Hausa Novels and Stories

Matar Damisa Book 1 Chapter 16

Sponsored links

“NIIII MAI BAKI KARIYA NE, still ya ‘kara tintsirewa da razananniyar dariyar shi mai ban tsoro….

Lokaci guda kuwa haske ya bayyana ta daina jin kukan mujiyan.

“Innalillahi wa inna’ilaihi raju’unnn wannan wani irin bala’i ne a cikin gidan nan, Aljanu da mutane duk suna rayuwa a gidan nan” zuciyarta ne ta soma magana kamar haka “Ayush kar ki manta wannan Addu’ar da malamin nan ya koya muku ke da mahaifiyarki” anan ta tuno da Baba tsoho wanda yayi hijira zuwa dajin da suka zauna yayi tsawon shekara biyar atare da su, Babban malami ne na gaske shi ya koya musu karatun al’qur’ani mai girma tare da addu’oi ya koya musu alwala da yanda ake sallah su wankan janaba da haila ba abunda bai koya musu ba ta 6angaren addini,Ayush lokacin bata wuce 15yrs ba ita kuma mahaifiyarta tana ‘kara koyan karatun ne domin wad’annan karatuttukan mahaifin Junaid ya koyar mata su tin suna GHANA.

Damuwar dai Ayush ta samu ta koya duk da itama tana koya mata wasu abubuwan!!

 

Anan tayi firgitt ta soma jero manya-manyan addu’o’i….

 

👉. “Allahumma laa sahla illaa maa ja’altahu sahlan wa anta taj’alul hazna izaa shi’ita sahlan”

(Yaa Allah! Babu wani abu mai sau’ki sai abin da ka sanya shi ya zama mai sau’ki, kuma Kai kana sanya tsanani idan ka so ya zama sau’ki)

“‘Kadrul laahi wamaa shaa’a fa’ala”

(Kaddarar Allah ce, kuma abin da Allah ya so, shi ne yake aikatawa, domin da-na-sani tana bud’e ‘kofar aikin shaid’an).

 

“Laa ilaaha illallaahul aziimul haliimu,

Laa ilaaha illallahu rabbul arshil aziim,

Laa ilaaha illallahu rabbus samawati wa rabbul ardi wa rabbul arshil kariim”….

Bayan ta kammala addu’o’in ta ta shafa ayatul kursiyu, duk wani tsoro da fargaba da ‘kuncin zuciya ya wuce mata ta ‘kwarin gwiwarta ta mi’ke tsaye ta nufi d’akin da ake bu’katar taimako!

Upstairs ta fara takawa a hankula har da iso bakin ‘kofar d’akin tasa hannu zata ture d’akin…

Aka daka tsawa “kada ki kuskura ki bud’e” amma kash duk wannan maganganun kunnen Ayush ya toshe bata jin maganar

Tana bud’e d’akin kuwa wani irin duhu ne a d’akin babu haske kwata-kwata tana shiga d’akin haske ya bayyana ta ko Ina, still yanda taga mutanen nan a kwance haka ta same su

Ta d’aga kanta ta kalli yanda Junaid yake a manne a jikin gini ganinsa yasa ta tsorita naman jikinsa duk ya farfashe ciwon yanzu yafi na d’azu hakan na nufin har yanzu basu daina azabtar da shi ba,

Girgiza Kai tayi tana maganar zuci “bazan iya kusantar ka ba, ka rigada ka mutu”. Toilet ta nufa ta d’auko bucket da ruwa a ciki duk bodyguard d’in da suke kwance ta bisu da ruwa tana kwakwkwara musu cikin sa’a kuwa suka tattashi a firgice suna ajiyar zuci, bayan sun dawo hayyacin su kowa rige-rigen fita yake daga cikin d’akin har mai gadin!

Ta dawo kan Mommy itama ruwa ta yayyafa mata, ajiyar zuciya tayi tana Jan numfashi sama-sama tana ambaton “Junaid! Junaid my son, ya mutu ko? Kamar wata zararriya haka take magana tana bin Ayush ta kallo, mommy bata san waye akan ta kawai dai tana sambatu ne,

Ayush ta tsaya tana tunanin aina ta ta6a jin sunan nan!

Tana cikin wannan tunanin tajiyo kukan mommy ya tsananta sosai tana kuka tana nuna gurin da Junaid yake da yatsanta, kafin kace mai Mommy ta tashi da gudu tayi kan Junaid

Da karfin gaske aka hankad’o mommy baya da sauri Ayush ta tareta badon haka ba fad’uwa ‘kasi zatayi.

Lokaci guda idon Mommy ya ‘kakkafe ta dafe ‘kirjin ta tana shure-shure ciwon zuciyar ta ta tashi,

Ayush ta tsorita sosai da ganin haka da kyar ta iya d’ago Mommy suka fita daga d’akin

Falo ta nufa tana zuwa ta tarar da bodyguards duk sunyi cirko cirko kowa yaji jiki sai ajiyar zuciya suke sau’kewa

Da sauri sukayi kan mommy

‘Daya daga cikin bodyguard ne ya d’aga mommy cakk yayi waje duk sauran ma binsa sukayi a baya

Motor suka shiga gaba d’ayansu

Motor biyu suka d’auka

Biyu suka shiga d’ayan motor and order car shima mutum biyu a ciki,

Kafin one minute sunbar harabar gidan, iya Ayush da mai gadi kawai aka bari a gidan, da sauri Ayush ta nufi gurin mai gadi tana fad’in “Ina zasu Kai ta?”

In short amsa mai gadi ya bata “Asibity” yana fad’an hakan ya shige cikin d’akinsa zallar tsoro ne a tattare dashi…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button