Hausa Novels and Stories

Idon Naira 37

Sponsored links

Acan gidan haj maryamah kuwa umma sati daya tayi ta komawarta bayan tasake zuwa asibitin so daya kafin ta wuce.

Aqeel kuwa ya Isa lfy yanata kokarin fara karatunsa Amma yakasa samun Maminsa

Yayiwa ummansa magana ta sanar dashi baa sallamosuba tukuna dole ya hakura harsu dawo gidan yasamu ko ummansa zata hadasa da mamin tasa a waya.

Haj maryamah kuwa tini ta tattara ta wuce Abuja itama kafin tawuce tazo asibitin ta sake dubata so daya taqara Bata wasu 10k din ta wucewarta bataredama zainab din tasan gari zata Bari ba.

Ahankali ahankali Saida zainab ta share kusan sati uku a asibitin kafin aka sallameta ta nufi gidanta da ‘yarta.

Gidan yayi datti sosai dayake lokacin iska ne Dan haka dole ta goya Maryamah tafara aikin gyaran gidan.

Saidata gyare koina ta share ta wanke kafin ta fito ta samu yaro ya siyo gawayi ta Dora ruwan zafi tayi wanka tayiwa maryamah da aka koyo mata yanda zatayi mata daga asibitin.

Ruwan zafin Tasha da Lipton ta kwanta suka Dan samu bacci tana tashi maqotanta Wanda Basu samu zuwa asibitinba suka shigo sunatayi mata barka da qarin gaisuwar malam.

Da daddare Dole ta dafa shinkafa dayake akwai sauran abinci dasuke dashi.

Da manja taci shinkafar tasake Shan ruwan Lipton tagama sauran ayyukanta ta kwanta.

Washe gari ma haka ta wuni ita kadai a gidanta daga ita sai ‘yarta dare yayi suka kwanta abinsu.

Haka ta runguma rayuwarta data ‘yarta data zama sanyin idaniyarta Kuma sanyin zuciyarta,

A yanzu duniyarta ‘yarta itace babban abinda yake gabanta,

Batada buri ko buqatan daya wuce inganta rayuwar yarta data warware abinta tayi mulmul sbd nono mai kyau da sauran madarar datake Bata wadda har lokacin sunada sauran kusan gwanwani biyu da Basu fasaba.

Aduk lokacinda tayi sallah iyayenta da Malam da Aqeel sune farko a adduarta da ‘yarta kafin kanta,

Ayanxu wata rayuwa take gudanarwa ta kadaici da rashin kowa,

Batada wani farin ciki ko jin dadi

‘yarta kawai take kalla taji qwarin gwiwa da farin cikin rayuwa,

Ba laifi tana hulfar arziki da maqotanta duk da babu Wanda ya taba zuwa yabata taimako ko tallafi daga cikin mutanen malam harna Aqeel Dan haka taci gaba da lallaba abubuwan datake dasu Shi abincinta tuni ya qare dole kayayyakin gidan ta tattara ta Saida tabar katifar kwanciyarsu kawai da kayan kitchen.

yar sanaar Saida gawayi da kayan Miya tafara Amma mutane sun maida komai bashi take suke kwashe komai data kawo Amma bashi

Qarshe Kuma wasu da yawa basa biya haka zataita yawon bin bashin kudin Amma basa bayarwa koyaushe da qaryar da zasu fada.

Babu inda sanaar taje komai ya karye aka rasa kudin gabaki daya Takoma tana kame kame.

Watanta uku da dawowa hayarsu ta qare masu gidan suka Bata notice dole tafara tunanin barin gidan.

Batada gurin zuwa,

Batasan Ina zata da jinjirar ‘ya ba gashi bazaso ‘yarta tayi tashin garari ba.

Ana hakan ne Daren wata asabar wani mummunan tsautsayi ya sameta na shogowar qato gidanta

Allah bai basa ikon yimata komaiba saidai fuskarta ta kumbura da irin Marin daya ringa zabga mata sbd taqi yarda yayi Mata komai

Qarshe haka ya gudu bai samu damar lalata mutuncintaba haka itama Bata samu taga fuskarsaba.

Tunda take hankalinta bai taba tashi da tsoroba irin hakan Dan haka gari na wayewa takai maganar gurin Mai anguwa Amma qarshe dai haka mutuncinta ya zube babu wani takamaimai sheda ko tabbacin abinda ta fada din sbd kusan duka anguwar ansan juna

Basuda samari duka dattijai ne da tsofi

To tayaya take tunanin zasu yarda kowa da mutuncinsa zai shiga yayi irin hakan.

Qarshe hakuri aka Bata akan saidai daga wata anguwar aka shigo aka Mata hakan.

Wannan lamarin ya sake firgita tsayuwarta ta rasa inda zata saka kanta da ‘yarta,

Tsoron gidan da anguwar ma takeji kwata kwata Dan kuwa duka rayuwarta ko yanda ake fyade Bata saniba sai yanzu da hakan yaso faruwa da ita,

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button