Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 38

Sponsored links

Bai kulata ba ya ida ajiyeta a ruwan dake ta faman tashin ƙamshi na masifa, ga wani ɗumi mai ratsa ƙashi da ɓargo. Fuska a ƙwaɓe take duban kanta da yanda ya sakata ita da kayan gaba ɗaya cikin ruwan. Sai taji kamarma ta saki kuka kawai ta huta. Wannan wane irin kalar walaƙanci ne. Idan yace mata taje tai wanka kawai ai ya wadatar, amma yanzu gashi ya jiƙa mata kaya duka al’halin bata da yaƙinin wasu dan ta fahimci a sashensa take. Bai dai san tanai ba, dan tuni ma shi ya fice abinsa. Haka ta cire kayan a jiƙe ta ajiye a gefe, nutsa kanta ta sakeyi a ruwan tana mai lushe idanu kamshin ruwan da ɗuminsa na ratsata, ga yanda kumfar tai a sama ful-ful na wani irin ƙayatar da ita…..

★Ta jima a bayin kafin ta fito, sam batai tunanin samunsa a ɗakin ba. Dan haka ta fito kanta tsaye a zatonta ai zai fita ya bata waje tunda ya san wanka ta shiga. Sai da tazo tsakkiyar ɗakin tana ƙoƙarin sharce ruwan dake sakkowa daga jiƙaƙƙen kanta data wanke zuwa kan fuska ta tsaya turus. Da sauri ta juya bayanta kamar zata fasa ihu. ALLAH ma ya sota bathrobe ta sanyo ba towel ba. Ai da yau taji ƙarshen kunya a duniya.

 

Babu alamar zai motsa a zaman ƙasaitar da yay cikin haɗaɗɗiyar kujerar da yake duk da yaji fitowar tata. Sai da ya mula dan kansa ya ɗan ɗago idanunsa ya dubeta kaɗan ya kauda kai. (Bata tausayama kamata) ya ayyana a zuciyarsa yana jan sirrin tsaki a can ƙasan maƙoshi. System ɗin dake a cinyarsa ya ajiye saman ɗan coffee table ɗin gabansa ya miƙe fuska a daƙile, ta gabanta ya raɓa ya wuce kamar bai ganta ba. Jitai kamar tasa ihu dan takaicinsa, sai dai kuma ta kasa motsawa da ga tsaiwar har ya sake dawowa. A bazata yanzun ma taji tattausan hanunsa kan dogon gashinta data naɗe dan ya tsane da wuri kasancewar ta jiƙesa lungu da saƙo dan wanki ta masa mai ƙyau. Warwaresa yay sannan ya ɗaura karamin towel ɗin hanunsa baby pink a kanta ya fara tsane mata ruwan. A yanzu kam ba mamaki ne ya kashe Iffah kawai ba har da suman wucin gadi tai na ɗunbin mamakinsa. Ita Iffah, ɗiyar Babiy da Ummu ne tsaye Shahan-shan ke mata hidima, Shahan-shan fa ba wai hadimin daular ruman ba. Shahan-shan gaba ɗaya, wanda ke amsa shugaban na ƙasarta baki ɗaya, shugaban kuma al’ummar ƙasar ruman baki ɗaya. Sarkin da duniya ke shakka da tsoron nunama koda ƙasarsa yatsa. Ɗan gata da iyayensa suka haifa shi ɗaya ƙwallin ƙwal a duniya. Shi ɗin nan dai da duniya ke kallo matsayin wani babban tauraro mai girman gaske. “Kai ya ALLAH anya ba mafarki nake ba?”

(Idonki biyu) zuciyarta ta bata amsa da tabbatar da abinda takewa kokwanto. Ai kanta bai nema kwancewa ba sai da ya kama igiyar bathrobe ɗin jikinta ya kwance. A ɗan zabure ta riƙe hannunsa caraf cikin nata tana waro idanu. “Mi zakayi…?” kalmar ta fito a suɓuce daga bakinta. Wata irin dariya ce ta nema kufce masa ya danneta da ƙyar. Cikin ƙara kame fuska ya tsareta da idanun nan nasa masu kaifin tsiya, hanun nata ya ture zai ƙarasa kwancewa abinsa. Sai kawai ta daka uban tsalle ta faɗa masa a jiki “Ni wlhy ba ƴar iska bace, babu fa komai a c….” ta kasa ƙarasawa tana ƙara cikuykuyesa da ƙyau.

 

 

Jikinsa rawa ya neman farayi saboda yanda ta ƙanƙamesa, tunda yake a rayuwarsa bayajin ya taɓa rungumar mace kamar haka. Gaba ɗaya abinda ya ɗauka tsahon shekaru yana dakon dannewa ya nema yunƙurowa. Ƙoƙarin janyeta yake tana sake ƙadandanesa a tunaninta so yake ya cire matan koda tsiya. (Ya arrahaman zata halakani) ya faɗa a zuciya yana mai rumtse idanunsa da masifar ƙarfi a zahiri. Cikin zafin nama ya finciketa da sauri yana ƙoƙarin riƙe rawar da jikin nasa ya fara. Cikin wata ƴar sassarfar da bata hana takunsa na ƙasaita fita a yanda yake ba ya bar wajen, a kujerar da ya tashi ya koma ya zube. Faɗi yake (shike nan ta buɗe aiki, Fitinanniyar yarinya zata halakani).

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button