Hausa Novels and Stories

Zafin Kai 15

Sponsored links

Annensu yanayin manyanci da wahala ga kunnenta da bataji yanzu sosai yanda ya kamata yasa jikinta da lafiya suka fara yimata qaranci yau da gobe wasu ayyukan bata iya yinsu da kyau dan haka sune suka karbe mata duk wani aiki saidai idan suna

makaranta a bata wani aikin shima suna dawowa zasu karban mata hande tayi ta fada amma karba sukeyi saidai wata ran susha marika gurin Ababa akan sun fara Rena hande.

Sbd Anne yasa Benazir takoma gaggawa takewa karantunta ana tashi take dawowa bata batar da lokaci ko qanqani Shiyasa basa dawowa tare da sumayyah kusan tafiyarsu yanzu tare ta rage sosai,

 

Sumayyah tafara IT dinta a wata makarantar kusa da anguwarsu dan haka Ababa ya dena bata kudin mashin ita da qafa take zuwa ta dawo da qafa dan haka take rigan Benazir fita tinda safe.

Bilal ne da kansa yake kaita lokuta da dama kuma ya daukota ita kuma Benazir Sulaiman ne yaci gaba da kaita kuma abincinta babu wanda aka fasa kawo mata makaranta kaman yanda itama sumayyah acan ake kai mata nata.

IT din sumayyah ya sake kusancinta da Bilal kwatsam saiga maganar aurenta da wanda yayi alqawarin bawa yana karban kudinsa akan karatunta ta taso sbd karatun nata yazo karshe dan haka maganar aure ta taso take gadan gadan ba daukan lokaci.

Maganar auren ta rusa duk wani kwanciyar hankalin Bilal ita kuma dukkanin hope din data samu ya wargaje sbd tasan maganar Ababa bamai fasuwa bace ko gardamawa,ko mahaukacin kare ya cijeta bazata iya ko dagowa ta kalli Hukuncin Ababan ba bare gardamawa.

Abinda ya dagawa bilal hankali kenan wato sarewarta da kasa iya cewa komai akan hakan sbd shi anasa bangaren yaso ta basa hadin kai da goyan baya ya sakewa Ababan Nera ba yar kadan ba dan ya hanawa kowa aurenta ya basa ita sbd a hankali ya fahimci irin asalin rayuwar rashin gata da yancin dasukeyi hannunsa dan hakan ne ma yakejin idan bai karbesu su dakan daga hannun Ababan ba kaman zai iya shiga wani halin sbd zai iya komai dan ya rabasu da gidan dan haka auren Sumayyah din yake jin tabbas ba fashi garesa da yardar Allah.

Benazir tayi nisa a karatunta batasan tashin hankalin da suke cikiba saida Yaje daukanta da kansa ranar yake sanar da ita irin yanda yakeson daukesu daga gidan suyi rayuwarsu kaman kowa.

 

Haka kuma a shirye yake da auren Sumayyah ta roketa tabarsa yaje gurin Ababan dan yana qin zuwan ne sbd baisan kalan azabar da zai janyo musu ba shiyasa yaketa kiyayewa.

Ita kanta Benazir jin hakan saida takusa shidewar mintina sbd firgitaccen tashin hankalin wucin gadin data shiga sbd zuwansa gurin Ababa koda motar kudi zai ake masa wlh saiya kusa aikasu lahira kafin ya amsa kudin sbd sun take qaqqarfan doka da sharadinsa akansu na kula kowane irin namiji.

Cikin rashin boye masa tashin hankali da tsoronta taqi amincewa zuwansa itama,

Anne ma dataji da sauri ta hanasu qarasa zancen sbd kusan da hannu suka kwatanta mata rabin zancen tinda bataji sosai sai an dan daga murya gashi zancen bana a daga murya bane wani yaji Alqiyamarsu ta tsaya.

Wanna maganar tasa ta sanya kwata kwata suka fara qaurace masa ga tsananin Ababa akansu ta qaru dan kusan yanzu dabiar kai musu ziyarar ba zata ya dauko dan haka suka shiga taitayinsu ba shiri

Kusan sati biyu Bilal yayi bai saka daga Sumayyah har benazir a idanuwansa ba dan haka ya shiga damuwa da tashin hankali sosai sbd kar Ababa fa yayiwa Sumayyah aure bai saniba.

Ita kanta sumayyah tana cikin damuwa da qunci ga dukan da yanzu kusan kullum sai tasha sbd tinani ya hanata nutsuwa ta aikin data saba kullum saita qona manyan kayan mutane gurin guga dan haka a cikin qanqanin lokaci ciwonta yafara kokarin dawowa na kai,

Benazir na ganin haka tafara kokarin kada Ababan ya gane ciwon Sumayyah saidai kuma kusan abin gaba gaba yafara sbd da asarar datake ja masa tayi yawa sai ya hanata fita kwata kwata makarantar datake IT din bayan wahala da duka babu abinda take samu kullum a gurinsa.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button