Hausa Novels and Stories

Abban Sojoji Chapter 27

Sponsored links

Abun da ya faru MARSHAL OMAR bai samu zuwa kaduna ba sakamakon Emmergency Call din daya samu daga wurin Abbansu cewa yana bukatar shi A headquater dinsu, a lokacin Motarsu har ta fita daga garin Abuja amma suka juyo da hanzari saboda Omar baya wasa da Omarnin mahaifinsa ko musu baya iyayi mashi, duk da yadda ya matsu akan son ganin su hosana da jahad amma haka ya haƙura😔

Tun bayan da suka kammala shan corn flakes junaid ya wuce bedroom dinsa saboda dama agajiye yake, sehrish kuwa sai da ta tsaya a kitchen din har azmee tazo suka fara aiki, cikin kankanin lokaci suka kammala dinner,

 

sannan ta wuce bedroom ɗinta ta kwanta tasha bacci har wurin magrib sannan ta tashi donyin sallah, bayan ta kammala jiki na rawa ta bude wardrobe dinta, tsayawa tayi saboda ruwan ido ta ma rasa me zata sanya acikin kayan, hannu tasanya ta janyo wata haɗaɗɗiyar Gown black colour mai kyalkyali masu daukar ido, jinjina kai tayi tare da cewa “Wannan zan sanya,” tayi maganar tare da hanging dinta asaman murfin wardrobe din, shaf shaf ta tube riga da wandon dake jikinta ta tura su, cikin laundry basket dinta, sannan ta dauki rigar ta shiga kiciniyar zira ta ajikinta, bayan ta kammala ta koma gaban mirror tana kallon kanta ta cikinsa, fuskarta dauke da murmushi tana tuna yaushe rabon da taji ta acikin kayan mata, kayan ma irin wannan sabbi masu kyau, rigar tabi shape din jikinta,hannunta mai dan tsayi ne wanda ya tsaya dai-dai elbow dinta,Jujjuyawa tayi tana ƙarewa kanta kallo, kafin tasa hannu cikin jerin Perfumes dinta ta dauko kwalbar turaren TOUCH ta feffesa ma jikinta har wani lumshe ido take yi saboda yarda fragrance dinsa ke dakar hancinta, bayan ta mayar da turaren ta koma cikin wardrobe din ta ɗauko mayafi white colour tayi rolling dinsa irin lagen da larabawa suke yi masha Allah

Kama hanyar fita tayi tana bude kopan azmee na sanyo kai dama dakin nata ta nufo itama, ganin yarda azmee tasaki baki yasa sehrish sa hannu ta rufe fuska don tasan kallon na menene,

“Nama rasa mai zance irin wannan kyau haka? Yarinya kamar ƴar larabawa ashe dama haka kike da Kyau ga ki dirarra,’?

 

Cikin jin kunya sehrish tace “Aunty azmee ko fa makeup banyi ba, i know u are just teasing me,

 

Azmee tace “Reesh ae ko ba kiyi kwalliya ba kyau kike, ae ni ban ma so kiyi kwalliyar yanzu, don banson ki rikita samarin gidan nan, mu rasa wa zamu ba acikin su,’

 

“BABBAN YAYA’ ta faɗi acikin zuciyarta a fili kuma tace “Mai rabo,” dariya azmee tayi tana cewa “Toh Allah yaba mai rabo sa’a time kawai zamu jira muga wanene wannan in da rai da lafiya,’

 

Murmushi kawai sehrish ke saki, suna cikin wannan tsayuwar motocin su suka shigo atare mai ɗauke da jiniya, azmee tace “Alhamdulillah shikenan ma, tun da kin shirya in suka shigo ki tabbatar kin kaima Babban yayansu dinner dinsa tare da Omar, yanzu ma na kammala jera na dining din basu kai ga saukowa sunci ba, dama Twins ne da suka dawo bada jimawa ba sai Junaid da HAROON, just zanji da sauran kawai

ta ƙare bayanin tare da kama hanyar fita daga ɗakin tana nanata mata,

 

Sehrish ta amsa mata da “toh insha Allah,”

 

cikin sauri ta koma wurin window dinta ta janye labulan ta zuge glass din tana hangensu,

 

kowannansu agajiye ya fito daga cikin Motar, Abbansu ne tare da marshal Omar sai SGR, Abbansu na sanye cikin kaki, haka SGR army trouser ne ajikinsa sai shirt light green mai gajeran hannu sun ɗame jikinsa, Omar kuma Shigar dazu ce ajikinsa wadda yayi shirin Zuwa Kaduna dazu,

 

tunda Armstrong ya buɗe masa mota ya fito yake faman lumshe ido hannunsa ɗaya na acikin sumar kanshi yana yamutsa ta, kallon shi Abban su yayi tare da cewa “Ko dae saina taimaka na goyaka ne? Naga alamar baka iya tafiya,” ɗago da eye balls dinsa yayi ya kalli Abban nasu sannan anatse yace “Dad kenan, ni da kai wa zai goya wani? kai ma ka sani,”

Yayi maganr tare da soma tafiya abban nasu kam dariya yayi yana cewa “Oh kana jin kanka Tamkar giwa ko? Ae ba abun mamaki bane kaga na sa6eka abayana, in banda ma yanzu daka zama jibgege haka ga tsayi nan nan nake ɗaukarka kana yaro har goya ka nake yi,” duk Omar na jinsu yana murmushi kawai saboda atare suka jera suka nufi cikin gidan,

 

ɗan gyaran murya yayi tare da cewa “Abba yanzu ae sai dai ka goya grandchild dinka masu zuwa,” Omar ya faɗi,

 

Abban su yace “hmmmm taya hakan zata faru bayan ƴan bukulu sun hana ruwa gudu, burina kenan kullum kamar yadda na haifa nima nawa su haifa amma abun takaici duka ya’yan nawa babu wanda ya ajiye ko budurwa bayan ni tun ina 20 years aka sanƙamamun aure muka sha soyayya gaba ɗaya,’

Omar yace “Kada ka damu Abba, Insha Allah burin ka zai cika, in har hakan zaisa ka farin ciki, kawai acigaba da yi mana addu’a,’

 

Jinjina kai abbansu yayi yana ɗan kallon SGR dake gefensa shiru tamkar baya jin me suke cewa,

 

Ruko hannunsa yayi cikin nasa sannan yace “kai fa Son, Naji baka ce komai ba ? Ko baka son farin ciki na ne?

 

yatsina fuska yayi tare da cewa “In dai yaron da zaka goya ne zan kawo maka shi,’

“Uwar fa”? Abban ya tambaya adai dai lokacin da suke shiga babban falon SGR yace “Babu,” dariya omar kawai yake yi.abbansu kuwa baki sake yace “Shege zaka kawo min,’?

 

“Ko baka so ne”? Sgr ya tambaya shima da zolaya,

 

Abbansu yace “Ae da babu gwara ba daɗi, akawomin inaso,”

 

Omar yace “So funny wlh, abba son jikokin harya kai haka, to. Insha Allah ba shege acikinsu, Original zaka samu daga gurin kowan nan mun, ‘ cike da nishaɗi suke fira kamar bazasu iya rabu ba, wuce wa Abbansu yayi part dinsa, shima SGR tare da OMAR suka wuce Uptairs nasu parts din,

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button