin naki? Akwai inda ke miki ciwo yanzu”?   Tayi tambayar tana janye jikinta daga na hosanar,

Daker ta iya cewa “Naji sauƙi sosai jahad ba inda ke mun ciwo yanzu, amma magana tana mun wahala,Kuma ina jin jikina kamar ba nawa ba”

hannu jahad tasa tana shafa gefen fuskarta tace “Insha Alah zaki dawo dai-dai hosana, yanzu hankali na ya kwanta tun da naga kina murmushi nasan cewa sauƙi ya samu

Jahad tace “muyi mashi Uziri hosana, ni nasan cewa yana sane damu kuma zaizo nan very soon,’

 

Sun jima suna yin fira atsakanin su, ita kanta jahad tasan cewa hosana juriya kawai take yi tana yin surutu, daker tasamu hosana ta koma ta kwanta, itama a gefenta ta ra6a ta kwanta, lokaci guda bacci ya kwashe su su duka,

 

Ba ƙaramin bacci suka sha ba, don kuwa har sai da gari ya waye rana ta fito sannan jahad tafarka, hosana kuwa nata faman sharar baccin ta, ganin yadda hosana ke bacci anatse ya ƙara tabbatarwa da jahad cewa tasamu sauƙi sosai, tashi tayi ta cire hijab ɗin dake jikinta, ta shige toilet ɗin dakin Alwala tayi sannan ta fito ta ɗauki hajiabin ta zura, tana faman tunanin in da zata samu tayi sallah don babu carpet

Fitowa tayi don ta duba hafsat samu tayi bata anan inda tabar ta jiya babu ita ba alamarta a wurin, sai taji hankalin ta ya ɗan tashi tsoranta kar ace guduwa tayi tabarsu a asibitin,

 

Hankali atashe ta fito harabar asibitin ga mutane nan nata wuce wa wasu na shigowa wasu na fuce wa, sai faman waige waige take yi tana neman hafsat, har wurin ajiye motoci taje taga ko zata ga motarta amma babu ita, hakan na nufin tabar asibitin kenan, da alama ma tun asubahi tabar asibitin, tuni jikin JAHAD yayi mugun sanyi,

 

Koma wa tayi tasamu wurin inda taga wasu mata zazzaune suna fira, tayi musu sallama suka amsa mata da fara’a

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button